Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daliban kasar Kamaru 59 na kwalejin confisius sun samu tallafin karatu daga Jakadan kasar Sin
2019-06-22 15:36:13        cri
Dalibai 59 na kwalejin Confiscius na Kamaru, sun karbi tallafin karatu daga jakadan kasar Sin a kasar, Wang Yingwu, a jiya Juma'a.

An raba tallafin ne tsakanin daliban da suka yi kokari sosai a gwajin da aka yi musu na harshen Sinanci.

Ariane Zetchounag, mai shekaru 24 wadda ke mataki na biyu a kwalejin, kuma daya daga cikin wadanda suka sami tallafin, ta ce kyautar za ta taimaka mata wajen kara zagewa kan koyon harshen Sinanci.

A cewar Jakada Wang, ta hanyar nazarin kasar Sin da al'adunta, wadannan matasan 'yan Kamaru, za su zama masu daukaka abota tsakanin kasashen biyu.

Bikin da aka gudanar jiya, ya kuma yabawa kwazon malaman Sinanci na kwalejin, na zangon karatu na 2018/2019 (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China