Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya taya taron na'urori masu sarrafa kansu da ba da ilmi na kasa da kasa murna
2019-05-16 14:09:15        cri

An kira taron na'urori masu sarrafa kansu da ba da ilmi na kasa da kasa yau din nan 16 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika wata wasika don taya shi murna.

A cikin wasikar, shugaba Xi ya bayyana cewa, na'urori masu sarrafa kansu wani muhimmin karfi ne dake jagorantar kwaskwarima a sabon zagaye na juyin juya halin kimiyya da fasaha da sauyawar masana'antu, wanda ke kawo babban sauyi kan matakan da aka dauka wajen samar da kayayyaki, zaman rayuwar jama'a, da samun ilmi, wanda kuma ya sa kaimi ga Bil Adama da ya shiga wani sabon zamani na hadin kan jama'a da na'urori, hadewar fannoni daban-daban, da yin kirkire-kirkire da more su tare. Abin da ke gaban aikin ba da ilmi shi ne yin amfani da zarafi mai kyau na bunkasuwar na'urori masu sarrafa kansu na duniya, da bin hanyar da ta dace, da horar da masani a wannan fanni dake da fifiko sosai ta fuskar kirkire-kirkire da hadin kai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China