>
Babi22: Kayayyakin Tarihi
Kayayyakin Tarihi

Kogon Longmen da ke birnin Luoyang

Kogon Longmen yana wurin da ke kudu da birnin Luoyang, ya kai nisa kilomita 12.5 a tsakaninsu. Domin duwatsu biyu suna nan suna gaba da juna. Kogin Yi ya wuce a tsakaninsu. Bayan daular Tang ta kasar Sin, a kan kira wannan wuri "Longmen". Longmen yana da muhimmanci sosai, kewayensa ma yana da kyaun gani kwarai, kuma ana jin dadin yanayin wannan wuri, mawaka da masana su kan je wurin domin shan iska. Ban da wannan, domin ingancin dutse na wurin yana da kyau, a kan haka kogo a wannan wuri.

Kogon Longmen da Kogon Mogao na Dunhuang da Kogon Yungang da ke birnin Datong su ne "Kogo 3 dake cike da fasahohin zane-zane da aka yi su a kan dutse na kasar Sin". Yau da shekaru 1500 da suka wuce, an fara haka Kogon Longmen tun daga lokacin sarki Xiaowen na daular Wei ta Arewa, wato tun shekarar 471, bayan shekaru 400 da aka haka da sassaka zane-zane da mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha a wurin Longmen, an kamala aikin sassaka Kogon Longmen. Daga Kudu zuwa arewa na Kogon Longmen ya yi kilomita wajen 1, yanzu akwai kogo fiye da dubu 1 da dari 3 da hasumiyoyin da mabiya addinin Buddha suka yi fiye da 50 da mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi mata bauta fiye da 9700. Daga cikinsu, Kogon tsakiya na Bingyang da dakin addinin Buddha na Fengxian da Kogon Guyang sun fi shahara.

Kogon tsakiya na Bingyang yana wakiltar al'adar daular Wei ta Arewa, wato tun daga shekarar 386 zuwa shekarar 512. Tsawon lokacin haka wannan kogo ya yi da yawa har ya kai shekaru 24. A cikin wannan kogo, akwai manyan mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi mata bauta guda 11. Daga cikinsu mutum-mutumin Sakyamuni wanda ya kafa addinin Buddha yana zaune a tsakiya. A gaban mutum-mutumin Sakyamuni akwai mutum-mutumin damisa guda biyu. A wurin da ke hagu da dama da mutum-mutumin Sakyamuni, sai mutum-mutumin almajiransa guda 2 da mutum-mutumin da 'yan addinin Buddha ke bauta masa guda 2. Ban da wadannan mutum-mutum, an kuma sassaka sauran mutum-mutum a cikin wannan Kogon tsakiya na Bingyang. Suna cikin kogon kamar suna sauraran laccar ilmin addinin Buddha da malaminsu suke yi musu.

Kogo na mabiya addinin Buddha na Fengxian ya fi girma daga cikin dukkan kogunan Longmen. Wannan Kogon Fengxian ya wakilci halin musamman na daular Tang, wato tun shekarar 618 zuwa ta 904, wajen sassaka fasahohin zane-zane a kan dutse. Tsawo da fadinsa fiye da mita 30. Dukkan mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi mata bauta suna nan suna nuna fasahohin zane masu kyaun gani tare, musamman mutum-mutumin Lushena ya fi kyaun gani sosai. Mutum-mutumin Lushena wanda tsayinsa ya kai mita wajen 17 yana nan kamar yana da rai. A cikin idonsa za a iya ganin hankalinsa. Ya kallo masu yawon shakatawa daga sama. Sabo da haka, masu yawon shakatawa za su iya jin karfinsa.

Ya fi sauran Koguna na Longmen rinjaye an haka kogo na Guyang. Abubuwan da suke cikin kogon Guyang sun fi yawa. Shi ma kogo daban da ke wakiltar al'adar daular Bei Wei. A cikin wannan kogon Guyang akwai kananan mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta. A kan wadannan mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke bauta masa, a kan rubuta sunaye da lokacin sassake su. Sabo da haka sun zama abubuwa masu daraja wajen nazarin fasahar rubuce da ta sassakawa.

Bugu da kari, a cikin Kogon Longmen, har yanzu, kayayyakin tarihi sun hada da na addinai da fasahar zane da fasahar rubuce da na kide-kide da tufafi da magani da na gine-gine da na zirga-zirga da dai makamatansu. Sabo da haka, Kogon Longmen shi ma wani babbar ma'adanar kayayyakin tarihi da aka sassake su a kan duwatsu"

A ran 30 ga watan Nuwamba na shekara ta 2000, an zabi Kogon Longmen a cikin Takardar Sunayen Kayayyakin Tarihi ta Duniya. Kwamitin kula da kayayyakin tarihi ya ba da sharhi cewa: Kogon Longmen da mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke bauta masa sun yi nune-nunen fasahar zane ta karshen daular Bei Wei da ta daular Tang. Mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke bauta masa da aka sassake su a cikin Kogon Longmen sun fi da yawa kuma sun fi gwamninta. Wadannan abubuwan fasahar zane inda suke bayyana labaru game da addinin Buddha suna kan matsayin koli na fasahar zane da aka sassake su a kan dutse a nan kasar Sin.

Tsaunin Emei da babban Budda na tsaunin Leshan

Tsaunin Emei wanda ake kiransa "babban tsaunin Guangming yana tsakiyar kudancin lardin Sichuan da ke yammacin kasar Sin, kuma yana shiyyar da ke tsakanin kwarin Sichuan da faffadan tsaunin Qinghai-Tibet, kololuwa mafi tsayi da ake kira Wanfu na wannan tsauni wanda nisansa daga leburin teku ya kai mita 3099. Tsaunin Emei ya shahara a kasar Sin da kasashen waje sabo da tsaunin yana da kyau kwarai da kuma kayatarwa, kuma irin addinin Budda na tsaunin ya yi kama da da'awa, ni'imtaccen wurin da al'adun gargajiya mai dogon tarihi suka hadu yadda ya kamata, sabo da haka akan yi wa tsaunin yabo da cewa, "tsaunin Emei ya fi ni'ima a duk duniya baki daya".

Tsaunin Emei yana wurin haduwar abubuwan halittu masu yawa kuma masu yamutsi, a nan akwai ire-iren halittu masu rai kuma masu wadata, kuma ire-iren halittu na musamman suna da yawa, an kiyaye cikakken tsarin tsire-tsire na shiyya mai zafi kadan, yawan shingen bishiyoyi ya kai kashi 87 bisa 100. Tsaunin Emei yana da manyan tsire-tsire fiye da iri 3200 wadanda suka kasu cikin sassa 242, wato yawansu ya kai wajen kashi 10 bisa 100 na duk tsire-tsiren kasar Sin, daga cikinsu irin tsire-tsiren da suka yi girma ko kuma aka gano su a kan tsaunin, ko kuma wadanda aka ba su suna Emei sun kai fiye da 100. Ban da wannan kuma, tsaunin Emei ya zama wurin da irin dabbobin da ba safai akan gan su ba suke zama, ire-iren dabbobin da aka san sunayensu sun kai fiye da 2300. Nan ne muhimmin wurin da ake yin binciken tsare-tsaren halittu masu rai na duniya da sauran batutuwa masu ma'anar musamman.

Tsaunin Emei yana daya daga cikin "manyan shahararrun tsaunukan addinin Budda guda 4 na kasar Sin". Barbazuwar addinin Budda, da kafuwa da kuma wadatuwar haikalai sun bullo da hali mai ban ta'ajibi a tsaunin Emei. Al'adun addini musamman ma al'adun addinin Budda sun zama ginshiki na al'adun gargajiya na tarihin tsaunin Emei, duk gine-gine da mutum-mutumi da kayayyakin addini da huduba da kade-kade da zane-zane da ke cikin haikalai dukkansu sun nuna halin al'adun addini. Haikalan da ke kan tsaunin Emei sun kasance layi-layi, daga cikin su da akwai haikalin Baoguo da na Wannian da sauran "haikalai guda 6 masu kokuwar dakunan zinariya" sun fi shahara.

Babban Budda na tsaunin Leshan wanda ake kira "babban Budda na Mile ko na Jiading" yana kan kolin Siluan da ke gabashin tsaunin Emei, wanda kuma aka fara sassaka shi daga shekarar 713 ta daular Tang, ba a gama aikin ba sai bayan shekaru 90. Buddan ya dogaro bisa tsaunin kuma yana duban teku, ya zama Budda mafi girma da aka sassaka da duwatsu na duniyar yanzu. Aan cewa haka, "duk tsaunin ya zama wani Budda ne, kuma Budda daya ya zama wani tsauni ke nan". Babban budda yana zaune a gabas yana hangen yamma, yana da fuska mai kwarjini, duk tsayinsa ya kai mita 71. An sassaka Budda cikin nitsuwa, duk jikin budda yana da kyau wajen fasali, ya nuna karfin zuciya irin na al'adun daular Tang. Ban da wannan kuma an sassaka mutum-mutumi masu kyau fiye da 90 kan duwatsun da ke kudanci da kuma arewacin babban Buddan.

Tsaunin Emei (wanda yake hade da babban Budda na tsaunin Leshan suna) suna wurin musamman da ya dace wajen halayen kasa, wannan wuri yana da kyau kwarai da kayatarwa, an kiyaye muhallin halittu da kyau, musamman ma wurin yana shiyyar da ta hada ire-iren halittu masu rai na duniya, wurin nan kuma yana da albarkatun dabbobi da tsire-tsire masu wadata, yana da halayen musamman sosai, halittu masu daraja wadanda kuma ke dab da karewa suna da yawan gaske. Cikin shekaru kusan 20 da suka wuce, an kago da kuma tattara al'adun gargajiya masu wadata wadanda addinin budda ne ke ba da muhimmiyar alama. Abubuwan tarihi da na al'adun gargajiya na tsaunin Emei suna da daraja sosai wajen tarihi da zane-zane da fannin bincike yadadawar kimiyya da kuma yawon shakatawa, su ne dukiyoyin tarayya na duk dan Adam.

An shigar da tsaunin Emei da babban Budda na tsaunin Leshan cikin "sunayen abubuwan tarihi na duniya" a shekarar 1996 bisa ma'aunin zabar irin wadannan abubuwan tarihi da na al'adun gargajiya. Kwamitin kula da abubuwan tarihi na duniya ya ba da daraja sosai cewa, a karni na farko, an gina haikalin addinin Budda na farko na kasar Sin a kan tsaunin Emei mai ni'ima da ke lardin Sichuan na kasar Sin. Bisa ginawar sauran haikalai da ke kewaye da shi, sai wannan wuri ya zama daya daga cikin muhimman wurare masu tsarki na addinin Budda. Cikin karni da yawa da suka wuce, an tattara al'adun gargajiya masu wadata. Daga cikinsu abu mafi shahara shi ne babban Budda na Leshan wanda aka sassaka a karni na 8 a kan wani babban dutse, wanda kuma kamar yake kallon wurin haduwar koguna guda 3. Buddan yana da tsayin ita 71, wato ya fi tsayi a duk duniya baki daya. Tsaunin emei kuma ya shahara a duniya sabo da ire-iren halittu masu rai na tsaunin sun yi yawan gaske, da tsire-tsire masu wadata, daga tsire-tsiren da ke shiyya mai zafi kadan zuwa ga gandunan daji na coniferus tree bisa manyan tsaunukan da ke wannan shiyya, kai har ana iya cewa, ba irin da babu, wasu itatuwa ma har suna da shekaru fiye da 1000.

Kogon Yungang da ke lardin Shanxi

Kogon Yungang yana kudancin Dutsen Wuzhou inda ke da nisan kilomita 16 da ke yamma da birnin Datong na lardin Shanxi wanda ke arewacin kasar Sin. Tun daga shekara ta biyu lokacin Xing'an ta daular Bei Wei, wato shekarar 453 ce aka fara haka wannan Kogon Yungang. An kammala yawancin ayyukan Kogon Yungang ne kafin shekarar 494, wato kafin daular Bei Wei ta kaurar da babban birninta zuwa birnin Luoyang, amma an dada sassaka mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta har shekarar 520 zuwa shekarar 525, wato yayin da ake cikin lokacin Zheng Guang ta daular Bei Wei. An sassaka Kogon Yungang bisa halin musamman da dutsen Wuzhou yake ciki. Tsawon wannan Kogon Yungang daga gabas zuwa yamma ya kai kilomita wajen 1. Wannan Kogon Yungang, inda abubuwa da yawa da aka sassaka su a cikin Kogon, yana da girma sosai. Amma ya zuwa yanzu, muhimman koguna 45 da manya da kananan akwatunan mutum-mutumi 252 kawai, inda ke da mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta fiye da dubu 51 suna kasancewa a nan duniya. Tsayin mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta mafi girma ya kai mita 17, amma tsayin na mafi karami bai kai centimita goma ba. Mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta da gwarzo da 'yan mata masu yin raye-raye da aka sassaka su kamar yadda suke nan duniya suke da rai. Wasu zane-zanen da aka mai da hankali kan yadda aka sassaka su a kan ginshikan koguna. Daga cikin wadannan zane-zane, za a iya ganin cewa, an yi amfani da fasahar nuna hakikanin halin da ake ciki da aka fara amfanin da ita tun daga daular Qing zuwa daular Han, wato tun daga shekarar 221 kafin haihuwar Anabi Isa zuwa shekarar 220 AD. Haka nan kuma an fara sassaka mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta da zane-zane a cikin Kogon Yungang da fasaha daban, wato fasahar nuna tunanin soyaya wadda aka fara yin amfani da ita lokacin da ake tsakanin shekarar 581 da shekarar 907, wato bayan an shiga daular Sui da ta Tang. Kogon Yungang da Kogon Mogao na Dunhuang da Kogon Longmen da ke birnin Luoyang su ne "Kogo 3 da ke cike da fasahohin zane-zane da aka yi su a kan dutse na kasar Sin", suna kuma daya daga cikin zane-zanen da aka sassaka su a kan duwatsu wadanda suke yi kaurin suna a duk fadin duniya.

Mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta da aka sassaka su a cikin Kogon Yungang suna da girma kuma suna da karfi sosai. Ban da wannan, ire-iren wadannan mutum-mutum suna da launi iri daban-daban. Sabo da haka, an ce, mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta suna matsayin farko daga cikin dukkan mutum-mutumin da aka sassaka su a cikin koguna daban-daban a nan kasar Sin a karni na 5. An kuma ce, Kogon Yungang shi ne wani wurin da ke da zane-zanen da aka sassaka su a kan duwatsu a da. Idan an raba su bisa lokutan sassaka su, za a iya raba su har kashi 3, wato lokacin farko da na biyu da na uku. Fuskokin mutum-mutumin da aka sassaka a wadannan lokuta 3 suna da bambanci kwarai. "Koguna 5 na Tanyao" da aka sassake su a cikin lokacin farko suna da girma kuma aka sassake su bisa al'adun yankunan da ke yamma da kasar Sin. Amma a lokaci na biyu, an mai da hankali sosai kan aikin sassakawa kuma da aikin kayatar da wadannan mutum-mutumin sosai. Sauye-sauye da adon da wadannan mutum-mutum a bayyane suke halin musamman na fasahohin zane-zane ne da ake ciki a lokacin daular Bei Wei. Kodayake kogunan da aka sassaka a lokacin uku suna kanana ne, amma fuskokin mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta sun kasance ramammun, girmansu ma suna daidai da na kogunan da suke ciki. Irin wadannan mutum-mutum sun zama zane-zanen koyo a baya lokacin da ake yalwata fasahar zane-zane na mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta a sauran wurare na Arewacin kasar Sin. Ban da wannan, irin wannan halin musamman shi ma asali ne ga fasahar sassaka mutum-mutum a ramamme. Bugu da kari, mutum-mutum masu yin raye-raye da masu yin tsalle da birkida iri iri sun bayyana zamantakewar jama'a ta daular Bei Wei kuma yaduwar addinin Buddha a nan kasar Sin.

Haka kuma a file ne mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta da aka sassaka su a cikin Kogon Yungang suka bayyana yadda fasahohin zane-zane irin nan addinin Buddha na kasar India da yankin Asiya ta Tsakiya suke zuwa nan kasar Sin, an kuma raya su har sun zama fasahar zane-zane irin ta addinin Buddha ta kasar Sin. Sun kuma bayyana tarihin yadda aka sassaka mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta dangane da fuskokin jama'a farar hula kuma irin wannan al'ada ta zama wata sashiyar al'adun kabilu daban-daban na kasar Sin. Masana sun ce, an riga an hada da fasahohin zane-zane iri daban-dabam, amma ba a taba yi a da ba a cikin Kogon Yungang. Tun da haka, hanyar Kogon Yungang ta zama wata muhimmiyar lokaci ga yaduwar addinin Buddha a nan kasar Sin. Kogon Yungang ya kuma yi tasiri sosai ga mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta wadanda suke bayyana al'adar lokacin daular Bei Wei kuma aka sassaka su a baya a Kogon Mogao na Dunhuang da Kogon Longmen.

An fara raya fasahar zane-zane irin na kogon bisa al'adar kasar Sin ne lokacin da ake raya fasahar zane-zane a Kogon Yungang. A lokaci na biyu, an fara sassaka gine-gine irin na fadan daulolin kasar Sin, kuma bisa wannan tushe, an fara sassaka akwatun bisa al'adun kasar Sin da suke kama da gidaje iri daban-dabam don mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta a cikin Kogon Yungang. Daga baya, an sassaka irin wadannan akwatuna sosai lokacin da aka haka koguna a wurare daban-dabam a nan kasar Sin. A lokaci na uku lokacin da aka haka koguna a Yungang, an shirya da kayatar da su kwarai. Koguna da akwatunan da aka sassaka su a cikin Kogon Yungang a lokaci na uku sun fi bayyana siffar gidaje da hanyar kayatar da gidaje da Sinnawa suka yi a waccan lokaci. Sun kuma bayyana cewa, an riga an hada fasahar zane-zane irin ta addinin Buddha da al'adar kasar Sin kwarai, har ta zama wata sashiyar al'adar kasar Sin.

A watan Disamba na shekara ta 2001 ne aka sa sunan Kogon Yungang a cikin takardar sunayen kayayyakin tarihi na duniya. Kwamitin kayyayakin tarihi na duniya ya ba da sharhi cewa, "Kogon Yungang wanda ke birnin Datong na lardin Shanxi ya wakilci fasahar zane-zane ta addinin Buddha irin ta kogo wadda ke samun yalwatuwa a karni na 5 da na 6. Daga cikinsu, "Koguna 5 na Tanyao" inda aka sassaka su bisa shirin da aka tsara kwarai, wani abu mafi kyau ne lokacin da fasahar zane-zane ta addinin Buddha ta kai matsayin koli a nan kasar Sin a karo na farko."

Tsohon wurin "mutanen Beijing" na Zhoukoudian

Tsohon wurin "mutanen Beijing" na Zhoukoudian yana tudun Longgu na kauyen Zhoukoudian na shiyyar Fangshan da ke kudu maso yammacin birnin Beijing da nisan kilomita 48. Nan ne wurin da ke tsakanin shiyyoyin tuddai da filayen karkara, a kudu maso gabashin wurin ya kasance da babban filin karkara na arewacin kasar Sin, a arewa maso yammacin wurin kuma akwai shiyyoyin tuddai. Yawancin shiyyoyin tuddai da ke kusa da kauyen Zhoukoudian duwatsun Limestone ne, sabo da amfanin karfin ruwa, shi ya sa akwai kogwan duwatsu manya da kanana da yawa a wannan wuri. A kan tudun kuma akwai wani kogon dutse wanda tsawonsa ya kai wajen mita 140 wanda kuma ake kira "kogon mutanen zamanin da masu kama da gwagguna". A shekarar 1929, an iske abubuwan da mutanen zamanin da suka bari cikin wannan kogo, don haka sai a ba wa kogon sunan "wuri na farko na Zhoukoudian".

Shiyyar Tsohon wuri na Zhoukoudian wani muhimmin wuri ne na zamanin tsoffin kayayyakin duwatsu da ke arewacin kasar Sin, wuri mafi shahara daga cikin su shi ne wuri na farko na Zhoukoudian wato tsohon wurin "mutanen Beijing" na zamanin da. Mr. Anterson, masanin ilmi na kasar Sweden shi ne na farko da ya gano wannan tsohon makwafi a shekarar 1921, daga baya kuma da akwai masanan ilmi da yawa wadanda suka yi bincike a nan. A shekarar 1927, Mr. Budasheng, masaninkasar Canada ya yi bincike ga tsohon wurin Zhoukoudian da gaske, kuma ya lakaba wa hakora guda 3 na mutum da aka gano a nan sunan "rukunin Beijing na mutanen zamanin da masu kama da gwagguna na kasar Sin". A shekarar 1929, Mr. Pei Wenzhong, masanin ilmi wajen binciken abubuwan tarihi na kasar Sin ya tono kashin kan "Mutumin Beijing" na farko na zamanin da, wannan ya girgiza duk duniya baki daya.

An shafe shekaru fiye da 80 ana ta tono abubuwan tarihi a tsohon wuri na Zhoukoudian, har yanzu ana ta yin ayyukan binciken kimiyya a can. An riga an yi hakar kogon dutse har fiye da mita 40 a wuri na farko, amma har ila yau ba a kai ga bincika rabin yawan abubuwan da aka jibge cikin kogon ba tukuna. Yawan fossil din mutanen zamanin da masu kama da gwagguna, da kayayyakin duwatsu, da fossil din mammal wato dabbobi masu shan nono, da tulin tokar da aka gano daga tsohon wurin zaman mutanen Beijing na Zhoukoudian dukkansu ba su misaltuwa da na sauran tsoffin wurare na wancan zamani.

Ban da wannan kuma a wuri na farko na Zhoukoudian, an gano abubuwan tarihi da aka bari wajen yin amfani da wuta, sabo da haka aka tsawaita tsawon tarihin dan Adam wajen yin amfani da wuta har shekaru dubu daruruka. A tsohon wurin an gano toka har hawa-hawa 5, da tulin toka guda 3 da kuma tarin kasusuwan da aka kona. Hawan toka mafi kauri ya kai mita 6. Wadannan abubuwan tarihi da aka bari sun bayyana cewa, mutanen Beijing na zamanin da ba ma kawai sun fadakar da kansu wajen yin amfani da wuta ba, har ma sun iya tanada garwashi.

Cikin abubuwan tarihin da aka tono kuma da akwai kayayyakin dubu daruruka wadanda dukkansu aka yi su ne da duwatsun da aka samu daga wuraren da ke kusa da tsohon wurin, wadannan kayayyakin duwatsu yawancinsu kanana ne, kuma samfurorinsu suna da yawan gaske. A farkon-farko akan yi manyan kayayyakin duwatsu musamman domin kada abubuwa masu nauyi. Daga baya kuma akan yi kananan kayayyakin duwatsu sirara kuma masu wuka. A karshe kuwa akan yi kayayyakin duwatsu masu kanana sosai, abu musamman na wannan lokaci shi ne kayan aiki mai tsini da aka yi da duwatsu domin huda abubuwa.

Bisa kayayyakin tarihin da aka tono, an iya tabbatar da cewa, mutanen zamanin da masu kama da gwagguna na Beijing sun yi zaman rayuwarsu a shiyyar Zhoukoudian yau da shekaru wajen dubu 200 zuwa dubu 700, suna ciyar da kansu ne musamman ta hanyar cire 'ya'yan itatuwa, sa'an nan kuma da yin farauta. Lokacin farkon- farko shi ne yau da shekaru dubu 400 zuwa dubu 700, lokaci na tsakiya shi ne yau da shekaru dubu 300 zuwa dubu 400, lokaci na karshe kuwa shi ne yau da shekaru dubu 200 zuwa dubu 300. Mutanen Beijing na zamanin da su ne mutanen zamanin jahiliyya wadanda suka yi zaman rayuwarsu a lokacin sauyawa daga gwagguna na zamanin da zuwa mutane masu basira, gano mutanen Beijing na zamanin da yana da muhimmiyar daraja kwarai wajen binciken ilmin halittu masu rai da na tarihi da bunkasuwar dan Adam.

Gano mutanen Beijing na zamanin da da yi musu bincike, sun daidaita gardamar da sassan kimiyya suka yi har kusan rabin karni wato tun bayan da aka gano mutanen Java a karni na 19 a kan maganar ko "irin mutane masu tsayawa a kan kafafuwansu" gwagguna ne ko kuma mutane. Hakikanan abubuwa sun bayyana cewa, a zamanin wayewar gari na tarihin dan Adam, idan an duba siffar jikin mutane da halin al'adu da kuma kungiyoyin zaman al'umma, sai a gane cewa, gaskiya ce a wani lokacin tarihi ya kasance da "mutane masu tsayawa a kan kafafuwansu" wadanda suke su ne jikokin "gwaggunan kudancin kasar", kuma su ne kakani da kakani na "mutane masu basira" wadanda suka bullo daga baya. "Mutane masu tsayawa a kan kafafuwansu" suna cikin wani muhimmin lokacin sauyawa daga gwagguna zuwa mutane. Har ila yau ma ana duba siffar jikin "mutane masu tsayawa a kan kafafuwansu" ne bisa ka'idar mutanen Beijing na zamanin da na Zhoukoudian, kuma har ila yau tsohon wuri na Zhoukoudian ya zama wani tsohon wuri wanda yake da abubuwan tarihi masu wadata, da tsari kuma mafi daraja daga cikin tsoffin wuraren dan Adam na wancan zamani na duniya. Bisa ma'aunin zabar kayayyakin tarihin gargajiya na tarihin duniya, a watan Disamba na shekarar 1987 an shigar da tsohon wurin mutanen Beijing na Zhoukoudian cikin"sunayen abubuwan tarihi na duniya". Kwamitin kula da abubuwan tarihi na duniya ne ya bayyana haka : Har ila yau ana nan ana ta yin ayyukan binciken kimiyya a tsohon wurin "mutanen Beijing" na Zhoukoudian. Ya zuwa yanzu, 'yan kimiyya sun riga sun gano tsohon wuri na mutanen Beijing daga cikin mutanen zamanin da masu kama da gwagguna na kasar Sin, kila sun yi zama rayuwarsu ne a zamanin sauyawa na tsakiya, sa'an nan kuma sun gano kayayyakin zaman rayuwa iri daban-daban, da tsohon wurin sabbin 'yan Adan wadanda suka yi zama a shekara ta 18000 zuwa ta 11000 ta BC wato kafin haifuwar Annabi isa alaihisallam. Tsohon wuri na Zhoukoudian ba ma kawai ya zama wata shaidar tarihi wadda ba safai akan ga irin ta ba da ta shafi zaman al'ummar dan Adam na babban yankin Asiya na zamanin da ba, hatta ma ya bayyana yunkurin sauyawar dan Adam.

Tsohon birnin Lijiang

Tsohon birnin Lijiang yana gundumar Lijiang ta kabilar Naxi mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin wadda aka gina shi a karshen zamanin daular Song da farkon zamanin daular Yuan (wato a karshen karni na 13). Tsohon birnin yana faffadan tsaunin Yunnan-Guizhou, nisansa sama daga leburin teku ya kai fiye da mita 2400, duk fadin birnin ya kai murabba'in kilomita 3.8, tun fil azal shi ne ya zama wata babbar kasuwa da kuma wani muhimmin gari wanda ya shahara wurare daban-daban. Yanzu tsohon birnin yana da mutane fiye da iyalan 6200 wato mutane fiye da 25000. Yawancin mutane daga cikinsu 'yan kabilar Naxi ne, kuma da akwai mazauna wajen kashi 30 bisa 100 wadanda har ila yau suke yin sana'o'in hannu da kasuwanci na gargajiya musamman yin kayayyakin tagulla da na azurfa, da yin jima da masaka da sana'ar yin giya.

Hanyoyin da ke cikin tsohon birnin Lijiang wadanda aka shimfida su ne ta hanyar dogaro bisa duwatsu kuma suna kallon ruwan koguna, kuma aka shimfida su da duwatsu masu launin ja, idan an yi ruwa ba za a ga tabo a kan hanya ba, a yanayin rani ma kura ba za ta tashi ba, a jikin duwatsu kuma akwai surori iri-iri na halitta kuma masu kyaun gani, wadannan hanyoyi sun dace da muhallin duk birnin sosai. Titin Sifangjie dake tsakiyar tsohon birnin yana wakiltar tsoffin hanyoyin birnin Lijiang.

An gina gadoji 354 bisa kogin Yuhe da ke cikin tsohon birnin Lijiang, wato a kowane murabba'in kilomita daya an gina gadoji 93. Wadannan gadoji suna da siffofi daban-daban, gadoji masu shahara daga cikin su su ne gadar Dashi da ta Wanqian da ta Nanmen da ta Maan da ta Renshou wadanda dukkansu aka gina su ne a zamanin daular Ming da na Qing (wato daga karni na 14 zuwa na 19). Daga cikin su gadar Dashi da ke da nisan mita 100 daga gabashin unguwar Sifang ta fi kasancewa mai sigar musamman.

Fadar "Mu" da ke cikin tsohon birnin da ma hukumar wani hakimi ta hanyar gado wanda sunan iyayensa "Mu" ne da ke birnin Lijiang, fadar nan wadda aka gina ta a zamanin daular Yuan (wato daga shekarar 1271 zuwa ta 1368), bayan da aka yi mata gyare-gyare a shekarar 1998 sai aka canja sunanta da ya zama cibiyar ajiye kayayyakin tarihi ta tsohon birnin. Fadar "Mu" tana da fadin fiye da kakada 3, da akwai dakuna manya da kanana 162 a cikin fadar. Cikin wadannan dakuna kuma an rataya alluna 11 masu dauke da kalmomin yabo da sarakuna na dauloli daban-daban suka bayar kyauta, wadannan alluna kuma sun bayyana tarihin tasowa da faduwa na babban iyalin "Mu".

Babban gini mai suna Wufeng na haikalin Fuguo da ke cikin birnin wanda aka gina shi a shekara ta 29 ta zamanin Wanli na daular Ming (wato a shekarar 1601), ginin yana da tsayin mita 20. Sabo da siffar ginin ta yi kama da fiffikau guda 5 sosai, shi ya sa an ba shi sunan "Wufenglou" wato fiffikau guda 5, a jikin rufin ginin kuma an zana surori masu kyaun gani. Ginin Wufeng ya hada halayen fasahar gine-ginen kabilar Han da ta Tibet da ta Naxi, ya zama wani gini mai daraja kuma mai gwada misalin koyo sosai wajen gine-ginen zamanin da na kasar Sin.

Gine-ginen gidajen jama'a na Baisha suna arewa da tsohon birnin Lijiang mai nisan kilomita 8, nan ne ya taba zama cibiyar shiyyar Lijiang wajen siyasa da tattalin arziki da al'adu a zamanin daular song (wato daga karni na 10 zuwa na 14). Gine-ginen gidajin jama'a na Baisha suna barbazuwa bisa wani muhimmin layin da ya tashi daga kudu zuwa arewa, a wurin da ke tsakiya na wadannan gine-gine kuma akwai wani babban fili mai siffar matataka, kuma ruwan marmaro ya shiga cikin babban filin daga arewa, kuma ya kasance da hanyoyi guda 4 wadanda ke tashi daga babban filin zuwa gefuna 4, suna da sigar musamman sosai. Gina gidajen jama'a na Baisha da kuma kyautata su sun aza harsashi ga tsarin fasalin tsohon birnin Lijiang da aka yi daga bayan.

Gine-ginen gidajen jama'a na Shuhe suna arewa maso yamma da tsohon birnin Lijiang mai nisan kilomita 4, sun zama wata karamar kasuwa da ke karkarar tsohon birnin, dukkan gidajen jama'a da ke cikin wadannan gine-gine suna wuraren da ya kamata, fasalinsu mai dacewa da zaman jama'a, da ni'imtaccen wurin ban sha'awa da fasahohin kabilu masu sigar musamman na birnin duk sun sha bamban da na sauran biranen gargajiya wadanda suka shahara a tarihin kasar Sin. Sigar musamman mai daraja ta girmama halitta da neman gaskiya daga abubuwan hakika na gine-ginen tsohon birnin sun bayyana halin kagowa da ma'anar ci gaba na dan Adam da aka bayyana cikin gine-ginen birane da garuruwa kuma bisa sharudan musamman na tarihi. Tsohon birnin Lijang wani wurin gargajiya ne wanda yake da muhimmiyar ma'ana kuma cunkushe da 'yan kananan kabilu, kasancewarsa ta samar da bayanoni masu daraja wajen binciken tarihin gine-ginen birane da na bunkasuwar al'umman dan Adam, shi ne al'adun gargajiya mai daraja na tarihi, shi ne abu mai daraja sosai na kasar Sin har ma na duk duniya baki daya, sabo da haka ya dace da dalilin shiga cikin "sunayen abubuwan tarihi na duniya".

Tsohon birnin Lijiang ya hada abubuwa masu kyaun gani na halitta da na dan Adam, kuma ya hada fasaha da tattalin arziki mai amfani. An shigar da tsohon birnin Lijiang cikin "sunayen abubuwan tarihi na duniya" a watan Disamba na shekarar 1997 bisa ma'aunin zabar irin wadannan abubuwan tarihi da na al'adun gargajiya. Kwamitin kula da abubuwan tarihi na duniya ya ba da daraja sosai cewa, tsohon birnin Lijiang ya hada muhimmin wurin tattalin arziki da na muhimman tsare-tsare da yanayin kasa mai wahalar zirga- zirga da kyau, ya kiyaye kuma ya sake bayyana halayen abubuwan tarihi sosai. Gine-ginen tsohon birnin ya sha juriyar wahaloli na dauloli masu yawan gaske, ya shahara ko'ina sabo da ya hada sigogi musamman na al'adun kabilu daban-daban. Birnin Lijiang kuma yana da tsarin samar da ruwa na tsohon zamani, wannan tsari ya ratsa ta ko'ina, kuma yana da sigar musamman mai kyau, kuma har ila yau ana yin amfani da wannan tsari.

Dutsen Huang

A kasar Sin akwai wani karin magana cewar, bayan da aka ziyarci shahararrun tsaunuka 5 na kasar Sin, ba za a ziyarci sauran tsaunuka ba, bayan da aka ziyarci dutsen Huangshan, ba za a ziyarci sauran duwatsu ba, abin da a ke nufi shi ne dutsen Huangshan shi ne dutsen da ya fi kayatarwa, in ka ziyarci Huangshan, to, za ka ji sauran duwatsu ba abin a zo a gani ba. Daga wannan kafin magana za a gane irin ni'immar dutsen Huangshan.

Dutsen Huangshan yana a cikin wuri mai ni'imma na Huangshan a tsakiyar kasar Sin, fadin wurin ya kai muraba'in kilomita dubu daya da 200. Dutsen Huangshan yana da tsayi kuma yana da kwari mai zurfi, kuma akwai hazo da danshi da yawa, kuma a kan yi ruwan sama.

Dalilin da ya sa dutsen Huanshan ya yi suna haka shi ne sabo da yana da irin ni'imma na sauran duwatsu gaba daya, musamman abubu 4. da farko shi ne pine wato wani irin ice na kasar Sin. Wadannan tsofaffin icen pine duk suna cikin ramin duwatsu, kuma sun mika saiwoyinsu barkatai, musamman icen pine mai suna maraba da baki da ke kan dutsen Yunu ya zama alamar dutsen Huangshan; na biyu shi ne duwatsu masu kama da daji, ina ana iya ganin duwatsu masu kyau; na uku shi ne tekun hazo. In ka hao kan dutsen Huangshan za ka ga hazo ya yi kama da teku da ke kewaye dutsen, lallai yana da kyaun gani; na hudu shi ne idon ruwa mai dumi da cikin dutsen Huangshan.

A dutsen Huangshan ana iya ganin sharudan yanayi iri iri, halitattun abubuwa suna zamansu cikin daidaici, itatuwa da ciyayi da ke kan dutse da gindin dutse iri iri ne. Fadin gandun daji ya kai kashi 56 cikin kashi 100, fadin ciyayi ya kai kashi 83 cikin kashi 100. musamman shahararren shayi mai suna Huangshanmaofeng da Huangshanlingzi duk sun yi suna a gida da waje. A cikin dutsen Huangshan akwai tsofaffin itatuwa iri iri. Ban da haka kuma akwai namun daji da tsuntsaye masu daraja da yawa da ke zamansu a nan.

Ban da irin wannan ni'immar wuri kuma akwai al'adun 'yan Adam da yawa a Huangshan. A cikin tarihin kasar Sin mawaka da mawallafa da yawa sun yi mamaki da irin kyaun Huangshan, kuma sun yi wallafe wallafe da yawa don yaba dutsen Huangshan. A cikin tarihin kasar Sin shahararrun masu tsara wakoki sun rubuta wakoki da yawa don yaba dutsen Huanshan, yawan wakokin da suka rubuta ya kai fiye da dubu 20.

A wajen zane, akwai wani rukun masu zane wadanda su kan yi zane iri na Huangshan mai kyau. Kuma su kan tsamo irin abubuwa masu kyau na Huangshan don yin zanensu. Masu daukar hoto na zamani kuma sun dauki hotuna masu dimbin yawa don shaida irin kyau na Huangshan. Ban da haka kuma akwai wata tatsuniya game da sarki na farko na al'ummar kasar Sin wato sarki Xianyuan. An ce, daga nan ne ya je aljana, har yanzu ma akwai wuraren da aka ba su suna sabo da harkokin da ya yi. Ban da haka kuma dutsen Huangshan yana da matsayi mai muhimmancin gaske ga darikar Dao.

A shekara ta 1990 ne an sa dutsen Huangshan mai ni'imma a cikin sunayen wuaren gado na halitta da al'adu na duniya. Kwamitin kayayyakin gado na duniya ya sharhanta cewa, dutsen Huanshan ya sha yabo kwarai da gaske a cikin tarihin wallafe wallafe da da al'adu na kasar Sin, masu ziyarar yawon shakatawa da suka zo daga wurare daban daban na duniya da mawaka da masu zane da masu daukar hoto za su yi wa dutsen Huangshan yabo har abada.

Babbar ganuwa

Babbar ganuwa ta kasar Sin ita ce daya daga cikin abubu 7 na ban alajabi na duniya, ita ce tsohon aikin tsaron soja da ta fi kasaita da aka gina cikin dogon lokaci a kasar Sin. Wannan babbar ganuwa ta mika har fiye da kilomita dubu 7. a shekara ta 1987 an sa babbar ganuwa a cikin sunayen kayayyakin gado na duniya. An fara gina babbar ganuwa ne tun kafin karni na 9 kafin haifuwar Annabi Isa. A wancan zamani domin hana hare haren da 'yan kabilun arewacin kasar Sin su ke kawowa mulkin tsakiyar kasar Sin sun gina ganuwa don hada tasmaharar gadi da ke hana hare haren da a ke kawo. A zamanin Chunqiu, mahukunta sun yi yakekeniya a tsakaninsu, sabo da haka manyan kasashe su ma sun yi ta gina ganuwa bisa tuddai a tsakanin kasa da kasa. Ya zuwa shekara ta 221 na kafin haifuwar Annabi Isa wato bayan da sarki Qinsihuang ya hada kasar Sin gaba daya, sai ya hada wadannan babbar ganuwa da aka gina har sun zama wata tasmaharar hana hare haren da sojojin doki na kabilar Mongolia ke kawowa daga makiyayar arewaci, a zamanin nan tsawon babbar ganuwa ya riga ya kai kilomita fiye da dubu 5. a sarautar Han ta bayan sarautar Qin tsawon babbar ganuwa ya kai fiye da kilomita dubu 10. a cikin shekaru fiye da dubu 2 na tarihi. Mahukutan kasar Sin na lokatai daban daban duk sun yi kokarin gina babbar ganuwa, adadin tsawon babbar ganuwa da aka gina ya kai kilomita dubu 50, wato ya fi tsawon kewayen duniya.

Babbar ganuwa da a ke gani yanzu yawancinsu an gina ne a sarautar Ming wato daga shekara ta 1368 zuwa shekara ta 1644, ta taso ne daga Jiayuguan na lardin Gansu a yammacin kasar Sin har zuwa bakin kogin Yalujiang na lardin Liaoning a arewa maso gabashin kasar Sin, ta ratsa larduna da birane da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu 9, tsawonta ya kai kilomita dubu 7 da 300, shi ya sa ana kira ta babbar ganuwa. Babbar ganuwa an gina ta ne bisa tuddai, kuma ta ratsa hamada da makiyaya da fadamu, maginan babbar ganuwa sun yi aiki bisa surar kasa iri daban daban don ta yi karfi sosai, wannan lallai ya shaida hikimar kakannin Sinnawa.

Da ya ke an gina babbar ganuwa a kan tuddai ne shi ya sa a waje da babbar ganuwa da ke kan tudu ya yi tsayi kwarai, sabo da haka a zamanin da ba mai yiwuwa ba ne sojoji 'yan Mongolia su hau kan irin wannan babbar ganuwa don kawo hari. An gina babbar ganuwa ne da manyan tubala da dutsatsu a waje an sa kasa da barbashin duwatsu a ciki, tsayinta ya kai mita 10, fadin babbar ganuwa ya kai mita 5, wato dawaki 5 suna iya tafiya a kai gaba daya don a yi sufurin abinci da makamai. Kuma akwai matattakara a cikin babbar ganuwa don sojoji su hau da sauka. A kan babbar ganuwa kuma akwai dakalin kunna wuta, domin a wancan zamani babu waya, sabo da haka idan an ga makiya za su kawo hari sai su kunna wuta, nan da nan duk sojoji masu gadi za su gane cewa, makiya za su zo, sai shu shirya don hallaka makiya. Kuma a kan kunna wuta a dakali daya bayan daya don sanar da labarin yaki ga sarki da jama'ar duk kasa.

A zamanin yau, babbar ganuwa ba aikin tsaron kasa bane, amma masu ziyarar yawon shakatawa su kan yi mamaki da irin wannan gini mai kayatarwa. Babbar ganuwa tana da girma da karfi. In an hanga za a ga babbar ganuwa da ke kan tuddai, ta yi kama da wani babban dodo. In an duba kusa da babbar ganuwa za a ga irin gine gine masu kayatarwa kamar wani zabe, tana shere mutane!

Babbar ganuwa tana da babbar daraja a wajen ziyarar yawon shakatawa don shaida al'adun tarihi na kasar Sin. A kasar Sin mutane su kan ce, in ba a zo babbar ganuwa ba ba jarumai ba ne. masu ziyarar yawon shakatawa da shugabannin kasa su kan yi alfahari saboda sun hau kan babbar ganuwa. Yanzu akwai wasu sassan babbar ganuwa da aka kiyaye da kyau misali babbar ganuwa ta Badalin da Simatai da Mutianyu na Beijing. A ganiyar gabas ta babbar ganuwa akwai babbar kofa ta farko ta kasar Sin wato Shanhaiguan, a ganiyar yamma ta babbar ganuwa akwai Jiayuguan na lardin Gansu, duk sun shahara sosai a wajen ziyarar yawon shakatawa, masu ziyarar yawon shakatawa da yawa suna zuwa wadannan wurare kullum.

Babbar ganuwa tana hade da hikima da kokarin da jama'ar kasar Sin suka nuna a zamanin da, ko bayan shekaru dubbai ma tana tsaye a kasar Sin, ta riga ta zama alamar ruhun al'ummar kasasr sin. A shekara ta 1987, an sa babbar ganuwa wadda ke alamanta al'ummar kasar Sin a cikin sunayen kayayyakin gado na duniya.

Kogon Mogao da ke Dunhuang

Kogon Mogao na Dunhuang da ke arewa maso yammacin kasar Sin ya fi girma daga cikin kogon da ke cike da zane-zanen addinin Buddha kuma har yanzu ke kasancewa a cikin hali mai kyau yanzu a duk fadin duniya. A shekarar 1987, an rubuta suna Kogon Mogao a cikin "Takardar Sunayen Kayayyakin Tarihi na Duniya". Kwamitin kula da kayayyakin tarihi na duniya ya ba da sharhi cewa, Kogon Mogao ya shahara sosai a nan duniya domin zane-zanen da aka yi a kan bango da mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta da aka yi a cikin kogon. Wadannan zane-zane da mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha sun nuna fasahohin addinin Buddha da aka yi a cikin shekaru fiye da dubu 1 da suka wuce.

An haka wannan Kogon Mogao ne a kan wani dutse mai suna Dutsen Mingsha da ke karkarar birnin Dunhuang. Daga kudu zuwa arewa na wannan Kogon Mogao ya yi kilomita kusan 2. Wannan kogo kuma yana da benaye 5 inda ke da kananan koguna masu dimbin yawa. Ana jin mamaki domin wadannan kananan kogo suna nan cikin hali mai kyaun gani.

Tun daga shekara ta 336 ce aka fara haka Kogon Mogao. A cikin dauloli da yawa, an yi ta haka sabbin koguna. Ya zuwa daular Tang, wato ya zuwa kamar shekarar 618 na karni na 7 da ya gabata, yawan kogo ya riga ya kai fiye da dubu 1. Sabo da haka, ana kuma kiran Kogon Mogao sai "Kogo da ke cike da mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta dubu 1".

Lokacin da mutanen dauloli daban-dabam suka haka wannan Kogon Mogao, sun yi mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta da zane-zanensu da yawa a cikin kogon. Kogon Mogao yana kan wani muhimmin wuri na Hanyar Siliki wadda take hade da al'adun gabas da na yammacin duniya, an kuma kawo addinai na yammacin duniya da al'adu da ilminsu a cikin wannan Kogon Mogao. Sabo da haka, lokacin da ake yi zane-zane da mutum-mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta, an kuma hada fasahohin yin zane-zane na yammacin kasashen duniya da na kabilun kasar Sin. A sakamakon haka, zane-zane da mutum-mutumin da aka yi a cikin Kogon Mogao sun fi jawo hankulan mutane.

Amma a cikin shekaru da yawa da suka wuce, an kuma lalace Kogon Mogao sosai. Yanzu, yawan kogon da suke kasancewa ya kai kusan dari 5 kawai. Zane-zanen da suke nan a cikin kogon sun kai murabi'in mita dubu 50, mutum-mutumin masu bin addinin Buddha ma sun kai dubu 2 kawai. Domin zane-zane da mutum-mutumi sun nuna bambanci sosai. Za a iya ganin al'adu daban-dabam na dauloli dadan-dabam na kasar Sin. Idan an sa wadannan zane-zane a kan layi daya, tsawon wannan layi zai kai kilomita kusan 30.

An yi galibin zane-zane a cikin kogon Mogao ne dangane da addinin Buddha. Kamar misali, mutumin da mabiya addinin Buddha ke yi masa bauta da mutum-mutumin da 'yan Buddha ke yi masa bauta da 'yan Ajanna da wasu labaru da tatsuniyoyi da mutanen tarihi da suka shahara a India da yankin tsakiyar Asiya da a kasar Sin. Ban da wannan, zane-zanen da aka yi a dauloli daban-dabam sun bayyana zamantakewar kabilu da tufafinsu da gine-gine da kide-kide da raye-raye da dai sauransu na dauloli daban-dabam. A cikin Kogon Mogao ma za a iya ganin tarihin yin musayar al'adun kasar Sin da na kasashen waje. Sabo da haka, masanan kasashen Turai sun ce, zane-zanen da aka yi a cikin Kogon Mogao suna nan kamar wani laburaren da ke kan bango.

Amma a hakika dai abin da ya fi bakin ciki shi ne a cikin shekaru masu dimbin yawa an saci kayayyakin tarihi na Kogon Mogao sosai.

A shekarar 1900, ba zato ba tsammani, an gano wani karamin kogo na ajiye litattafai a cikin Kogon Mogao. A cikin wannan karamin kogon da tsawo da fadinsa ya kai mita 3 bi da bi yana cike da litattafan addinin Buddha da zane-zane da saka da sauran kayayyakin tarihin fiye da dubu 50 wadanda ba a taba ganinsu a da ba. Wannan kayayyakin tarihi sun shafe tarihi da ilmin labarin kasa da harkokin siyasa da kabilu da harkokin soja da kalmomi da harsuna da fasahohin zane-zane da addinai da fasahohi da kimiyyar magani da dai sauran kusan duk fannoni na karni na 4 zuwa karni na 11. A sabili da haka, an kira su "Litattafai game da ilmomi daban-dabam na karni na da".

Bayan an gano wannan karamin kogo, masu kasada na sauran kasashen duniya masu dimbin yawa bi da bi ne suka je Kogon Mogao. A cikin shekaru kusan 20, sun saci litattafai iri daban-dabam kusan dubu 40 daga wannan karamin kogo da sauran zane-zane da mutum-mutumi masu daraja. Wannan ya haddasa hasara sosai ga Kogon Mogao. Yanzu, za a iya ga wadannan kayayyakin tarihi na Kogon Mogao da yawansu ya kai 2 bisa 3 a Ingila da Faransa da Rasha da India da Jamus da Denmark da Sweden da Korea ta Kudu da Finland da Amurka.

A sa'i daya, bayan an gano wannan karamin kogo, wasu masanan kasar Sin sun fara yin nazarin litattafan da ke cikin kogon. A shekarar 1910, karo na farko ne aka wallafa litattafai inda ke da sakamakon da aka samu domin nazarin litattafan addinin Buddha da aka ajiye su a cikin kogon. Sakamakon haka, an fara kafa ilmin Dunhuang da ya yi suna sosai a duk fadin duniya. A cikin shekaru gomai da suka wuce, masana na kasashen duniya sun mai da hankula da yin nazari sosai kan fasahohin zane-zane na Dunhuang. Masana na kasar Sin ma sun yi nazari kan ilmin Dunhuang sosai kuma sun riga sun sami fifiko sakamako.

Kogon Mogao na Dunhuang wani muhimmin wurin tarihi ne da ke nune-nunen al'adun kasar Sin sosai. Gwamnatin kasar Sin ta kan mai da hankali kwarai kan yadda za a iya kiyaye shi. Domin masu yawon shakatawa na kasashen duniya da suka ziyarci Kogon Mogao sun yi yawa a kowace shekara, gwamnatin kasar Sin ta riga ta gina wata cibiyar nune-nunen zane-zane na Kogon Mogaon Dunhuang a wurin da ke gabansa, inda aka gina wasu kogo domin ajiye wasu kayayyakin tarihi na Kogon Mogao a ciki. Sakamakon haka, za a iya kiyaye tsofaffin Kogon Mogao, masu yawon shakatawa ma za su iya kallo kayayyakin tarihi na Kogon Mogao.

A cikin 'yan shekarun nan, gwamnatin kasar Sin ta kuma zuba kudin Sin yuan miliyan dari 2 domin yin amfani da fasahar zamani wajen gina Kogon Mogao irin na zamani. Sabo da haka, za a iya kiyaye kayayyakin tarihi da al'adun Kogon Mogao na Dunhuang kamar yadda ya kamata.

Dakin ibada da gida da kabari na confucius

Confucius shi ne daya daga cikin manyan 'yan firosofiya na duniya, kuma shi ya kago darikar Confucius. Dakin ibada da gida da kabari da aka gina don tunawa da Confucius su ne alamar da sarakunan kasar Sin suka kafa a shekaru dubu 2 da suka shige don nuna ban girma ga Confucius da darikar Confucius. Suna da muhimmin matsayi a cikin tarihin kasar Sin da al'adun gabashin duniya.

Dakin ibada na Confucius da gidan Confucius da kabarin Confucius suna garin Confucius wato birnin Qufu na lardin Shandong a gabashin kasar Sin.

Ana kira Dakin ibada na Confucius dakin ibada na farko a kasar Sin. A shekara ta 478 na kafin haifuwar Anabi Isa, wato shekara ta biyu bayan rasuwar Confucius, sarkin kasar Lu ya gina tsohon gidansa da ya zama dakin ibada, an ajiye tufafinsa da kayayyakinsa. A wancan lokaci, dakuna uku kawai. Daga bisani al'adun darikar Confucius ya zama al'adun gaske na kasar Sin, sarakunan kasar Sin sun yi ta habaka dakin ibada na Confucius, har sun zama manyan dakuna masu kayatarwa. Ya zuwa farkon karni na 18, sarki Yongzheng na szarautar Qing ya ba da umurnin gyara dakin ibada bisa babban mataki, har ya zama irin salon da mu ke gani.

Tsawon Dakin ibada na Confucius daga kudu zuwa arewa ya kai mita dubu daya, fadinsa ya kai muraba'in kilomita dubu 100, akwai dakuna kusan 500, girmansa yana bayan tsohuwar fada ta Beijing kawai. Lallai misalin koyo ne ga dakunan ibada na kasar Sin.

An gina dakin ibada na Confucius ne bisa fasalin fadar sarki. Yana da wani layin tsakiya na daga kudu zuwa arewa, an gina manyan dakuna a kan wannan layin tsakiya, kuma an gina dakuna a gefuna biyu na wannan layi. Dakin ibada na Confucius yana da hawa 9, da farfajiya 9, babban gini mai suna Dacheng yana da fadin dakuna 9. Da ma sai sarki yana da ikon yin amfani da 9 don gina fadar sarki, idan farar hula su gina gida mai dakuna 9, to ya taka doka ke nan, za a yanke masa hukuncin kisa, amma dakin ibada na Confucius halal ne. An gina babbar kofar dakin ibada na Confucius ne bisa tsarin fadar sarki, wato hawa 5.

Babban daki mai suna Dacheng shi ne cibiyar dakin ibada na Confucius, tsawonsa ya kai mita 30, fadinsa daga gabas zuwa yamma ya kai fiye da mita 50, kuma an gina rawayen rufi, yana da kayatarwa irin na fadar sarki. A gaban babban dakin nan kuma akwai manyan ginshikan duwatsu 10 da aka yi sassakar dodo, irin kyaunsa ya kai fiye da na tsohuwar fada.

A cikin dakin ibada na Confucius kuma an ajiye manyan duwatsu fiye da dubu 2 da aka sassaka bayani. Duwatsun da aka sassaka bayanonin da sarakuna suka rubuta sun kai fiye da 50, wannan sosai ya shaida matsayi mai daukaka na Confucius a kan tarihin kasar Sin.

Gidan Confucius yana dab da dakin ibada na Confucius, wato gida ne na jikokin Confucius. Shi ne babban gidan da ke bayan fadar sarki kawai.

An fara gina gidan Confucius ne a sarautar Song wato a karni na 12, fadinsa ya kai muraba'in mita dubu 50, gidan nan yana da dakuna kusan 500. Gidan Confucius yana da salon musamman, a gaban gidansa dakuna ne na yin harkokin gwamnati, a baya kuma dakuna ne na zaman yau da kullum. Irin dakunan karbar baki suna da surar sarautar Ming da Qing. A cikin gidan Confucius akwai takardun tarihi da tufafi da kayayyaki na zamanin da masu daraja da yawa.

Kabarin Confucius kabarin musamman ne da aka binne jikokin Confucius, shi ne kabarin da ya fi girma da ya fi dade a duniya. An yi amfani da wurin nan don binne jikokin Confucius har cikin shekaru dubu 2 da 500, fadinsa ya kai muraba'in kilomita 2, akwai karburbura fiye da dubu 100 na jikokin Confucius, kuma an kafa duwatsu fiye da dubu 5 da aka sassaka bayanoni.

Kabarin Confucius yana da amfani kwarai a wajen bincike ci gaban siyasa da tattalin arziki da al'adu da jana'iza na zamani daban daban na kasar Sin.

Dakin ibada da gida da kabari na Confucius sun shahara a duk duniya ba sabo da kayayyakin al'adu masu dimbin yawa kawai ba, kuma sabo da halitattun abubuwa. Misali a wurin nan akwai tsofaffin itatuta fiye da dubu 17 wadanda ke shaida dadadden tarihi na darikar Confucius, kuma suna da amfani kwarai a wajen bincike yanayi da halita na tsohon zamani.

Dakin ibada da gida da kabari na Confucius suna da kayayyakin al'adu da yawa, kuma da dadadden tarihi, sabo da haka suna da babbar daraja a wajen bincike kimiya da fasaha. A shekara ta 1994, kwamitin kayayyakin gado na duniya na kungiyara UNESCU ya nada dakin ibada da gida da kabari na Confucius da ya zama kayayyakin gado na duniya.

Tsohon birnin Pingyao na zamanin da a lardin Shanxi

A shekarar 1997, an rubuta sunan tsohon birnin Pingyao na zamanin da na Lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin cikin littafin rubuta sunayen shahararrun kayayyakin tarihi na duniya. Kwamitin kula da kayayyakin tarihi na duniya ya kimanta darajarsa cewa, tsohon birnin Pingyao da aka gina a zamanin da shi ne wani tsohon brinin guduma ne da aka kare shi sosai da sosai a cikin kasar Sin, ya bayyana wa mutane wani cikakkun hotunan da ba a taba gani ba na nuna bunkasuwar da aka samu wajen al'adu da zamantakewar al'umma da tatalin arziki da addini a duk tsawon lokacin bunkasuwar kasar Sin a tarihi.

An soma gina tsohon birnin Pingyao a wajen karni na 9 kafin bayyanuwar Annabi isa (A.S), sifar tsohon birnin tana tamkar mai kaman shan soro wato Square cikin Turanci, yawan fadinsa ya kai murraba'in kilomita 2.25 kawai. Manyan gine-gine da tsarin shimfidu su na tsohon birnin da ke kasancewa a yanzu an kammala gina su ne kafin shekaru 600 da suka wuce, katangu da tituna da gidajen kwana na jama'a da shaguna da kantuna da haikali da saruan gine-gine suna nan a tsaye lami lafiya, daram sun bayyana al'adu da tunani na gargajiya na kabilar Han ta kasar Sin da aka yi cikin shekaru dubbai, birnin ya riga ya zama dakin nuna kayayyakin tarihi da fasahar gine-gine na lokacin daular Ming da daular Qing (1368-1911)

An soma gina katangun tsohon birnin kafin shekaru 2800 , a wancan lokaci, an gina ta ne da kasa kawai. Ya zuwa shekarar 1370 na bayyanuwar Annabi Isa(A.S), an sake gyara katangun tsohon birnin ta hanyar yin amfani da duwatsu da tubala, kuma an yi ta kara ingancinsu. Ya zuwa yanzu, katangun tsohon birnin suna kasancewa cikin tsoffafin sifofinsu.

Duk tsawon katangun tsohon birnin Pingyao ya kai mita fiye da dubu 6, tare da tsayin da ya kai mita 12. Sifar katangar ta kasance tamkar sifar kunkuru , sa'anan kuma na da kofofi guda 6, a kowace katangar ta kudu da ta arewa, akwai kofa guda daya, sa'anan kuma na da kofofi biyu a kowace katangar ta gabas da ta yamma . Kofar da ke kudancin katangar tsohon birnin ta yi kama da kan kunkuru, a wurin waje da kofar, an sami rijiyoyi guda biyu wadanda suke alamanta cewa, idannu biyu na kunkuru ne. Kofar arewa tana alamanta cewa, ita ce wutsiyar kunkuru, inda aka sauka kasa sosai bisa leburin duk birnin , ruwan da aka tattara daga duk birnin yana malalawa kuma yana fitowa zuwa waje daga wurin nan . A cikin al'adun gargajiya na kasar Sin, kunkuru ya yi alamar wadanda ke da tsawon rai, sifar katangar ta bayyana cewa, tsofaffin mutane na zamanin da na kasar Sin suna son birnin Pingyao zai kara inganta tamkar yadda duwatsu suke yi ta hanyar yin amfani da karfi mai ban mamaki da kunkuru ya samar har abada.

A cikin birnin da aka rufe kofofinsa, babban titin da ke ratsa tsakiyar birnin ya zama layin ginshikin birnin daga kudu zuwa arewa, manyan tituna da kananan unguwoyi sun kasance tamkar gizagizai,duk birnin ya shimfidu bisa tsarin da aka tsara yadda ya kamata da kuma na da bambancin amfaninsu.

Gine-ginen gidajen kwana na jama'a suna da farfajiyar da aka keyane su a fannoni hudu, kuma an gina su ne da tubala masu launin baki da kwanuka masu launin toka bisa manyan layi layi, an yi su ne tamkar yadda tagwaye suke tsayawa fuska da fuska, an yi bambancinsu sosai bisa manya da kanana. An rufewar kowace farfajiyar, tsayin katangarsu na da tsawo mita 7 zuwa 8. Mazaunan jama'a na tsohon birnin Pingyao na da halayen musamman sosai, wato manyan dakunansu suna kasancewa cikin siffofin ramukan da aka haka domin yin zama a ciki a shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin, an kuma sassaka katako da tubala da yanke takardu don su zama hotuna iri iri, kai ,siffofinsu sun bayyana halin da ake ciki a kauyuuka. Yawancin mazaunan jama'a fiye da 400 da har yanzu suke kasancewa a tsohon birnin Pingyao an gina su ne a lokacin daular Ming da daular Qing , daga cikinsu da akwai 400 ko fiye da aka kare su sosai da sosai, su ne garken mazaunan jama'a na zamanin da da aka kare su sosai da sosai a shiyyar da 'yan kabilar Han ke zama a cunkushe a halin yanzu.

A cikin tsohon birnin, tarin gine-ginen haikali guda 6 da shaguna da kantunan da ke jere a gefunan tituna biyu dukansu hakikanin gine-gine ne da aka gina a da, shagunan da aka rufe su da kwanuka masu haske tare da launukan rawaya da kore da gidajen da aka rufe da kwanuka masu launin baki suna bayyana alamar bambancin matsayin rukuni rukuni. Wadannan gine gine da ke da halayen zamanin da sosai da sosai ne suka bayyana halin da ake ciki na samun bunkasuwar kasuwanni a lokacin daular Ming da daular Qing.

Birnin Pingyao na da kayayyakin tarihi mai tsayin gaske. Alal misali,fadar kafa mutum mutumi masu bin addinin Buddah na haikalin Zhenguo da ke arewa maso gabashin birnin, ita ce ke bisa matsayi na uku na kasar Sin wajen gina gine-gine da katako, yana da tarihi da yawan shekarunsa ya wuce dubu. Kayayyakin sassaka masu launuka iri iri da aka yi a lokacin karni na goma a cikin fadar nan su ne sun zama samfurorin ba da misali da ake yin amfani da su don binciken kayayyakin sassaka na zamanin da na kasar Sin. ban da wannan kuma, da akwai haikalin da ake kira "Shuan Lin" wanda aka soma gina shi a karni na 6. A cikin manyan fadarsa fiye da goma, da akwai mutum mutumi fiye da dubu 2 da aka sassaka da kasa a karni na 13 zuwa na 17 , an daukaka darajarsa cewa, shi ne siton da aka ajiye kayayyakin fasaha masu launuka iri iri da aka sassaka a zamanin da a kasar Sin. Ban da wannan kuma, daga wuraren da ke cikin tsohon birnin da kuma waje da shi koina ana iya ganin duwatsun da aka sassaka kalmomi a kansu a zamanin da , yawansu ya wuce dubu.

Tsohon birnin Pingyao na da matsayin musamman a gun tarihin aiwatar da harkokin kudi na zamanin yau da muke ciki a kasar Sin. A shekarar 1824, a tsohon birnin Pingyao, an sami wani bankin farko da ake kira "Ri Sheng Chang" a kasar Sin, ya gyara tsarin gargajiya na biyan tsabar kudi don ya zama hanyar yin amfani da takardar bill . Sa'anan kuma, "Ri Sheng Chang" ya kafa rassansa a ko'ina a kasar Sin, har ma ya habaka zuwa kasar Japan da Singapore da Rasha da saruan kasashe, an taba kiran shi da cewar wai lambawan a duniya. Bisa albarkacin jagorancin "Ri Sheng Chang", sha'anin bankuna na Pingyao ya sami bunkasuwa da saurin gaske, a lokacin bunkasuwar, an sami bankuna har 22 ko fiye. Yawansu ya kai rabin yawan bankunan kasar Sin a wancan zamani, ya zama cibiyar harkokin kudi na kasar Sin.

babban titin da ke yammacin tsohon birnin Pingyao na yanzu, titi ne na aiwatar da harkokin kudi kafin shekaru fiye da dari. Har zuwa yanzu, a titin yammacin birnin, akwai bankuna a jere layi layi , kuma suna ci sosai da sosai. A cikin wadannan bankuna, ana iya gano bankin da ake kira "Ri Sheng Chang", wato bankin farko na kasar Sin , bankin nan ba ya da girma, balle a ce yana da karfin bajinta , amma game da gidan nan da ke nisa da cibiyar titin nan ya taba zama babbar cibiyar harkokin kudi da ta hada da tsarin harkokin kudi na gida da na waje.

Tsohon birnin Pingyao na zamanin da ya taba samun wadatuwa sosai, ya zuwa yanzu, yana ci gaba da cike da karfin jawo hankulan mutane, wata katangar zamanin da ta kasa sabon birnin gunduma na zamanin yau cikin duniyoyi guda biyu da ke da bambancin siga. Tituna da shaguna da gine-ginen kasuwanni da ke cikin katangar sun shimfidu ne bisa tsarin da aka yi kafin shekaru 600, amma wurin da ke waje da katangar, ana kiran shi sabon birni. Wannan ne wuri mai kyau sosai da aka hada da gine-gine na zamanin da da na yanzu da kuma jawo hankulan mutane sosai da sosai.

Kabarin Sarki na farko na Daular Qin

Kabarin Sarki na farko na Daular Chin yana nan ne a Kauyen Yanzhai dake wurin da ke nisan kilomita 5 daga Gabashin gundumar Lintong ta Lardin Shaanxi. Kudancin kabarin ya dogara bisa Tudun Lishan . Arewacinsa kuma yana fuskantar Kogin Weishui . Daga sararin sama ana ganin cewa, Kabarin kamar wani babban dala wato Al Ahram.

Fasalin kabarin Sarki na farko na Daular Chin ya kwaikwayi zayyane-zayyane da gine-ginen birnin Xianyang, hedkwatar Daular Chin . Babbar Fadar dake karkashin kasa ta alamanta Fadar Sarki mai haske . Fadin kabarin ya kai muraba'in kilomita 66.25 wanda ya ribanya fiye da sau daya kan umguwar birnin Xi'an ta yanzu .

Sarki na farko na Daular Chin ya fara gina kabarinsa tun bayan da ya hau kujerar sarki a lokacin shekarunsa 13 da haihuwa. Da ya dinke kan kasashe 6 , ya tattara mutane fiye da dubu 100 daga wurare daban daban don su ci gaba da gine-ginen kabari har ya mutu yana da shekaru 50 da haihuwa . Wato an yi shekaru 37 kafin a gama aikin gina kabarinsa . Bisa lattafin tarihin da aka rubuta , an ce , an haka farfajiyar Kabarin a karkashin ruwan marmaro, sa'an nan kuma an karfafa shi da tagulla. A cikin fadar kabarin an ajiye lu'u lu'ai da kayayyaki masu daraja da yawa . Don hana yi masa sata , a cikin dakin kabarin an sa wani kayan baka da kibiya wanda a kowane lokaci in an yi motsi sai kibiya ta tashi .

A kewayan kabarin an ajiye gumakan dawaki da mutum-mutumin sojoji da yawa. Zayyanar kabarin ta bayyana babban iko da martabar Sarki na farko na Daular Chin .

A shekarar 210 kafin hijira , Sarkin ya mutu a wurin da ake kira Pingtai na Lardin Hebei. A watanni biyu bayan mutuwarsa aka kai gawarsa zuwa birnin Xianyang kuma an yi bikin jana'iza .

Lokacin da ake binne gawar Sarkin , Hu Hai , sarki na biyu na Daular Chin ya ba da umurnin cewa , a binne dukannin matan Sarki na farko tare da mijinsu . Mutanen da suka haka kabarin kuma za a binne su don kare asiri .

A bayan shekarar 1949, masu binciken abubuwan tarihi na kasar Sin sun yi binciken kabarin Sarki na farko na Daular Chin . A kewayan fadar karkashin kasa sun haka koguna fiye da 200 , sa'an nan kuma sun gano koguna biyu wadanda barayi suka haka. Daya yana arewa maso gabashin Kabarin. Daya kuma yana yammacin kabarin. Yanzu an riga an rufe kogunan.

© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China