Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 5 sun mutu sakamakon harin da dakarun 'yan adawa a kasar Sham suka kai
2019-05-13 11:16:37        cri
Kafar yada labarai ta kasar Sham ta ba da labari a jiya 12 ga wata cewa, dakarun 'yan adawa a kasar, sun kai harin rokoki a garin Sqailbiyeh na jihar Hama dake tsakiyar kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar yara 4 da mace 1, da kuma sauran yara 6 wadanda suka ji rauni.

Labarin ya ce, harin da dakarun suka kai ya lalata gidajen fararen hula da dama, kana sojojin gwamnati kuma sun maida martani nan da nan, tare da murkushe wasu sansanonin 'yan adawa da makamansu.

An ce, a ranar 8 ga watan, 'yan adawar sun kai hari a wani gari na daban dake arewa maso yammacin jihar Hama, lamarin da ya sa fararen hula da dama suka ji rauni ciki hadda kananan yara.

Kwanakin baya bayan nan rikici tsakanin sojojin gwamnatin da dakarun 'yan adawa ya kara tsananta a kudancin jihar Idlib da arewacin jihar Hama.

Jihar Idlib yana arewa maso yammacin kasar Sham wanda ke dab da kasar Turkiyya, kana kuma ya kasance yanki na karshe da 'yan adawa da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi suke rike da shi a kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China