2019-05-17 20:11:28 cri |
Jiya shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana yayin da aka tambaye shi ra'ayinsa kan matakin da Amurka ta dauka don hana ci gaban kamfanonin fasahohin kasar Sin wajen raya fasahar 5G cewa, yanzu bai dace ba wata kasa ta tayar da yakin kimiyya da fasaha ko yakin cinikayya da wata kasa ta daban, kasar Faransa tana nacewa ga manufar gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin bangarori da dama, kuma ba zai yiyu ba ta dauki matakin sanya katanga ga kamfanin Huawei ko sauran kamfanoni makamantansu.
Kan wannan, yau kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yaba da matsayin da Faransa ta dauka kan batun shiga aikin raya fasahar 5G na kamfanonin fasahohin kasar Sin. Yanzu kasashen duniya suna dunkulewa waje daya, a don haka akwai bukatar cudanya da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa yayin da ake kokarin raya fasahar 5G, matakin da Amurka ta dauka domin cimma makarkashiyar siyasa zai hana ci gaban fasahar, kana ya saba wa ka'idar yin gogayya bisa adalci, a karshe kuma zai lalata moriyar daukacin kasashen duniya.(Jamila)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China