2019-05-28 10:21:26 cri |
Yayin wani taron manema labarai a jiya, Ni Chunxia, jami'i a ma'aikatar kula da harkokin al'umma ya ce kawo yanzu, an nada jami'an sa sanya ido 45,000 da masu kula da yara 620,000 a matakan garuruwa da kauyuka.
A cewar takardar ka'idoji da ma'aikatar ta fitar da hadin gwiwa sauran sassan gwamnati, aikin masu sanya idon shi ne, ziyartar yaran da iyayensu suka kaura zuwa birni suka barsu da yaran dake cikin matsanancin yanayi a akai kai, inda za su rika tattara rahoto da bayanan yaran dake bukatar taimako domin taimka musu samun tallafi.
Takardar ta kara da cewa, za kuma a horar da jami'an domin taimaka musu sauke nauyin da ya rataya a wuyansu yadda ya kamata. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China