2019-05-15 21:04:09 cri |
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yaba da mabanbanta da muhimman wayewar kan Asiya, shugaban ya bayyana hakan ne, yayin da ya halarci bikin nune-nune, a ci gaba da taron tattaunawa kan wayewar kan al'adun Asiya dake gudana a nan birnin Beijing.
Xi ya kuma bayyana a farkon jawabinsa cewa, al'adun Asiya sun nuna tasiri da ingancinsu, godiya ga tarin wayewar kan al'adun Asiya. Ya kuma bayyana cewa, "Yau, za a kalli kyawawan al'adun Asiya baki daya"
Ya ce, fasohohin za su karade iyakokin kasashe, su taba zukatun jama'a su kuma ratsa su, suna nunawa duniya wani haske, shahara, zaman lafiya da ci gaban Asiya.
Shugaba Xi ya ce, al'ummar Sinawa, na fatan kasashen Asiya, za su taimakawa juna su yi aiki kafada da kafada domin ciyar da kansu gaba tare da sauran kasashen duniya.(Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China