Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda ake tsare da malama Meng Wanzhou ya keta doka
2019-05-09 20:27:55        cri
A jiya Laraba, babbar kotun lardin British Columbia na kasar Canada ta fara shari'ar Malama Meng Wanzhou, babbar darektar harkokin kudi a kamfanin Huawei, kan bukatar Amurka ta mika ta kasar. A yayin zaman kotun, lauyoyin malama Meng Wangzhou sun yi nuni da cewa, Amurka ba ta da wata hujja ta tusa keyarta zuwa kasar, kuma yadda kasar Canada ke tsare da ita ma ya keta doka.

Lauyoyin sun kara da cewa, furucin shugaba Donald Trump na Amurka a game da batun ya shaida cewa, lamarin na da nasaba da wani buri da ake neman cimmawa ta fannin siyasa.

Alkalai dai ba su yanke hukunci ba, amma sun yanke shawarar sake ci gaba da shari'ar daga ranar 23 zuwa 25 ga watan Satumba mai zuwa, sa'an nan a dora daga ranar 30 ga watan Satumba zuwa 4 ga Oktoba. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China