Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude dandalin yin musayar ra'ayi kan fasahohin gudanar da ayyukan kasa na Asiya a birnin Beijing
2019-05-16 11:05:48        cri

An bude dandalin yin musayar ra'ayi kan fasahohin gudanar da harkokin kasa na Asiya dake karkashin taron tattaunawar wayewar kan Asiya mai taken "Yin musanyar wayewar kai da raya kyakkyawar Asiya cikin hadin kai", a jiya Laraba 15 ga wata a birnin Beijing. Mamban hukumar siyasa, kana shugaban sashen yayyata ayyuka na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Mista Huang Kunming ya halarci dandalin tare da ba da jawabi, inda ya jaddada wajibcin yin musayar wayewar kai da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ta Asiya cikin hadin kai, da kara tuntubar juna tsakanin kasashen Asiya kan fasahohin gudanar da harkokin kasar, ta yadda kasashe daban-daban za su koyi fasahohi masu wayewar kai wajen samun bunkasuwa tare, da kuma sa kaimi ga ci gaban wayewar kan Asiya.

Mista Huang ya kuma nuna cewa, jawabin da shugaba Xi ya bayar a gun taron bude babban taron tattaunawar wayewar kan Asiya, ya samar da wayewar kai irin na al'ummar kasar Sin wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ta Asiya har ma ta dukkanin Bil Adama, da kuma samarwa kasashen Asiya da abin koyi mai daraja ga manufofin gudanar da harkokin kasa da samun bunkuwarsu mai wadata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China