Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ba za ta cimma burinta na fakewa da batun 'yancin bin addini tana yin shisshigi a harkokin sauran kasashe ba
2019-07-22 20:39:56        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Gengshuang ya bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a yau Litinin cewa, kawancen kasa da kasa kan 'yancin bin Addini da Amurka ta kafa fakewa ne da batun 'yancin bin Addini da yin katsalandan a harkokin cikin gidan sauran kasashe, kuma dole ne ba za ta yi nasara ba.

Ya kara da cewa, wasikar nuna adawa da kasar Sin da kafofin yada labarai na Amurka suka gabatar kwanan baya, cike take da son zuciya kan ra'ayoyi daban-daban da tunanin ra'ayin yakin cacar baka, lamarin da zai kawo illa ga bunkasuwar huldar Sin da Amurka, za kuma a yi watsi da shi a kundin tarihi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China