A kwanakin baya, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da kididdigar tattalin arzikin kasar ta farkon rabin shekarar bana, a cikinsu yawan GDP ya karu da kashi 6.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Bayan da aka gabatar da kididdigar, wasu kafofin watsa labaru na kasashen waje sun bayar da labarai cewa, yawan tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 6.2 cikin dari a rabi'u na biyu na bana, wannan ne ya zama mafi karanci a cikin shekaru 19 da suka gabata, abin da ya shaida cewa, tattalin arzikin Sin ya ragu. Game da wannan batu, direktar ofishin kula da manufofin tattalin arzikin Sin na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki da bunkasuwa wato OECD Margit Molnar ta bayyana cewa, wannan ra'ayin da wasu kafofin watsa labaru suka bayar ba shi da tushe, tattalin arzikin Sin ya yi tafiya mai kyau bisa yanayin kasa da kasa.
Madam Margit ta amince da ra'ayin Sin cewar tattalin arzikinta ya yi tafiya yadda ya kamata a farkon rabin shekarar bana. Ta ce, Sin ta samu babban ci gaba kan canja tsarin bunkasa tattalin arzikinta a sakamakon kwaskwarima kan tsarinta a shekarun baya baya nan.
Game da bunkasuwar tattalin arzikin Sin na karshen rabin bana, madam Margit ta bayyana cewa, Sin ta iya sa kaimi ga jama'arta da su kashe kudi ta hanyar kyautata tsarin tabbatar da rayuwar jama'ar kasar. (Zainab)