Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron hada-hadar kudi tsakanin Sin da Afrika ya mayar da hankali kan musayar dabaru da damarmaki
2019-05-29 09:39:02        cri

Masu tsara manufofi da kwararru kan harkokin hada-hadar kudi daga cibiyoyi daban daban na kasar Sin da Afrika ne suka hallara a Nairabi, domin tattauna yadda za a gaggauta zuba jari da hada gwiwa wajen samar da hidimomin hada-hadar kudi na zamani ga kowa a Afrika.

Yayin taron na "samar da hidimomin hada-hadar kudi na zamani ga kowa na Sin da Afrika na 2019", wanda ya biyo bayan makamancinsa da aka yi cikin watan Satumban shekarar 2017 a birnin Beijing, kwararru za su tattauna yadda za a inganta da raya ajandar samar da hidimomin hada-hadar kudi na zamani ta duniya, ta hanyar samar da dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, da nufin saukaka musayar dabaru da hadin gwiwa da zuba jari.

Yayin taron wanda ya mayar da hankali kan ci gaba, da kirkire kirkire kan hidimomin hada-hadar kudi na zamani a Kenya da Afrika baki daya, manyan kamfanonin kasar Sin na wannan bangaren, sun bayyana irin ayyukansu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China