>
Babi23: Kayayyakin Kida
Kayayyakin Kida

>>[Kayan Busawa na Kabilu]

Kayan bugawa mai suna Rewapu wanda mutane na kabilar Weigur da kabilar Tajike da kabilar Uzbeike dukkansu suna son irin kayan bugawa kwarai. Daga karni na l4 na bayan bayyanuwar Innabi Isa har zuwa yanzu akwai tsawan shekaru fiye da 600.A wancan lokaci, mutane na jihar Xinjiang da na sauran wurare na gida da na kasashen waje suna yin cudanyar juna sosai, kuma sun yi musanye musanye kan sassa daban daban kamar tattalin arziki da ciniki da al'adu. Bayan da aka yi cudanyar sai mutane na kabilar Weigur sun tsamo kayayyaki da kyau daga wuraren dake waje da su, kuma bisa tushen kayayyakin bugawa na kabilarsu, sai sun kago wadansu sabbin kayayyakin bugawa da kayayyakin gogewa. Kayan bugawa mai suna Rewapu shi ne daya daga cikin wadannan sabbin kayayyakin bugawa da aka kago.

Da katako ne an yi wannan kayan bugawa, kuma sigarsa mai kyakkyawan gani sosai, wannan kayan bugawa mai suna Rewapu yana da wuya mai dogo sosai, a karkashinsa kaman wani rabin kwallon kwando.

Da gashin awaki ne an yi layi layi wato a lokacin da ake bugawa sai ana kada wadannan ligiyoyin layi layi, muryarsa mai dadin ji sosai.

Mutun daya ya iya bugawa wannan kayan bugawa mai suna Rewapu, bugu da kari kuma mutane da yawa ma suna iya bugawa tare.

A jihar Xinjiang mai ikon tafiyar da harkokin kanta akwai musulmai da yawa, kuma akwai kabilu iri daban daban, misali kabilar Weigur da kabilar Tajike da kabilar Uzbeike dukkan mutane nawadannan kananan kabilu suna son bugawa ga irin kayan bugawa mai suna Rewapu, masu bugawa suna iya tsayawa kuma suna iya zaune kan kujera, kai irin kayan bugawa da ake bugawa cikin halin anashu'a sosai, Mutanen dake kewaye masu bugawa suna yin raye raye cikin farin ciki sosai.(Dije)

Saurari: Rewapu Tawa

Liuqin

Kayan bugawa mai suna Liuqin kaman irin kayan bugawa mai suna pipa, da katako ne akan yi shi, kuma surarsa kaman ganyen ice sabo da haka ne ana kiransa mai suna Liuqin. Surar kayan bugawa mai suna liuqin da fasalinsa dukkansu kaman na kayan bugawa mai suna Pipa. Tun a farko ne fasalin wannan kayan bugawa a saukake ne sosai,an ce, irin kayan bugawa sai manoma na kauye ne sukan yi amfani da shi don yin kide kide.

Tun a zamani na da ne a wurare na lardin Shandong da na lardin Anhui da na lardin Jiangsu, wato a lokacin da ana yin wasan opera na wuri wuri ne sai ana bugawa irin kaya mai suna Liuqin.

Irin kayan bugawa mai suna liuqin ba ma kawai surarsa kaman na kayan bugawa mai suna Pipa ba, hatta ma fasahar bugawa ma tana kaman buga kayan bugawa mai suna pipa.

In mai bugawa ya zauna kan kujera, sai hannun hagu ya dauke da wannan kayan bugawa mai suna liuqin, kuma hannun dama yana fara bugawa da yatsa.

A karshen shekara ta l958, wani shahararren mai yin bugawa mai suna Wang huiran tare da sauran ma'aikata na yin irin kayan bugawa sun kago wata dabarar yin irin kayan bugawa mai suna liuqin, a karshe dai sun sami nasara da yin irin kayan bugawa mai suna liuqin na sabon salo.(Dije)

Saurari: Mu Mian ta yi furani

Guqin

Kayan kida mai suna Guqin wani tsohon kayan kida ne na kasar Sin. A tsohon zamanin da, sunan Guqin da ake kira Yaoqin, wato tun da dadewa ne misali kafin shekaru fiye da 3000 da suka shige wato a daular zhou, mutanen kasar Sin sun fara yin amfani da wannan kayan bugawa mai dadi sosai.

Sigar wannan kayan kida mai suna Guqin mai kyaun gani sosai, kuma muryarsa mai dadi ji, irin kide kiden da aka bugawa yana iya sifanta halin mutu sosai.A tsohon zamani na da, in mutane sun fara buga wannan kayan bugawa, sai an yi share fage sosai, da farko an yi wanka da canja tufaffi, sa'an nan, an kona turare, an zauna da hada kafaffuwansa, an aza kayan bugawa mai suna Guqin a kan kafarsa ko a kan tebur. In an fara bugawa, da hannun hagu ana bugawa, da hannun dama yana ba da taimako wajen bugawa, duk bugun da aka yi na iya tafiya har zuwa nesa sosai.

Yaya ake kera wannan kayan bugawa mai suna Guqin? Kai da wuya sisai a daular Tang da daular Song, mutane sun fi nuna sha'awa ga buga wannan kaya, amma daga baya, irin fasahar yin wannan kayan bugawa ba a iya karba ba, kuma girmansu sun sha bamban.

A cikin 'yan shekaru da suka shige, wadansu mutanen kasar Sin sun yi kokarin bincike fasahar yin wannan kayan bugawa, har sun yi gyare gyare ga irin kayan bugawa, wato bayan da suka bincike wani tsohon kayan bugawa mai suna Guqin, sai sun kyautata wadansu kayayyakin dake ciki, sun kuma kara wasu a ciki, ta haka ne irin muryar da aka buga tana kara dadin ji sosai.

Irin wannan kayan bugawa mai suna Guqin ya iya bayyana abubuwa da yawa, wato in an yi farin ciki, sai wannan muryar da aka buga za ta iya nuna farin ciki da kara wa mutane farin ciki sosai. Amma, in mutane sun yi bakin ciki, sai irin muryar da aka buga ya iya bayyana bakin ciki na mutun, Wannan kayan bugawa ya kuma iya bayyana halayen halitta iri iri.

Hanyoyin kayan bugawa mai suna Guqin iri daban daban, wato mutun daya kawai ya iya bugawa, kuma mutane su iya bugawa tare, haka kuma tare da sauran kayan bugawa ne an iya buga wannan kayan bugawa mai suna Guqin tare. Kuma a lokacin da mawaka suke rerawa sai an iya buga wannan kayan Giqin don kara bayyana halin da mawaka suke iya nunawa.(Dije)

Saurariļ¼š Duwatsu da Kogi

Jiayeqin

Kayan bugawa mai suna Jiayeqin shi ne tsohon kayan bugawa na kabilar Korea, a jiha mai ikon kula da harkokin kanta ta kabilar Korea dake arewa maso gabashin kasar Sin, surar irin kayan bugawa mai suna Jiayeqin ta yi daidai da ta kayan bugawa mai suna Guzheng na kabilar Han, kuma yana da dogon tarihin dake hade da kayan bugawa mai suna Guzheng. Bisa abubuwan da aka rubuta kan takardar tarihi, a cikin shekaru 500 na kafin bayyanuwar Annabi Isa, akwai wata kasa mai suna Jiaye, sai wani sarki na kasa mai suna Jiaye na tsohon zamani na Korea ya kwaikwayo wajen kerar wani kayan bugawa kaman na kayan bugawa mai suna Guzheng, sai mutane na kabilar Korea suna kiran wannan kayan bugawa haka "Jiayeqin".

Tun daga farko har zuwa yanzu, wato bayan da aka fara yin irin kayan bugawa mai suna jiayeqin sai tsawon tarihinsa ya kai shekaru fiye da l500. A tsohon zamani na da, da wani ice ne aka yin kayan bugawa mai suna Jiayeqin, amma daga baya, an yi gyare gyare ga irin kayan bugawa mai suna Jiaye, sai fasahar yin irin kayan bugawa tana nan tana kara samu kyautatuwa sosai. A karshe dai an yi wani irin kayan bugawa mai kyau sosai, kuma yana da inganci sosai.

Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin,irin kayan bugawa mai suna jiayeqin ya kara samu kyautatuwa, wato masu yin kayan bugawa suna ta bincike da koyon sabuwar fasaha wajen kera shi, an kuma kara karfin muryarsa da wadansu kananan kayayyaki a ciki, kuma muryarsa yana kara dadin ji sosai.

Masu yin irin kayan bugawa suna zaunawa, da hannu daya ne ya iya bugawa da tabowa tare, wato irin muryar da aka buga tana da dadin ji kwarai.

Mutun daya ya iya bugawa wannan kayan bugawa mai suna jiayeqin, kuma cikin taraya ne akan yi kide kiden nan, daga nesa ne ana iya saurarar wannan kide kide masu dadin ji sosai.(Dije)

Saurari: Samari mai suna Ali

Huobusi

Wani tsohon kayan bugawa mai suna Huobusi, mutanen kabilar Mongoliya suna son buga irin kayan bugawa sosai. Bisa lafazin da aka yi ana sha banban wajen karanta sunan wannan kayan bugawa.

A tsohon zamani na da, mutane na arewancin kasar Sin suna kwaikwayo kayan bugawa mai suna Guzheng sai sun kera irin kayan bugawa mai suna Huobusi, surar wannnan kayan bugawa kaman wani babban cokali, wato ba na tsawo sosai ba.

Masu dauke da irin kayan bugawa mai suna huobusi, hannu daya yana bugawa, muryar wannan kayan bugawa mai karfi kuma mai dadin ji kwarai. Kullun mutun daya yake bugawa ko mutane da yawa sukan bugawa tare ko tare da yin raye raye, wato akan bi hanyoyi daban daban wajen buga wannan kayan bugawa mai suna huobusi.

Daga karni na l3 zuwa karni na l4 na bayyanuwar Annabi Isa, an fara buga wannan kayan bugawa mai suna huobusi, A wancan lokaci, an mai da kayan bugawa mai suna huobusi a kan matsayin gwamnati ne, wato a lokacin da akan yi kasaitaccen biki ne akan buga wannan kayan bugawa mai suna huobusi, A karshe dai sai farar hula su ma sukan yi wasa da wannan kayan bugawa don jin dadi.

Zuwa Daular Qing, ban da a gun kasaitattun shagulgulan da a kan shirya, an yi wasa da wannan kayan bugawa mai suna huobusi, haka kuma a lokacin da sarakuna na daular Qing suke farauta, sai ana bugawa irin kayan bugawa mai suna huobusi don kara karfin farauta da shan nishadi, kuma suna jin dadi sosai.

Sabo da dalilai da yawa ne sai a karshen Daular Qing ba a yi amfani da irin kayan bugawa mai suna huobusi a cikin fadar sarakuna na daular Qing ba.

Amma, bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, bayan da masu kide kide sun yi matukar kokarin bincike irin kayan bugawa mai suna huobusi, sai sun kwaikwayo irin kayan bugawa mai suna huobusi da aka fitar daga karkashin kasa, a karshe dai an kago wani irin kayan bugawa mai suna huobusi na sabon salo mai kyau sosai. Yanzu, mutane na kabilar Mongoliya sukan yi amfani da irin kayan bugawa mai suna buobusi don shan nishadi da nuna wasanni iri iri tare.(Dije)

Saurari: Tuta na Asi'er

Dongbula

Kayan bugawa mai suna Dongbula shi ne tsohon kayan bugawa na kabilar Hasake, a wadansu iyalai na kabilar Hasake, dukkan 'yan iyalansu sun iya bugawa irin kayan bugawa. A cikin yaren Hasake,ma'anar Dongbula ita ce muryar bugawa mai dadin ji ta kayan bugawa mai suna Dongbula.

Tsawon tarihi irin kayan bugawa mai suna Dongbul ya yi dogo sosai da sosai,Wato a karni na uku na bayan bayyanuwar Annabi Isa, sai mutane na jihar Xinjiang sun fara yin amfani da shi wajen yin nishadi.

Da katako ne an yi wannan kayan bugawa mai suna Dongbula, wato fasalinsa a saukake, sigar kayan bugawa mai suna Dongbula kaman wani babban cokali, wato da wani babban katako an haka cikinsa, har ya zama fasalin kayan bugawa mai suna Dongbula.

Mutane na kabilar Hasake suna son wannan kayan bugawa mai suna Dongbula sosai da sosai, a dukkan iyalan kabilar Hasake, dukkan 'yan iyalansu sun iya bugawa tare da yin wake wake har da yin raye raye tare, Kai kullun suna shan nishadi tare da buga wannan kaya mai suna Dongbula, suna zaman jin dadin sosai.

Mutun daya ya iya bugawa kuma mutane da yawa sukan iya bugawa tare. Tare da wannan kayan bugawa mai suna Dongbula ana iya bayyana halayen musamman iri iri.(Dije)

Saurari: Kaunar da Gida

Ruan

Kayan bugawa mai suna Ruan shi ne shahararren kayan bugawa na kasar Sin, A tsohon zamani na da, an taba kiran wannan kayan bugawa mai suna Qin pipa, Wajen a daular Qin na karni 2 ko 3 na bayan bayyanuwar Annabi Isa, mutane sukan yi amfani da wata karamar ganga, a karshe dai an yi gyare gyare ga irin kayan bugawa, wannan shi ne masomin kayan bugawa mai suna Ruan.

A karni na uku na bayyanuwar Annabi Isa, wani mai yin kide kide mai suna Ruan ya yi matukar yin wannan kayan bugawa, sabo da fasaharsa ta yi kwararre sosai, sai ya sami maraba sosai daga dimbin mutanen dake wurin, A kwana a tashi, sai an fara yin amfani da sunasa kaman wannan kayan bugawa haka.

Sigar wannan kayan bugawa mai suna ruan kama kewaye haka, kuma akwai wani dogon hannunsa, wato fasalinsa a saukake ne.

Muryar wannan kayan bugwa tana da karfi sosai kuma mai dadin ji.(Dije)

Saurari: Tuna da Yunlan

Konghou

Kayan bugawa mai suna Konghou wani tsohon kayan bugawa na kasar Sin, tsawon tarihinsa ya yi dadewa sosai da sosai. Bisa abubuwan da aka bincike kan tarihi, an bayyana cewa, tsawon tarihi na wannan kayan bugawa ya kai shekaru fiye da dubu biyu da 'yan kai. A tsohon zamani na da, ban da a fadar sarakuna akan yi amfani da wannan kayan bugawa mai suna konghou, a wurare daban daban na duk kasa mutane sukan yi amfani da shi don nuna wasanni iri iri.

Daga daular Tang ne tare da bunkasuwar tattalin arziki sosai da ci gaban al'adu, kasar Japan ta shiga da wannan kayan bugawa mai suna konghou kuma akwai kasar Korea da sauran kasashen dake makwabtakar da kasar Sin dukkansu sun shigar da wannan kayan bugawa don neman ci gaban al'adunsu.Har zuwa yanzu dai, a cikin wani dakin ibada na kasar Japan, akwai kayan bugawa mai suna konghou guda biyu da ake ajiye a ciki.

Amma daga karshen karni na l4, mutane ba su ci gaba da yin amfani da irin kayan bugawa mai suna konghou ba, har an ce, irin kayan bugawa kusan rasawa. Wato a karshe dai mutane su iya gani irin hoton kayan bugawa mai suna konghou daga bangunan da aka manna.

Amma, daga shekaru 50 na karnin da ya shige, masu yin kide kide na kasar Sin sun yi bincike sosai da sosai kan irin kayan bugawa mai suna konghou. Bisa abubuwan da aka rubuta da hotunan da aka manna kan bango, sun tsara hotunan kayan bugawa mai suna konghou, irin wannan tsohon kayan bugawa mai suna konghou yana kasance da abubuwan rasawa, sabo da haka ne masu yin kide kide sun yi gyare gyare ga irin tsohon kayan bugawa, a karshe dai an fitar da wani irin kayan bugawa mai suna konghou mai kyau sosai.

Yanzu, a wurare daban daban na kasar Sin kungiyoyin makada sukan yi amfani da wannan kayan bugawa mai suna konghou don kara bayyana kyakkyawan halayen yin wasanni iri iri. Mai bugawa mutun daya ya iya bugawa, kuma mutane da yawa su iya bugawa irin kayan bugawa mai suna konghou tare.(Dije)

Saurari: Sarauniyar Xiang

>>[Kayan Gogewa]

Banhu

Kayan gogewa mai suna Banhu, kuma akwai sauran sunaye Banghu da Qinhu, tare da bullowar wasan opera na wurare daban daban ne kuma bisa tushen kayan gogewa mai suna Huqin sai an yi gyare gyare, in an yi kwatanta da kayan gogewa mai suna Banghu da sauran kayayyakin gogewa, muryar wannan kayan gogewa mai suna Banghu ta fi sauran kayayyakin gogewa karfi sosai, Kuma muryar kayan gogewa mai suna Banghu ta fi dadin ji sosai, wato wannan kayan gogewa mai suna Banghu ya iya bayyana farin ciki sosai da bakin ciki sosai.

Tsawon tarihi na wannan kayan gogewa mai suna Banghu sun kai fiye da shekaru 300, kuma sunansa yana canjawa bi da bi.

Da farko dai, mutane na arewacin kasar Sin sun yi amfani da irin kayan gogewa don nuna wasanin opera na wuraensu, wato a lokacin da ake bayyana wasanin opera na wurare daban daban sai an goge wannan kaya don kara dadin ji sosai da kara ba da taimako wajen bayyana wasannin opera iri iri mafi kyau.

Fasalin wannan kayan gogewa mai suna Banghu ya yi daidai kaman kayan gogewa mai suna Erhu.

Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, bisa matukar kokarin da masu yin kide kide da masu kerawa suka yi ne, sai an yi ta daga fasakar kerawa, an dinga samu ci gaba wajen kera irin kayan gogewa, har an sa wadansu sabbin kayayyaki da su kara cikin wannan kayan gogewa.Yanzu, irin kayan gogewa mai suna banghu ya iya bayyana wasan rera wakoki da yin raye raye da kyau sosai.(Dije)

Saurari: Da Qi ban

Ma touqin

Kayan gogewa mai suna Ma touqin shi ne kayan gogewa na kabilar Mongoliya na kasar Sin, domin a kan wannan kayan gogewa mai suna Ma touqin an saka wani doki a kansa sai ana kiran wannan kayan gogewa mai suna Ma touqin.

Tsawon tarihi na wannan kayan gogewa mai suna Ma Tuoqin ya yi dadewa sosai. Kuma a farkon karni na l3 da suka shige ne an fara yin wannan kayan gogewa cikin kabilar Mongoliya, domin a wurare daban daban ne, sabo da haka , sunan wannan kayan gogewa da sigarsa da muryarsa suna da bambanci sosai. Kuma fasahar gogewa na wannan kayan gogewa mai suna Ma Touqin tana da bambanci a tsakanin mutane na wurare daban daban.

Kayan ba da muryar da akan yi kaman wani akwati ne, kuma akwai igiyoyin gashin doki masu tsawon da akan yi amfani da su don yin goge goge.

Tun can farko ne, mutane su kansu su kera irin kayan gogewa mai suna Ma tuoqin,amma muryarsa ba ta da karfi sosai, tare da bunkasuwar sha'anin kide kide na kananan kabilu na kasar Sin, sai kwararru masu gogewa na kabilar Mongoliya sun yi ta yin gyare gyare kan tsohon kayan gogewa, har fasaharsu tana da daguwa sosai. A da in an yi goge wannan kayan gogewa mai suna Ma touqin sai shi kansa wato mutun daya ne akan yi goge goge, amma yanzu tare da kungiyar makada ne ana iya gogewa tare, sai muryarsa tana kara dadin ji sosai.

Yanzu, masu kera irin kayan gogewa mai suna Ma touqin sukan yi sake sake kan wannan kayan gogewa, ga hotuna iri iri kuma masu kyan gani sosai, yawancin mutane na kabilar Mongoliya ta kasar Sin su iya yin goge gogen kayan nan tare da dadin ji sosai.(Dije)

Saurari: Shekaru hudu

Lei qin

Kayan gogewa mai suna Leiqin shi ne sabon kayan gogewa da ya bullo ne a shekaru 20 na karnin da ya shige.

Wannan kayan gogewa da wani shahararren mai gogewa na kasar Sin mai suna Wang Dianyu ya yi gyare gyare kan tsohon kayan gogewa mai suna Zhuihu, a karshe dai ya kago wannan kayan gogewa mai suna Leiqin. Wannan shahararren mai gogewa shi ne makaho, domin iyalinsa mai talauci sosai, tun daga yaronsa ne idanunsa sun gamu da ciwo mai tsanani, a karshe dai bai iya gani kome ba. Ya taba nuna ban girma ga wani farfewa don koyon gogewa na gargajiya ta kasar Sin. Sabo da cikin tsanaki ne ya yi matukar kokarin koyon fasahar gogewa, sai ya iya goge kide kide iri iri na wasan opera na wurare daban daban. Daga karshen shekaru 20 na karnin da ya shige, wannan malam ya yi matukar gyare gyare ga wani tsohon kayan gogewa, ya kara tsawon jarorar gogewa, bayan da ya yi gyare gyare kan tsohon kayan gogewa, sai muryar wannan kayan kogewa ta kara karfi sosai kuma kara dadin ji. A shekara ta l953, da gaske ne an nada irin kayan gogewa da ya yi masa gyare gyare mai suna Leiqin.

Kamar sauran kayayyakin gogewa ne masu gogewa sukan zauna kan kujera, sa'an nan su ajiye kayan gogewa kan kafarsa sai ana yi ta gogewa tare da kide kide iri iri masu dadin ji.(Dije)

Saurari: Wakar A Fanti

Niu tuiqin

Kayan gogewa mai suna Niu tuiqin shi tsohon kayan gogewa na gargajiya ta kasar Sin, wuraren dake kudancin kasar Sin, kaman a lardin Guizhou da lardin Guangxi da wuraren da mutane na kabilar Don ke zaunawa a cunkushe na lardin Hunan, akan yi amfani da irin kayan gogewa don biye da wasanni iri iri, Shin me ya sa ana kitansa kaman kafaffuwan shanu haka? Domin wannan kayan gogewa dogo siriri kaman kafar shannu, ta haka ne ana kiran wannan kayan gogewa mai suna kafaffuwan shanu gogewa. Tare da wani katako mai fadi haka, a bayan rabinsa, an hake babban rami a ciki, sa'an nan an manna wani katako rashin kauri a kansa, kuma yana da dogon wuya, tare da igiyar gora ne akan yi gogewa tare da karfi kuma mai dadin ji sosai. Muryar wannan kayan gogewa mai suna Nuituiqin tana da karfi sosai,kuma sigarsa kaman kayan gogewa da mutane na kasashen yamma sukan kira shi da turanci violin. Kuma muryarsa mai dadin ji kaman na wannan kayan gogewa da mutane na kasashen yamma sukan kiransa da turanci violin.

Yawancin wannan kayan gogewa mai suna Nuituiqin da akan fitar da su daga cikin farar hula na kasar Sin, wato mutane na wurare daban daban na kasar Sin su kansu su iya kera irin wannan kayan gogewa mai suna Nuituiqin, amma kayayyakin da akan kerawa sun sha banban a wurare daban daban. Misali a wuraren da mutane na kabilar Dong ke zaune a cunkushe, sun yi ta yin gyare gyare kan irin kayan gogewa, irin kayan gogewa mai suna nuituiqin bayan da aka yi gyare gyare, sai muryarsa da akan bayyana ta fi karfi sosai, kuma ta iya bayyana halaye iri iri kaman a yi farin ciki da yi bakin ciki da kuma ana jiku sosai kuma da dai sauransu.

A cikin zaman al'adu na mutane na kabilar Dong,wannan kayan gogewa masi suna Nuituiqin ya kama muhimmin wuri, wannan kayan gogewa ya iya bayyana abubuwa da yawa, kaman ana bayyana wata tatsuniyar da ta faru, da irin wakokin da ake rerawa don cika wani makasudi da wani roko da na sauran halaye iri iri. Wato kusan ko wane saurayi na kabilar Dong dukkansu suna da wannan kayan gogewa mai suna Nuituiqin. Wato a cikin zaman yau da kullun ne sukan iya bayyana abubuwan da suke neman fadawa da neman same su. A dukkan bukukuwan aikin gona, ko yanayin hutu, samari maza sukan goge wannan kayan gogewa, suna tafiya suna gogewa, har akan jawo mutane da yawa da su kewayensu don saurari irin kide kide masu dadin ji sosai.(Dije)

Saurari: Kide kide na hasken wata

Gaohu

Wani kayan gogewa mai suna Gaohu, wannan kayan gaohu kaman Erhu da mun taba bayyana muku, yadda ake gogewa kusan daidai. Wato bisa tushen kayan gogewa mai suna Erhu ne ana yin gyare gyare da neman samu kyautatuwa sosai. A wuraren dake kudancin kasar Sin, misali a lardin Guangdong, tun da dadewa ne an fara yin kayan gogewa mai suna Gaohu.Wato wannan kayan gogewa yana hade da kide kide na lardin Guangdong.

Kide kide na lardin Guangdon yana shfe wuraren dake kudancin kasar Sin, wannan ya hada wani wasan opera na wuraren dake kudancin kasar Sin, daga shekaru 20 na karnin da ya shige, wani farfesa na lardin Guangdong ya kago wannan kayan gogewa mai suna Gaohu, wato bayan da ya yi gyare gyare kan kayan gogewa mai suna Erhu sai ya kara samu ci gaba wajen yin amfani da wannan kayan gogewa.

Fasalin wannan kayan gogewa mai suna Gaohu saukake ne sosai, wato dukkan kayayyakinsa kaman na kayan gogewa mai suna Erhu. A wadansu wurare, an kara igiyar gashin wutsiyar dawaki guda daya, wato wannan kayan gogewa mai suna Gaohu yana da igiyoyin gashin wutsiyar dawaki guda uku da akan gogewa. Kuma muryar da akan yi gogewa da kayan Gaohu ta fi na kayan gogewa mai suna Erhu karfi sosai, wannan muryar kayan gogewa mai suna Gaohu ta iya bayyana abubuwa masu karfi kaman bayyana babban karfin da akan nunawa wajen aikin soja da dai sauran irinsu. Kuma shi kansa ya iya bayyanawa a cikin wasanni iri iri da akan nunawa.(Dije)

Saurari: Ruwan sama ya fadi

Erhu

Kayan gogewa mai suna Erhu shi ne shahararren kayan gogewa na gargajiya na kasar Sin, tsawon tarihinsa yana da dogo sosai, har daga zamanin daular Tang ta kasar Sin na karni 7 zuwa karni na l0 bayan bayyanuwar Annabi Isa. A wancan lokaci,ana yin kayan gogewa mai suna Erhu a wurare na kananan kabilu dake wurare arewa maso yammacin kasar Sin. A cikin tsawon lokacin fiye da shekaru 1000 na gudanawar da wannan kayan gogewa, wannan kayan Erhu shi ne muhimmin kayan gogewa dake rakiyar wasan opera iri iri.

Fasalin kayan gogewa mai suna Erhu a saukake ne, wato wani dogon katako kuma mai siriri, ban da haka akwai igiyar wutsiyar dawaki guda biyu, kuma akwai wani abin gogewa mai dogo tare da igiyar gashin wutsiyar dawaki, in mutun yana son gogewa sai ya zauna kan kujera ya dauk abin gogewa, sai ya iya bayyana halayen musamman nasa daga wannan abin gogewa. Fasalinsa a saukake, amma karar da ya bayar tana da dadin ji sasai, wadansu mutane suna siffanta wannan kayan gogewa kaman wani kayan gogewa da Turawa ke kira da turanci" violin" na kasashen yamma. Wannan karar kayan gogewa ta iya bayyana halin bakin ciki da na farin ciki sosai.

Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, wato daga shekara ta l949, a kan kerar kayan gogewa mai suna Erhu an yi gyare gyare sosai, sabo da haka ne daga baya, wannan kayan gogewa ya iya bayyana shi kansa ba tilas tare da sauran kayayyakin kide kide ba.

Sabo da ba wuya da kerar wannan kayan gogewa, kuma muryarsa mai dadin ji, ta haka ne mutanen kasar Sin suna son wannan kayan gogewa sosai, yanzu a wurare daban daban na duk kasar Sin, wato a ko ina ne ana iya ji muryar kayan gogewa mai suna Erhu.(Dije)

Saurari: Tsuntsaye cikin duwatsu

>>[Kayan Busawa]

Xibili

Kayan busawa mai suna Xibili na kabilar Korea na kasarmu, wato dimbin mutane na kabilar Korea na kasar Sin suna son irin kayan busawa. A wurin da 'yan kabilar Korea ke cunkushe a arewancin kasar Sin da sauran wurare na 'yan kabilar Korea ke zaune. Irin muryar da ake busawa daga wannan kaya yana da karfi sosai, kuma irin halin musamman na kabilar Korea ne.

Tsawon tarihi na wannan kayan busawa mai suna Xibili ya yi dogon lokaci sosai, wato sigarsa kaman jagora ba na tsawo ba, a kansa akan haka rumuka guda 7, a bayansa akwai wani rami guda daya, kuma akwai baki da akan hada su guda daya.

Koda yake irin kayan busawa ya iya fitar da murya mai dadin ji, amma in an yi busawa da kyau, ya kamata a yi matukar kokari ga koyon fasahar nan. Wato da wuya ne ake iya busawa da wannan xibili da kyau sosai.(Dije)

Saurari: Kide kide na kauye

Houguan

Houguan wani kayan busawa sunan wani daban shi ne zhuguan, wannan kayan busawa da ya fitowa ne a wuraren daku kudancin kasar Sin, a kan kananan tituna, akwai masu baje koli da suke yin saye saye kayayyakinsu don jawo masu sayawa ne sai suke yi ta bushe wannan kayan Hougun.

Daga shekaru 20 na karnin da ya shige, kungiyoyin makada na lardin Guangdong sun fara yin amfani da irin kayan busawa don kara dadin ji, a karshe dai a duk mafadin lardin Guangdong da lardin Guangxi, in akwai al'amari mai farin ciki da ya auku, ko bukukuwan murnar salla iri iri ne akan busa wannan Houguan don bayyana farin cikin jama'a.

A kan yi amfani da katako don fitar da irin kayan houguan, dogo siriri, a kansa an hake ramuka, kuma a bakinsa akan yi wani karin baki, kuma muryarsa akwai banbanci sosai, wato akwai mai karfi ko marasa karfi.(Dije)

Saurari: Ruwan sama na Bazara

Xiao

Xiao wani kayan busawa ne, sunansa daban shi ne Dongxiao, wannan shi ne kayan busawa na tsohon zamani na da. Tun fil azal ne an fara yin amfani da irin kayan busawa don bayyana farin cikin da jama'a suke bayyanawa sabo da girbi mai armashi. A kan jagora ba na dogo sosai ba, akan haka ramuka layi layi, da yatsa ne aka iya tabe su sai muryar daban daban suke fitowa, kuma an iya bayyana abubuwa daban daban da mutanen suke nunawa.

Amma in a dare, wani yana bushewa irin Xiao, kai muryar da mutane suke ji mai dadi ji kwarai.

A daular Han, an fara fitar da irin kayan busawa, tun fil azal ne mutane na kudancin kasar Sin sun fara busa irin kayan Xiao. Mutanen da sukan busa irin kayan xiao don bayyana hali mai kyau,yawancinsu an yi amfani da su don bayyana ni'imtattun wurare da hali mai kyau na mutane.

Wannan kayan busawa mai suna Xiao kullun mutun daya ya iya busawa da bayyanawa. Yanzu, mutanen dake kudancin kasar Sin kamar na lardin Fujien da lardin Guangdong,ban da haka kuma a cikin wasan opera na wurare daban daban ne akan yi amfani da irin kayan xiao don kara hali mai kyau.(Dije)

Saurari: Tsuntsaye

Guanzi

Guanzi wani kayan busawa ne kuma mai dadin ji sosai, tsawon tarihin wannan kayan busawa mai suna guanzi yana da dogon lokaci. An fara yin amfani da wannan kayan busawa ne daga kasar Iran a tsohon zamani na da.

Kafin shekaru fiye da dubu biyu da 'yan kai da suka shige, wato a daular yammacin Han, an shigo da wannan kayan busawa zuwa jihar Xinjiang ta kasarmu, daga baya, mutane na wuraren dake tsakiyar kasar Sin sun fara yin amfani da kayan busawa mai suna guanzi a cikin kungiyoyin makada, a lokacin da ake murnar girbi mai armashi da yin bikin aure, kuma fasahar busawa tana nan tana kara daguwa. Yanzu mutane na arewancin kasar Sin ma suna son irin kayan busawa, wato a cikin kungiyoyin kide kide, kullun an iya gani irin kayan busawa kuma mai dadin ji sosai.

Muryar wannan kayan busawa tana da karfi sosai, kuma muryar wannan kayan busawa tana da kuruciya, da wannan kayan busawa ana iya bayyana yadda manoma suke yin girbi mai armashi sosai.

Yanzu, a cikin wasannin opera iri iri da aka bayyana, makada sukan yi amfani da irin kayan busawa.(Dije)

Saurari: Bude kofa

Xun

Kayan sarewa mai suna Xun shi ne daya daga cikin kayayyakin sarewa na tsohon zamani na da, kuma tsawon tarihin wannan kayan sarewa mai suna Xun ya kai fiye da shekaru dubu 7. Daga tsohon zamani na da, wato a wancan lokaci, mutanen da ba su iya yin zaman yau da kullun kamar na yanzu haka ba, wato ba su da kayayyakin neman samu abinci kuma ba su iya yin shuke shuke, sai su da hannunsa sukan kama dabbobin daji kawai, a karshe dai sun yi amfani da duwatsu masu kewaye don jefa wa dabbobin daji da kame su don neman samu namansu.Irin wannan kayan sarewa mai kewaye haka, , a karshe dai an haka ramuka a kansa, sai an iya yin bushe bushe masu dadin ji.

Daga baya, sigoggin irin kayan sarewa daban daban ne, amma yawacinsu masu kewaye ne.

A tsohon zamani, a fadar sarkin kasa, in kungiyar makada sun yi kide kide da kyau, a cikin ba shakka akwai irin kayan sarewa mai suna Xun da aka yi amfani da su wajen nuna wasannin opera iri iri.

Daga shekaru 20 zuwa 30 na karnin da ya shige, wani farfesa na kolejin koyon kide kide na kasar Sin ya fara yin wannan kayan sarewa da tangaram, a karshe dai ya sami babban sakamako.(Dije)

Saurari: Wakar Chu

Sheng

Sheng wani kayan sarewa na tsohon zamani na kasar Sin, a cikinsa akwai wani kaya mai taushi sosai, tawon tarihinsa ya fi na sauran kayayyakin sarewa na duk duniya, Kana kuma a tarihi ya taba ba da babban taimako wajen ingiza ci gaban kayayyakin sarewa na kasashen Turai gaba.

A shekara ta l978, daga wani kabarin dake lardin Hubei na tsakiyar kasar Sin, an fitar da irin kayayyakin sarewa, tsawon tarihinsu sun kai shekaru fiye da 3000 da suka shige.

Sabo da tsawon tarihi na irin wannan kayan sarewa ya yi dade sosai, yanzu a wurare daban daban, irin kayayyakin sarewa da aka fitar suna da irin daban daban, wato a kwana a tashi ana dinga canja fasahar kerawar wannan kayan sarewa.

Muryar wannan kayan sarewa mai suna Sheng tana da dadin ji sosai kuma tana da babban karfi. A wadansu lokatai wannan kayan sarewa Sheng shi kansa kadai ana iya sarewa don bayyanuwa, amma a wasu lokatai, ana yin amfani da shi tare da sauran kayayyakin kide kide iri iri don nunawa tare.(Dije)

Saurari: Tsuntsaye mai suna "Feng huang"

Huluxiao

Wani kayan sarewa mai suna Huluxiao wato kwariyar sarewa wannan shi ne daya daga cikin muhimman kayayyakin sarewa na kananan kabilu na kasar Sin,kuma wadansu kananan kabilu kamar su kabilar Dai da kabilar Achang da kabilar Wa dake kudu maso yammacin kasar Sin sun fi so irin kayan sarewa sosai.

Kayan sareawa mai suna Huluxiao yana da tsawon tarihi sosai, wato asalinsa daga daular sarkin Qin, amma har wa yau dai fasalinsa kaman tsohon zamani sosa.

Sigogin Huluxiao suna da iri iri, wato irin Hulu kaman aguna da aka yi shuke shuke, a Afrika ma akwai irin dogo siriri.In sun yi girma har sun nuna, mutanen kasar Nigeria sukan yi amfani da shi wajen debo ruwa ko yin amfani da su a sassa daban daban.

Kamar sauran kayayyakin sarewa suke, muryar kayan sarewa mai suna Huluxiao ba ta da karfi sosai ba, amma muryarsa mai dadin ji sosai.

Sabo da kasancewar bambancin dake tsakanin kabilu da shiyoyyi, ta haka ne irin kayan sarewa na lardin Yunan da na sauran wuraren kananan kabilu, kuma a kan dabarar kera kayan sarewa da dabarar sarewa akwai banbanci sosai. Amma suna da halin mumman daya, wato dukkansu sun dace da sarare wakokin manoma da na kauyuka kuma muryarsu ta iya bayyana burin jama'a sosai.

Amma, masu aikin kide kide na kasar Sin sun kyautata wannan kayan sarewa mai suna Huluxiao, har an kara karfin muryar kayan sarewa. Tare da masu yin kide kide na kasar Sin sun fita don nuna irin wasanni a kasashen waje, sai wannan kayan sarewa mai suna Huluxiao ya hau dakalin fasaha na duniya.(Dije)

Saurari: Wakar hasken rana

Dizi

Kayan busawa mai suna Dizi iri na kasar Sin ya zama wani muhimmin kayan busawa daga cikin kayayyakin bushe bushe da akan yi amfani da su. Dukkan irin kayan busawa da jagora ne aka yi su, wato ana kiransa Zudi.

Mai yin kayan bausawa mai suna Dizi ya cire abubuwan dake cikin jagora, sa'an nan ya hake kananan ramuka kan jagora, wato kaman kide kide da za a busa daga wadannan kananan ramuka ne za a iya ji dadin kide kiden nan.

A dukkan daulolin tarihi, a lokacin da ake yi bukukuwa iri iri, kaman bikin aure da bikin saukar da haihuwa da sarakuna su ha karagar mulki, in akwai makada kuma akwai masu busa irin Dizi, wato wannan kayan busawa iri na gargajiya na kasar Sin.

Kide kide da aka busa daga cikin wannan Dizi suna da dadin ji sosai, kuma masu busawa su iya kwaikwayo muryar tsuntsaye iri iri.

A da, mutanen da suka fi son yin bushe bushe da wannan kayan dizi na kudancin kasar Sin ne, daga baya mutane na arewancin kasar Sin su ma suna son wannan kayan busawa.(Dije)

Saurari: Tafiya a Gusu

>>[Karamin Kayan Bugawa]

Yangqin

Kayan bugawa mai suna Yangqin, wannan kayan bugawa da mutanen kasar Sin sukan yi amfani da shi cikin kungiyar masu buge buge. Muryar wannan Yangqin da aka buga tana da dadin ji, wato muryarsa ta iya bayyana ma'ana iri iri, Kana kuma mai bugawa guda daya ko masu bugawa da yawa su yi bugawa wannan kayan yangqin tare, kuma cikin kungiyoyin masu bugawa ya dau muhimmin matsayi wajen fitar da muryar kide kide masu dadin ji.

Da katako ne akan yi wannan kayan bugawa mai suna Yangqin. An ce a cikin tsohon zamani na da, a kasashe Larabawa, akan yi amfani da wani irin kayan bugawa kaman irin kayan bugawa mai suna Yangqin na kasar Sin, daga baya a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, an fara yin amfani da irin kayan bugawa mai suna yangqin, wannan kayan bugawa ya iya bayyana ma'anar abubuwa da yawa, kaman mutane sun yi farin ciki sosai, sai mai bugawa sun yi saurin buga yangqin, sai ana ji dadi sosai.

An, irin kayan bugawa mai suna yangqin yana da tsawon tarihi na shekaru fiye da dari hudu. A cikin wannan tsawon lokaci, masu bugawa na kasar Sin sun yi ta kyautata wannan yangqin, yanzu a lokacin da ake bugawa sai an yi amfani da lantarki mai karfi sosai.

Bayan da masu bugawa na wannan yangqin sun yi matukar kokari cikin shekara da shekaru, sai fasahar kera wannan kayan bugawa ta dagu sosai, kuma fasahar bugawa ita ma ta dagu sosai, yanzu dukkan mutane suna son ji muryar kayan bugawa mai suna yangqin.(Dije)

Saurari: Bazara ta shiga kogin Qing

>>[Kayan Busawa na Baki]

Kouxian

Wani karamin kayan busawa sunansa Kouxian, wannan kouxian ya fi karami sosai a cikin dukkan kayayyakin busawa na gargajiya ta kasar Sin, wato wannan kouxian kayan busawa na kananan kabilu na kasar Sin,An ce, tun daga tsohon zamani wato daga karni na 40 na kafin hijira, mutane sun fara yin amfani da wannan kayan busawa don neman dadin ji sosai.

Irin kayan busawa da aka kera da jagora, wani irin jagora mai karfi sosai, da farko an sa wuka don yanyyanke irin jagora, daga cikin kayan busawa, an ajiye wani abu layi layi kanana siriri sosai a ciki.

Akwai mutane da yawa sukan kera irin kayan busawa da karfe, ko da tagula da kanannadadden karfe, irin kayan busawa da aka kera sun fi dadin ji sosai.

A lokacin da masu busa irin kaya, sai an sa yatsa iri iri tare da busawa da iskar da masu busawa suke fita daga baki.(Dije)

Saurari: Kide kide na Lei bo

>>[Kayan Bugawa]

Qing

Qing wani karamin abun bugawa don neman dadin ji, wannan kayan qing abin bugawa na tsohon zamani kuma na kananan kabilu na kasar Sin, fasalinsa mai kyaun gani sosai.A tsohon zamani na da, mutane ba su iya gina gidaje ba, a wurin waje ne suka yi zaman rayuwarsu, sabo da haka ne ba su yi shuke shuke da kula da gonaki ba, sai sun yi farauta wato sukan yi kame kame ga dabobin daji kawai, bayan aikinsu sai sun yi hutu da sa fatan dabobi iri iri don yin raye raye da kuma buga duwatsu, sannu a hankali, daga baya ne aka fara yin amfani da irin dutse don bugawa da neman dadin ji sosai.

A lokacin da ake yin raye raye ne akan yi tare da bugawa wannan qing don kara dadi ji ga masu yin raye raye, daga baya an fara yin amfani da wannan kayan bugawa don yi bikin jana'izza da yin bikin aure da sauran shagulgula.

A watan augusta na shekata l983, daga karkashin kasa na gundumar Sui ta lardin Hubei dake kudancin kasar Sin, an gano da wani kayan bugawa mai suna Qing daga wani kabari na tsohon babban jami'I na daular Chu,a cikin wannan hakawa, ban da kayan bugawa qing kuma akwai sauran kayayyakin bugawa masu daraja sosai. Amma abin nadama shi ne a lokacin da aka gano wadannan kayayyakin bugawa dukkansu sun katse har ba a iya bugawa da kyau sosai ba, A shekara ta l980, cikin gama guiwa ne sassa daban daban da abin ya shafe sun yi matukar kokari don kwaikwayo da kera sabbin irin kayayyakin bugawa, kai kaman gaskiya ne a lokacin da ake bugawa ga muryar nan mai dadin ji kwarai.(Dije)

Saurari: Kide kide na Zhu Zhi

Bianzhong

Bianzhong wani kayan bugawa ne kararsa mai dadin ji sosai. In an yi buge buge irin kayan bugawa, ya kamata a rataya kayayyakin bugawa layi layi a kan babban katako, domin tsawon lokacin tarihi ya sha banban, sai sigoginsu suna da banbanci sosai, kuma a kan bangon kayan bugawa, an zana hotuna iri iri masu kyan gani.

Kafin shekara ta 3500 na daular Shang, kasar Sin tana fara yin amfani da wannan kayan bugawa mai suna bianzhong, a da kayayyakin bugawa guda uku uku da aka rarraba kananan kungiyoyi, daga baya kayayyakin bugawa suna nan suna kara yawansu. A daulolin da suka shige, an yi amfani da wannan bianzhong don yi bukukuwa iri iri a cikin fadar sarki, in rundunar soja ta kasa za ta tashi don yin gaba da makiyi, sai an yi buge buge ga wannan bianzhong don sa kaimi ga sojojin da za su tashi.

A tsohuwar kasar Sin, sai a fadar sarakuna ne akan yi amfani da wannan bianzhong don nuna fiffiko ga masu mulkin kasa. A zamani na yau, a wurare da yawa an gano irin kayan bugawa, misali a lardin Yunnan da lardin Shanxi da lardin Hubei da sauran wurare, wato daga kabari na masu babban mulki ne aka fitar da irin kayayyakin bugawa masu dadin ji. Irin kayan bugawa da ake buge shi, kararsa kaman muryar da mawaki suke rerawa.

A shekara ta l982, ma'akatar yin kayayyakin bugawa na birnin Wuhan na lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin ta yi bincike sosai har ta fitar da wadansu kayayyakin bugawa mai suna Bianzhong, Bayan da 'yan kimiyya suka dudduba tare da wani inji na zamani, an ce fasaharsa da ingancinsa sun kai matsayi na zamani sosai.(Dije)

Saurari: Tuna da Qu Yuan

Luo

Kayan Luo shi ne wani kayan bugawa na gargajiya ta kasar Sin, a cikin kayayyakin bugawa na kabilun kasar Sin, kayan luo ya kama wani muhimmin matsayi, kana kuma a duk mafadin kasa ne ana yin amfani da wannan kaya, wato kungiyoyin gargajiya na kasar Sin dukkansu ba su rasa irin kayan bugawa ba in an yi bukukuwa iri iri, kuma a cikin wasanni na wurare daban daban da yin raye raye da wake wake ko yin murar girbi mai armashi da yin gasar aikin gona, wato a dukkan wuraren yin shagulgula, ka iya gani irin kayan bugawa wato kayan luo da aka buge buge mai dadin ji sosai.

Irin kayan bugawa na garganiya ta kasar Sin da kayayyaki iri iri ne akan iya kera da su, misali da karfe, in da karfe an kera wannan kayan bugawa wato luo, muryarsa ya iya baza zuwa nesa kwarai, wato daga nesa ne akan iya ji karar kayan luo da ake bugewa. Kuma akwai kayan katako da aka kera wannan wannan kayan bugawa, amma irin karar da aka buga ba za ta iya zuwa nesa sosai ba. Wannan kayan bugawa mai suna luo mai fadi kewaye ne.

Tun da wuri ne a wuraren kananan kabilu dake kudu maso yammacin kasar Sin, mutane sun fara yin amfani da wannan kayan bugawa don yin shagulgula iri iri. Tare da musaye musaye tsakanin kabilu daban daban ne sai mutane na tsakiya kasar Sin sun fara yin amfani da wannan kayan bugawa, a wancan lokaci, a cikin yake yaken da aka yi akan yi amfani da wannan kayan bugawa don kara kuruciya ga rundunar sojan dake fadawa.

A cikin kayayyakin bugawa, luo ya kan iya ba da jagora ga sauran masu bugawa, a kai a kai ne masu bugawa sun yi bugawa tare.

Yanzu, a cikin wasanni iri na kudu da na arewa, akan yi amfani da wannan kayan bugawa don yi bikin budewar wasa, misali a cikin wasan opera na Beijing, akan yi amfani da wannan kayan bugawa luo don kara dadin ji sosai.(Dije)

Saurari: Kama kifi

Gu

Kayan bugawa mai suna Gu, wato ganga ne, a kasar Sin akan yi amfani da irin kayan bugawa, wato tun tuni ne mutane na kasar Sin suka fara yin amfani da wannan kayan bugawa. Daga kayayyakin bugawa da aka hako daga karkashin kasa,an iya nuna tabbaci cewa, tsawon tarihin wannan kayan bugawa ya kai shekaru kusan 3000 a tarihi. A tsohon zamani na da, kayan bugawa mai suna Gu ba ma kawai akan yi amfani da shi wajen bukukuwan burna iri iri, kana kuma a cikin yaken yaken da aka yi, akan buga kayan ganga don kai farmaki ga makiyi da kai bugu ga dabobin daji da kuma nuna gargadi ga mutane .

Tare da ci gaban zaman al'umma, ana nan ana kara yin amfani da gu a kan sassa daban daban, a cikin kungiyoyin gargajiya ta wasanni iri iri kamar wasan opera na Beijing da opera na wuraren daban daban na duk kasar Sin, in ana wake wake da raye raye sai akan buga wannan ganga don kara dadin ji sosai. Tare da fatan dabobin daji iri iri ne akan yi wannan kayan ganga, fadin kewayensa mai kyaun gani. Kuma surarsu akwai iri iri, akwai babba kuma akwai karami karami kadan kadan.Kuma sigogginsu ire ire ne, yawancinsu da akan yi amfani da su cikin kungiyoyin raye raye, domin in an yi raye raye tare da buga wannan kayan ganga sai ana jin dadin da yin raye rayensu.(Dije)

Saurari: Damisa

© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China