Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatare Janar na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai yankin tsakiyar Mali
2019-06-11 09:55:19        cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin da aka kai yankin tsakiyar Mali, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula akalla 95.

Sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, ta ce Sakatare Janar din ya fusata da rahoton cewa, fararen hula 95 sun mutu, ciki har da mata da yara, da raunatar wasu da dama, biyo bayan harin da aka kai kauyen Sobanou-Kou na yankin Mopti dake tsakiyar kasar Mali.

Stephane Dujarric ya ce, Antonio Guterres ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin, yana mai kira ga hukumomin kasar da su yi bincike kan lamarin tare da tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu ciki.

Sakatare Janar din ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a kasar Mali su kauracewa daukar matakin ramuwa, yana mai bukatar gwamnatin kasar da masu ruwa da tsakin su shirya tattaunawar sulhu tsakanin al'ummomi domin warware zaman dardar da sabanin da ke akwai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China