Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daliban Zimbabwe 10 za su halarci horo a helkwatar Huawei a Sin
2019-07-11 11:00:16        cri

A ranar Laraba kamfanin fasahar zamani na Huawei dake Zimbabwe ya kaddamar da shirin kyautata makoma na shekarar 2019, karkashin shirin, an zabi wasu daliban jami'o'in kasar 10 domin tura su halartar shirin samun horo kan fasahohin zamani a babbar helkwatar kamfanin dake birnin Shenzhen na kasar Sin.

Shirin kyautata makomar, wani muhimmin aiki ne na sauke nauyin dake bisa wuyan kamfanin na Huawei, inda kamfanin ke yin hadin gwiwa da makarantu, jami'o'i, da kwalejojin ilmi domin samar da horo da musayar kwarewa ga dalibai.

Manufar shirin ita ce domin samar da kwararrun fasahar zamani ta ICT a kasashen da kamfanin Huawei ke gudanar da ayyukansa da kuma raya kamfanonin fasaha na cikin gida.

Daliban 10, za su ziyarci kasar Sin daga ranar 12 zuwa 28 ga watan Yuli, inda adadin wadanda suka amfana da shirin a kasar Zimbabwe zai kai 40 tun bayan kaddamar da shirin a shekarar 2016.

Manajan daraktan kamfanin Huawei dake Zimbabwe Shao Jie, ya ce, shirin zai baiwa daliban damar samun horo na tsawon makonni biyu ne game da samun ilmi kan al'adu da fasahar zamani ta kasar Sin, za su fara ne da shafe tsawon mako guda a birnin Beijing kafin daga bisani su dunguma zuwa helkwatar kamfanin dake birnin Shenzhen domin kara mako guda, ta yadda za su samun horo kan sabbin fasahohin zamani na ICT, wadanda suka hada har da fasahar zamani ta 5G.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China