Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin sabon babban alkalin alkalan kasar
2019-07-18 09:10:38        cri
Majalisar dattawan Najeriya, ta tabbatar da nadin Ibrahim Tanko Muhammad mai shekaru 66 a matsayin sabon alkalin alkalan kasar, bayan da majalisar dake Abuja, fadar mulkin Najeriyar ta tantance shi jiya Laraba. Wannan matsayi ya ba shi ikon shugabantar kotun koli da bangaren shari'ar kasar.

Tun a watan Janairun wannan shekarar ce dai, hukumar kula da harkokin shari'a ta Najeriya ta nemi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya nada shi a matsayin mai rikon mukamin alkalin alkalan kasar.

Nadin nasa ya biyo bayan dakatar da magabacinsa Walter Onnoghen, bayan da aka zarge shi da yin coge wajen bayyana kadarorin da ya mallaka, lamarin da ya saba dokar kotun da'ar ma'aikata, wadda ta bukaci jami'an gwamnati da su bayyana kadarorin da suka mallaka.

A ranar 11 ga watan Yulin wannan shekara ce, shugaba Buhari ya mikawa majalisar dattawan kasar sunan Tanko, don neman amincewarta kamar yadda kudin tsarin mulkin Najeriyar ya tanada.

Gabanin nadin sa kan wannan mukami, Tanko ya yi aiki a matsayin alkalin kotun kolin Najeriya tun shekarar 2017 har zuwa wannan lokaci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China