![]() |
|
2019-08-26 10:11:02 cri |
A cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, majalisar mulkin kasar Sudan ta ayyana sauke gwamnan jihar Red Sea tare da babban jami'in tsaron jihar, sannan an sabunta dokar ta baci a jihar kana an bada umarnin gudanar da bincike kan abin da ya haddasa mummunan tashin hankalin.
Majalisar ta kuma lashi takobin hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu a tashin hankalin kana za ta biya diyya ga wadanda lamarin ya rutsa da su.
Tun da farko a wannan rana, 'yan sandan Sudan sun sanar da cewa, mutane 17 ne aka hallaka a tashin hankalin na fadan kabilanci tsakanin kabilu biyu dake birnin Port Sudan, babban birnin jihar Red Sea.
A ranar 22 ga watan Ogusta, fada ya barke tsakanin al'ummomin kabilun Bani Amer da Al-Nuba a birnin Port Sudan, inda majalisar mulkin karamar hukumar ta sanya dokar hana fita.
Ana ganin tashin hankalin na Port Sudan a matsayin karin tashin hankali makamacin wadanda suka faru a baya a biranen gabashin Sudan, wanda ya hada da Gadarif, Khashm al-Qirba da Kassala, tsakanin wadannan kabilun biyu. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China