2019-05-09 10:18:10 cri |
Jami'an MDD sun bukaci a kara samar da kayayyakin jin kai ga miliyoyin mutanen da tashin hankalin da ya barke ya shafa, in ji Farhan Haq, mataimakin kakakin sakatare-janar na MDD Antonio Guterres.
A cewar Haq, masu gudanar da ayyukan jin kai dake zaune a kasashen Burkina Faso, Mali da Nijer sun yi gargadin cewa bukatar kayayyakin tallafin jin kai da ake da shi ya zarta abin da ake da shi a hannu, a yayin da tashe-tashen hankula ke ci gaba da kara kamari da kuma barazanar dake ci gaba da bazuwa zuwa sassan gabar tekun kasashen yammacin Afrika.
Adadin matsalolin tsaro da suka faru a Burkina Faso, Mali da yammacin jamhuriyar Nijer ya sake karuwa matuka a cikin watannin baya bayan nan, inda aka samu tashe-tashen hankula sama da 150 a cikin watan Afrilu kadai wadanda suka yi sanadiyyar rayukan sama da mutane 300. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China