Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin tana son more damar bunkasa fasahar 5G tare da duniya
2019-07-09 20:20:47        cri
A jiya, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi da takwarabsa na kasar Poland Jacek Czaputowicz sun gana da 'yan jarida, inda suka amsa tambayoyi game da fasahar 5G.

Wang Yi ya yi nuni da cewa, fasahar 5G alama ce ta bunkasuwar kimiyya da fasaha ta dan Adam, kana sakamakon hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa. Ya kamata dukkan duniya ta more damar da bunkasa fasahar 5G ta kawo. Sin ta sa kaimi ga kamfanonin kasar da su more sabbin nasarorin da aka samu a fannin fasahar 5G tare da sauran kasashen duniya, don inganta sha'anin sadarwar duniya tare da amfanawa jama'ar kasa da kasa. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China