Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayaka 165 a kasar Kamaru sun ajiye makamai
2019-05-08 10:22:15        cri
Kwamitin kwance damarar makamai da sake hada kan 'yan kasa a kasar Kamaru (NCDDR) ya sanar a jiya Talata cewa, mayaka 165 a yankin arewa mai nisa da yankuna biyu na kasar da ke magana da Turancin Ingilishi ne suka ajiye makamai bisa radin kansu a cikin watanni biyar din da suka gabata, domin su dawo cikin al'umma

Jami'in tsare-tsaren kwamitin Francis Fai Yengo shi ne ya shaidawa manema labarai hakan bayan ya yi wa firaministan kasar da wasu manyan jami'an gwamnati karin haske game da sabon ci gaban da aka samu. Ya ce, duk da cewa adadin ba shi da yawa, amma hakan wata babbar nasara ce, ganin yadda daruruwan masu dauke da makamai suka yarda su ajiye makamansu ba tare da sun bayyana ba.

Yengo ya ce, kwamitin zai tsugunar tare da koyawa tsoffin mayakan da suka tuba sana'oi a cibiyoyin da aka tanadar a sassa daban-daban na kasar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China