Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matsakaicin shekarun Sinawa ya kai 77 a bara
2019-05-27 21:14:03        cri
Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta fitar da wata sanarwa kan alkaluman ci gaban harkokin kiwon lafiya na kasar na shekara ta 2018, inda ta nuna cewa, matsakaicin shekarun al'ummar kasar Sin ya karu daga 76.7 a shekara ta 2017 zuwa 77 a bara, kuma yawan mace-macen mata masu juna biyu da mata a lokacin haihuwa gami da yawan jariran da suka mutu duk sun ragu.

Matsakaicin shekarun jama'a, da yawan mace-macen mata masu juna biyu da mata a lokacin haihuwa, gami da yawan mace-macen jarirai su ne muhimman mizanin matsayin ci gaban harkokin kiwon lafiya na kowace kasa. Bisa sanarwar da aka bayar, wadannan alkaluman uku suna matukar kusa da babban burin da gwamnatin kasar Sin ta ke fatan cimmawa nan da shekara ta 2020, yayin da kuma aka cimma manufar da aka tsara game da rage yawan mace-macen jarirai.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China