Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana iya yin amfani da fasahar 5G a dakunan wasa 4 na gasar kwallon kwando ta hukumar FIBA
2019-09-04 15:37:44        cri

Ana gudanar da wasanni na gasar kwallon kwando ta hukumar FIBA ta shekarar 2019 a kasar Sin, an ce, ana iya yin amfani da fasahar 5G a dakunan wasa 4 na gasar dake biranen Guangzhou, da Shenzhen, da Foshan, da kuma Dongguan, inda ake iya watsa wasanni kai tsaye ta fasahar 5G da kuma 4K, tare da samar da hidima ga masu amfani da fasahar 5G a wayoyin salula.

Gasar kwallon kwando ta hukumar FIBA, gasar wasan koli ce a duniya. Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta gudanar da gasar, wadda aka yi wasannin gasar a birane 8 na kasar wato Beijing, da Guangzhou, da Nanjing, da Shanghai, da Wuhan, da Shenzhen, da Foshan, da kuma Dongguan. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China