Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalissar dokokin Afirka ta kudu ta yi kira da a kawo karshen mamayar gonaki
2019-07-09 09:47:59        cri
Majalissar dokokin Afirka ta kudu, ta yi kira da a kawo karshen mamayar gonaki ba bisa ka'ida ba, tana mai alkawarta daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin kaucewa mummunan tasirin da manufar sauyi ga dokar mallakar filaye ta kasar ka iya haifarwa.

Da yake tsokaci game da wannan batu, shugaban kwamitin majalissar mai lura da ayyukan noma, da gyaran fuska ga dokar mallakar filaye, da ci gaban yankunan karkara Nkosi Mandela, ya ce dole ne majalissar ta yi duk mai yiwuwa wajen dakile karya doka, ta yadda bata-gari ba za su kawar da kasar daga tsarin da doka ta tanada ba, ko hana masu filaye ikon mallaka na halak.

Nkosi Mandela na wannan tsokaci ne, biyowa bayan harin da wasu matasa suka kai wata gona mai fadin hekta 7,500 a lardin KwaZulu-Natal, inda suka cinnawa amfanin dake cikin gonar wuta, suka kuma tura manajan gonar cikin wuta. Rahotanni sun ce yanzu haka manajan na samun sauki a asibiti sakamakon kuna da ya samu.

Aukuwar wannan lamari dai ya jawo damuwa tsakanin al'ummar kasar, game da halascin sauye sauye da ake yi ga dokokin mallakar filaye a kasar, a gabar da 'yan majalissar dokokin ke yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, wadda za ta ba da damar sauya ikon mallakar filaye ba tare da biyan diyya ba. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China