>
Babi08: Aikin Ba Da Ilmi
■ Aikin Ba Da Ilmi

>>[Me ka sani]

Ana yin aikin ba da ilmi bisa babban mataki mafi girama a duniya

Kasar Sin kasa ce mai yawan mutne sosai, kuma masu koyon ilmi suna da yawa sosai. Yanzu kasar Sin tana nan tana tafiyar da aikin ba da ilmi bisa babban mataki mafi girma a duk duniya,Yanzu, jimlar mutanen dake cikin makarantu daban daban da jami'o'I daban daban don koyon ilmi na duk kasar Sin ta kai fiye da miliyan 200.

Ayukan ba da ilmi na kasar Sin suna hade da gidan reron yara, da makarantun firamare da makarantun sakantare da jami'o'I da kolejoji. Bisa aljihun Gwamnati ne Daliban da suke koyo daga makarantun firamare zuwa makarantun sakantare har cikin shekaru 9 a fayu. Wsdannan dalibai ba za su biya kudin koyo ba, amma a kowace shekara za su biya kudin litattafai da sauran kudi kadan.

Gwamnatin kasar Sin ta sa muhimmanci sosai ga aikin ba da ilmi a fayu, Bayan da aka yi kokari cikin shekaru gomai wajen aiwatar da aikin ba da ilmi a fayu, yawan daliban da suka more koyon ilmi a fayu sun karu daga kashi kusan 80 zuwa kashi fiye da 90 cikin dari. A cikin 'yan shekaru masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta sa muhimmanci ga aikin ba da ilmi a fayu a kauyuka da aikin ba da ilmi a jami'o'I, kuma gwamantin kasar Sin tana fatan dukkan yaran da su shiga makaranta, kuma cikin sauri ne a kasar Sin za a kafa jami'o'I n kasar Sin na matsayin gaba na duk duniya.

Ayyukan ba da ilmi na kasar Sin yawancinsu gwamnati ce tana tafiyar da su. Amma cikin 'yan shekaru da suka shige, mutane masu zaman kansu suna tafiyar da aikin ba da ilmi suna nan suna kara karuwa,Amma daga yawancin ayyukansu ba su kai matsayi na gwamantin ba tukuna.

>>[Tsarin ba da ilmi]

An yi tarbiyya ga yaran da shekarunsu ba su kai 6 da haihuwa ba

A kasar Sin, an yi tarbiyya ga yara ta hanyar gidan renon yara ko yin tarbiyya ga yaran da shekarunsu ba su kai 6 da haihuwa ba. Bisa karfin girman yara da halin musamman na tunaninsu, ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ta tsaida manyan ka'idojin ba da ilmi ga yaran da shekarunsa ba su kai 6 da haihuwa ba. Kana kuma hukumomin ba da ilmi ga yara daban daban sun horar da yara a kan sassan halayen musamman na yara, misali jin kai da yare da adadi da halin zaman rayuwarsu don ba da musu ilmi daban daban da horar da su kan zaman rayuwarsu

A kasar Sin, gidajen renon yara sukan karbi yaran da shekarunsu sun kai 3 zuwa 6 da haihuwa, Ban da haka kuma wadansu gidajen renon yara sukan iya karbar jarirai. Yanzu, jimlar gidajen renon yara na kasar Sin ta kai wajen dubu l50, kuma yawan yaran da gidajen renon yara suka karba sun kashi fiye da 30 cikin dari bisa na jimlar yara na duk kasar Sin, sabo da an kasance da dalilai iri iri, misalin shekarun yara da tsimin kudi da sauransu, sai iyayen yara suke kula da yaransu a gidajensu kawai.

Bisa hanyoyi biyu ne aka kafa gidajen renon yara, wato hanya daya ita ce gwamanati ta kafa gidajen renon yara, wata daban ita ce mutane masu zaman kansu su gina gidajen renon yara. Gidajen renon yara da gwamnati ta kafa har cikin dogon lokaci ne kuma suna da fasahohi da yara wajen horar da yara, kuma kudin da za a kashe ba da yawa ba, Amma gidajen renon yara da mutane masu zaman kansu suka kafa akwai halayen musamman nasu kuma kudin da za a kashe ya yi yawa sosai. Bisa bukatun kasuwoyi ne za a iya yin gyare gyare cikin daidai lokaci. Tare da bunkasuwar kasuwanni ne gidajen da mutane masu zaman kansu suka kafa suna nan suna kara yawansu, Yanzu, jimlar gidajen renon yara da mutane masu zaman kansu suka kafa ta kai wajen kashi uku cikin dari.

Aikin ba da ilmi na makarantar firmare

Aikin ba da ilmi ga yaran da shekarunsu sun kai 6 da haihuwa a makarantar firamare, Bisa dokokin shari'a na ba da ilmi a fayu na kasar Sin, gwamnati take tafiyar da aikin ba da ilmi ga yara a fayu, wato yaran da ke makarantar firamre ba su biya kudin koyo, amma ya kamata su biya kudin litattafai da sauransu kadan, Yawan kudin da kowane dalibi yakan biya ya kai kudin Sin Yuen daruruka.

Yawancin tsawon lokacin tsarin koyo na makarantar firamare na kasar Sin ya kai shekaru 6, Muhimman darussan da akan koyar da su suna hade sinanci,ilmin lisafi da kimiyya da yaren waje da tunanin nagari da kide kide da wasan motsa jiki da sauransu. Bisa sabon lisafin da aka yi an ce, jimlar makarantun firamare na kasar Sin ta kai fiye da dubu dari 4, Kuma jimlar daliban dake makarantun firamare ta kai miliyan l20, Yawan daliban da shekarunsu sun kai shiga makaranta da haihuwa ya kai kashi fiye da 98 cikin dari bisa na jimlar yaran da shekarunsu sun kai shiga makaranta da haihuwa na duk kasar Sin.

A matakin ba da ilmi a fayu, yawancin makarantun firmare da gwamnatin kasa ta kafa, bisa wuraren dake kusa da makarantun firamare ne yara su iya shiga makarantun dake kusa da gidajensu.

Yanzu, sassan kula da aikin ba da ilmi na kasar Sin suna nan suna kokari kyautata sharudan koyarwa, ta yadda 'yan makaranta za su iya samu damar koyo a fyu kuma cikin adalci; Bugu da kari kuma, a wuraren da manoma ke cunkushe na kauyuka, an tattara yara da su shiga wata cibiyar makaranta mai cikakkun kayayyaki don yin koyo da zaune a wannan makaranta.

Yin tarbiyya a makarantun sakantare

Aikin ba da ilmi a makarantar ilmi na kasar Sin a fayu, amma ana bukatar biyan kudin litaffi da sauran kudi kadan, wato yawan kudin da akan biya sun kai kudin Sin Yuan wajen daruruka kawai a kowace shekara.

Yawancin tsawon tsarin koyo na makarantar mikil na kasar Sin ya kai shekaru uku, Muhimman darussa da akan koyar da su suna hade da sinanci, ilmin lisafi da yaren waje da ilmin physics da ilmin chemistry, da tunani nagari da aikin ba da labaru. Bisa sabon lisafin da aka yi an ce, yanzu yawan makarantun mikil na kasar Sin sun kai fiye da dubu 60, kuma jimlar daliban dake makarantun mikil ta kai miliyan 60, kuma yawan daliban da shekarunsu sun kai shiga makarantun midil da haihuwa da su shiga makarantun mikil sun kai fiye da kashi 90 cikin dari, yawancin makarantun mikil na kasar Sin da gwamnati ce ta kafa kuma take aiwartar da su.

Sabo da yin koyo a makarantun midil a fayu ne ta haka bayan da daliban da suka gama koyonsu daga makarantun firamare kafin su shiga makarantun mikil ba a bukatan ci jarabawa don shiga makarantun mikil, wato sassan kula da aikin ba da ilmi sun tsaida makarantun mikil da daliban da suka gama koyonsu daga makarantun firamare bisa wuraren da daliban ke zaune da burinsu; bugu da kari kuma, a kauyuka, an tattara dalibai daga wurare daban daban don shiga wata makaranta mai cikakkun kayayyakin ba da ilmi, wato daliban makarantun midil na kauyuka suna koyo da zaune a makarantun midil. Yanzu kasar Sin tana nan tana yin kokarin ingiza aikin ba da labarun ilmi., a sanya babban karfin wajen bunkasa aikin koyarwa daga nesa don neman bunkasuwar aikin ba da ilmi tare.

Aikin ba da ilmi a manyan makarantu

Aikin ba da ilmi na manyan makarantu na kasar Sin shi ne bayan da daliban da suka gama koyonsu sai su shiga manyan makaranru, Wannan yana hade da manyan makarantu na kullun da manyan makarantu na sana'o'in musamman. Kuma Aikin ba da ilmi na manyan makarantu ba fayu ba, Wato in an shiga manyan makarantu ya kamata a biya kudin shiga. Bisa halayen tattalin arziki na wurare daban daban ne, jimlar kudin da kowanen dalibi na yawancin wurare sukan biya ta kai kudin Sin yuan dubbai.

Yawancin tsawon lokaci na tsarin karatu na manyan makarantu na kasar Sin ya kai shekaru 3, muhimman abubuwan koyo suna hade da Sinanci da ilmin matshomatics da ilmin chemestry da ilmin biology da ilmin ba da labaru. Bisa aljihun Gwamnatin kasa ne an kafa yawancin manyan makarantu, Saboda aikin ba da ilmi na manyan makarantu ba fayu ba, sai cikin 'yan shekarun da suka shige, mutane masu zaman kansu sun kafa wasu manyan makarantu masu inganci sosai.

A kasar Sin, bayan da dalibai suka gama koyonsu a makarantu ya kamata za su ci jarabawa don kara neman koyo a manyan makarantu, kuma bisa burin dalibai da sakamakon jarabawarsu ne za a zabi nagartattun dalibai don shiga manyan makarantu. An tsaida abubuwan da za a ci jarabawa bisa hadadden sashen kula da aikin ba da ilmi na wurare daban daban na duk kasa, Kana kuma cikin gama guiwa ne an tsaida yawan makin da za a samu. Bisa kididdigar da aka yi ba da dadewa ba, an ce, yanzu yawan manyan makarantu na kasar Sin sun kai fiye da dubu 30, kuma jimlar daliban dake cikin manyan makarantu sun kai miliyan 30, kuma yawan daliban dake cikin manyan makarantu sun kai miliyan 30, Kuma yawan daliban dake cikin manyan makarantu sun kai kashi fiye da 40 cikin dari bisa na duk samari masu shekarun da haihuwa daidai haka. Cikin 'yan shekaru biyu da suka shige, sassan ba da ilmi na kasar Sin suna nan suna sanya kokarin neman bunkasa aikin ba da ilmi na manyan makarantu, don biyan bukatu na dimbin dalibai masu neman samu ilmi.

Aikin ba da ilmi na jami'a

Ayyukan ba da ilmi na jami'o'I na kasar Sin suna hade kolejoji da neman samu digiri na farko da na neman samu digiri na biyu da na neman samu matsayin docter. Jami'o'I na kullun da jami'o'in koyon sana'o'in musamman da na ba da ilmi ta rediyo da ba da ilmi ta tashar T.V, kuma akwai jami'o'I na baligai da sauran ire irensu.

Tsawon tarihin aikin ba da ilmi na jami'a na kasar Sin sun kai fiye da shekaru l00. Bisa kididdigar da aka yi ba da dadewa ba, an ce,yanzu jimlar yawan jami'o'I na kasar Sin sun kai fiye da 3000, daga cikinsu akwai kashi biyu cikin kashi uku da gwamnatin kasa ta kafa, kuma kashi daya cikin kashi uku da masu zaman kansu suka kafa. Ban da haka kuma jimlar daliban dake jami'o'I sun kai miliyan 20, wato yawan daliban dake cikin jami'o'I sun kai kashi fiye da l7 cikin dari bisa na jimlar samari masu shekaru da haihuwa daidai da irinsu na duk kasar Sin.

A kasar Sin, in an shiga jami'o'I, sai ya kamata a ci jarabawar shigawa, bisa buri na dalibai da na sakamakon da suka samu an zabi nagartattu don shigar da su cikin jami'o'i. Ma'aikatar kula da aikin ba da ilmi ta kasar Sin da ta larduna daban daban sun tsaida abubuwn jarabawa tare, Kana kuma cikin hadin guiwa ne an tsaida yawan maki na shigowa.

Bisa aljihun gwamnati ne kasar Sin tana tafiyar da jami'o'I, wato shahararrun jami'o'I na kasar Sin dukkansu da gwamnatin kasa ta kafa, kuma bayan da aka ci hasara wajen ci jarabawa, sai an zabi jami'o'in da masu zaman kansu suka kafa ko neman ilmi ta hanyar saurara darashi daga rediyo ko rediyo mai hoto da kuma shiga jami'o'I na baligai.

A cikin 'yan shekaru biyu da suka shige,sassan kula da aikin ba da ilmi na kasar Sin suna kokarin kara habaka jami'o'I, kuma bisa babban mataki ne a kara jawo daliban da su shiga jami'o'I, kana kuma an kara jawo dalibai masu neman digiri na biyu da su shiga jami'o'i.

Aikin ba da ilmi na waje da makaranta

Ban da aikin ba da ilmi a makarantu da yawa, kasar Sin tana da hukumomin ba da ilmi masu yawa sosai na waje da makarantu, Har kullun ne mutanen kasar Sin sun nuna himma sosai ga aikin ba da ilmi, kana kuma suna sa himma wajen neman burinsu na kara ilmi a hukumomin waje da makarantu.

Wadannan hukumomin ba da ilmi na waje da makarantu suna hade da dakunan kara ilmi iri iri ga yara manyan gobe da cibiyoyin koyo da kos iri iri na horar da yara da samari da yin tarbiyya a hanyar internet. Samari da yara manyan gobe sukan koyi ilmin kide kide da wasan raye raye da yin zane da kara ilmin iri iri da wasan fasaha don kara ilmi da raya zaman al'umma masu dadin ji.

>>[Tsarin Jarabawa]

Ci jarabawa don neman shiga manyan makarantu

A kasar Sin, in an nemi shiga babbar makaranta daga karamar makarantar sakandare sai a ci jarabawa, irin jarabawar da aka ci ita ce jarabawar karamar makarantar sakandare. Sabo da yawan dalibai na kananan makarantu sakandare da za su shiga manyan makarantun sakandare sun kai kusan kashi 60 cikin dari, har irin yawansu ya yi kasa da na neman shiga jami'o'I, ta haka ne an mai da irin jarabawa kamar wata babbar wahalar jarabawa da za a ci.

Cikn gama guiwa ne sassan ba da ilmi masu kula da irin jarabawa na wurare daban daban sukan tsaida abubuwan jarabawa. Sassan ci jarabawa suna hade da Sinanci, harsunan waje da ilmin mathomatics da ilmin phisics da ilmin chemestry da dai sauransu. Kuma an tsaida cewa, a watan Yuni na kowace shekara, akan shirya wannan jarabawa.

In daliban da suka ci nasara cikin jarabawar nan za su iya shiga manyan makarantun sakandare, Sa'an nan za a iya neman shiga jami'o'I, A karshe dai za a iya samu aiki mai makoma. In ba a samu nasara cikin irin jarabawa ba, to za a yi gaban ayyuka maras al'adu sosai, wato maras kyau. Sabo da haka ne mutane da yawa na kasar Sin sun mai da muhimmanci sosai ga irin jarabawa.

Ci jarabawa don neman shiga jami'a

Ci jarabawa don neman shiga jami'a wannan ita ce jarabawar shiga jami'a. Bisa jarorancin abubuwan da ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ta tsara, kuma cikin hadin guiwa ne sashen kula da aikin ba da ilmi na gwamnati da na larduna daban daban sun tsaida abubuwan jarabawa. Daga ran 7 ga watan Yuni na kowace shekara akan fara ci jarabawar neman shiga jami'a, wato tsawon lokacin ci jarabawa kwanaki 2 zuwa 3

Yanzu, an kiran abubuwan ci jarabawa na kasar Sin "3+x", ma'anar 3 ita ce Sinanci da phisics da harsunan waje, ma'anar X ita ce sassan ilmi daban daban, wadanda dalibai masu ci jarabawa za su iya zaba daga cikinsu, A wadansu wurare wannan X tana wakilci sashen fasaha ko sashen kimiyya. In an nemi ci jarabawar sashen kimiyya, ya kamata za a ci jarabawa a kan sassan phisics da chemestry da biology da tarihi da dai sauransu.

Har kullun ne zaman al'umma na kasar Sin yakan nuna ban kula ga ci jarabawar neman shiga jami'a, Amma cikin 'yan shekaru da suka shige, an kara habaka daliban dake cikin jami'a da kara yawan shigar da dalibai cikin jami'o'I, sai karfin matsin dake kan wuyan iyayen dalibai ya ragu kadan. Ko da yake an yi haka, in lokacin cin jarabawar neman shiga jami'a ya zo, sai ya jawo hankulan mutane na sassa daban daban na kasar Sin sosai.

Ci jarabawar shiga jami'ar neman digiri na biyu

Ci jarabawar neman damar samu digiri na biyu ita ce yadda jami'o'I daban daban da hukumomin karbar dalibai masu neman digiri na biyu. Irin jarabawa yana hade da matakai guda biyu, wato na neman digiri na biyu da na neman matsayin doctor.

Ci jarabawar neman matsayin koyon digiri na biyu na kasar Sin yana hade da sassa biyu, wato a rubuce da ba da amsa ta baki kai tsaye, Sassan ba da ilmi na gwamnati ne akan tsaida abubuwan ci jarabawar nan, an kuma tsaida yawan makin da za a iya samu shigawa. Misali, in dalibai za su shiga sashen fasaha, ya kamata za su ci jarabawar siyasa da yaren waje, in dalibai za su shiga sashen kimiyya, Ya kamata za su ci jarabawar siyasa da yaren waje da mathomatics da sauran sana'o'In musamman. In masu ci jarabawa za su kai wani matsayin nasara, ya kamata za su ci jarabawar ba da amsa ta baki kai tsaye, bisa sakamakon da dalibai suka samu ne jami'o'I da hukumomin bincike za su shigar da nagartattun dalibai wadanda za su yi neman samun digiri na biyu.

Jami'o'I daban daban da hukumomin bincike su kansu suna da ikon tsaida abubuwan ci jarabawa don shigar da dalibai masu neman samu matsayin doctor. In dalibai masu digiri na farko kawai, ya kamata za su ci jarabawar yaren waje da sauraun sassan ili biyu ko uku wajen rubuce da ba da amsa ta baki kai tsaye.

Ci jarabawa don neman samu takarar shaida

Ban da a ci jarabawa don neman samu matsayin ilmi daban daban, Sa'an nan a kan sassa daban daban a shirya jarabawa daban daban don neman samu takardun shaida iri iri. Ana gani cewa, wadansu jarabawar da aka ci za su ba da taimako ga masu nemn smu aiki yi, Wato wadannan takardun shaida da aka samu bayan da aka ci jarbawa za su iya kara karfin iyawarsu.

Yanzu, muhimman takardun shaida da mutanen kasar Sin suke fi nemawa suna hade da sassan yaren kasashen waje da na ilmin lisafi da na kide kide da na raye raye. Ban da haka kuma akwai takardun shaida sana'o'I iri iri, kamar lauya da kawu wato mai yin lisafi da sauransu. Tare da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin tana shafi duniya, wadansu jarbawar neman sana'o'in duniya suna shiga kasuwannin kasar Sin.

Jarabawar neman takardun shaida na kasar Sin tana hade da matakai daban daban, don bayyana masu irin takardu na matakai daban daban.Sabo da haka ne ba ci jarabawa sau daya da za a iya samu takardar shaida b, ya kamata masu ci jarbaw su dinga koyo kuma su dinga ci jarabawa da kara yin koko har zuwa manyan jami'o'I za su ci gaba da koyonsu.

>>[Shahararren Jam'o'in Kasar Sin]

Takaitaccen bayani na game da jami'o'i na kasar Sin

Cikin 'yan shekarun da suka shige,bisa babban mataki ne kasar Sin ta kara habaka yawan daliban da suka shiga jami'o'I na gwamnati, Yanzu, yawan daliban dake cikin jami'o'I na gwamnatin kasar Sin sun ninka da yawa bisa na shekara ta l998, Wato yawan daliban nan sun kai miliyan 20, Kana kuma yawan daliban da suka shiga jami'o'I na kasar Sin sun karu daga kashi l0 zuwa kashi l7 cikin dari.

Yanzu, yawan jami'o'I na kasar Sin sun kai fiye da 3000, daga cikinsu yawan jami'o'I na gwamnati sun kai fiye da l300, kuma l200 ba na gwamnati ba, sauransu na baligai ne. Ayyukan ba da ilmi na jami'o'I suna hadawa da sassan musamman, digiri na farko da digiri na biyu da matsayin docter da sauransu.

Yanzu, jami'o'I na kasar Sin suna daukar dabarun neman maki cikin jarabawa, tsawon koyo na tsarin sassan musamman ya kai shekaru uku, digiri na farko tsawonsa shekaruya kai hudu, tsawon neman karin ilmi na digiri na farko da na docter sun kai shekaru 2 zuwa 3.

Jami'o'In gwamnati na kasar Sin suna kama muhimmin matsayi na cikin aikin ba da ilmi. Cikin 'yan shekaru da suka shige, yawan jami'o'In da ba na gwamnati ba sun karu karuwa da sauri, kana kuma bisa babban mataki ne, amma an kasance da rata sosai tsakanin jami'o'I na gwamnati da ba na gwamnati ba wajen ba da ilmi da matsayin ilmin malamansu.

Jami'ar Beijing

Jami'ar Beijing Jami'a ce mai cikakkun sassan koyon ilmi daban daban masu fasaha da na kimiyya, wadda tana da babban matsayin bincike ilmi sosai, wato tana shahara sosai a duk mafarin kasar Sin. A shekara ta l989 an kafa wannan jami'a, wato ita ce daya daga cikin manyan jami'a masu tsawon tarihi sosai na duk kasar Sin.

Bayan da wannan Jami'a ta sami bunkasuwa cikin shekaru dari da suka shige,yanzu, Jami'ar Beijing tana da sassan daban daban kamar na ilmin fasahohi da na zaman al'umma da na kimiyya da na aikin ba da labaru da sadarwa da na likitanci, Kuma tana da kolejoji 42, kuma cibiyoyin bincike nata sun kai 216, kuma tana da asibitoci masu koyarwa guda l8, daga cikinsu wadansu sassan koyo kaman na Sinansi da na Spain da na tarihi da na sauran ilmi suna shahara a duk kasar Sin.

Yanzu Jami'ar Beijing tana da dalibai masu neman digiri na farko guda fiye da dubu l5, yawan dalibai masu neman digiri na biyu da na matsayin docter sun kai dubu 12, Ban da haka kuma akwai dalibai da yawa na kasashen waje dake dalibta a wannan jami'a. Jami'ar nan tana da babban dakin karatu wanda ya fi girma a duk kasashen Asiya, Jimlar litattafan dake cikin wannan dakin karatu ta kai fiye da miliyan 6.29. In ka so kara neman sanin abubuwa na wannan jami'a sai ka shiga hanyar internet haka:

http://www.pku.edu.cn/

Jami'ar Tinghua

Jami'ar Tsing Huatana cikin birnin Beijing hedkwatar kasar Sin, wadda ta yi shahara sosai wajen bincike ilmin kimiyya kuma tana da cikakkun sassa daban daban, Kuma tsawon tarihi nata yana da shekaru kusan dari, Wato ita daya daga cikin muhimman wuraren dake horar da masu zurfin ilmi a kasar Sin.

Yanzu,Jami'ar Tsing Hua tana da kolejojin koyon kimiyya da gine gine da na madatsar ruwa da na kera injuna da aikin ba da labaru da na tattalin arzik da na dokokin shari'a da na yin zane zane, wato jimalar kolejojinta sun kai ll, wadansu sassansu na ilmin gine gine da na injunan kwakwalwa da na kera motoci dukkansu suna da kwarjini sosai a duk kasar Sin. Cikin 'yan shekaru kusan 20 da suka shige, jami'ar Tsing Hua a tana nan tana kara samu bunkasuwa wajen sassa daban daban, Ita kuma ta kara yawan sassanta na aikin kulawa da na Sinanci da na watsa labaru da na sauran sassan fasaha,Yanzu wannan Jami'a tana nan tana yin gine gine na asibiti.

Yanzu, jami'ar Tsing Hua tana da malamn koyarwa da masu aiki wajen dubu 7 da dari daya, jimlar dalibai sun kai fiye da dubu 20, daga cikinsu dalibai masu neman digiri na farko sun kai fiye da dubu 12, yawan dalibai masu neman digiri na biyu da na matsayin docter sun kai kusan dubu l0, Ban da haka kuma akwai dalibai da yawa na kasashen waje su ma suna yin dalibta a wannan jami'a. tashar internet ita ce:

http://www.tsinghua.edu.cn

Jami'ar Fu Dan

Jami'ar Fu Dan tana cikin birnin Shang hai, babban birnin masana'antu da na yin ciniki na kasar Sin, wadda ita ce daya daga cikin jami'o'I masu shahararrun sassan koyon fasaha da na kimiyya na duk kasar Sin.

Yanzu, wannan jami'a tana hade da sassan koyon ilmin zaman al'umma da na halitta da na fasaha da na aikin kulawa, Ban da haka kuma tana da kolejoji da yawa wajen koyon ilmin harsunan kasashen waje da na watsa labaru da na likitanci da na sauransu. Kuma tana da rasha guda 72, da hukumomin bincike guda 65 da cibiyoyin bincike kimiyya guda 91. Yanzu, jami'ar Fu Dan ta zama daya daga cikin cibiyoyin bincike zurfin ilmi wadanda suka shahara a duk duniya,Kuma ta kafa dangantakar hadin guwai wajen yin musaye musaye are da jami'o'I fiye da 200 na shiyoyyi da kasashe daban daban a duk duniya.

Yanzu, jimlar daliban dake wannan jami'a sun kai fiye da dubu 25, Yawan dalibai na kasashen waje dake dalibta a wannan jami'a sun kai l650. tashar internet na wannan jami'a ita ce: http://www.fudan.edu.cn/

Jami'ar horad da malamai ta Beijing

Jami'ar horad da malamai ta Beijing wadda ta kafu ne a shekara ta l902, kuma ita ce jami'a ta farko ta horar da mallamai a tarihin kasar Sin, kuma ita daya daga cikin shahararrun jami'o'I masu horar da malamai na kasar Sin, kuma ita ce wani muhimmin tushen horar da malamai na sassan ilmi iri iri.

Yanzu, Jami'ar horar da malamai ta Beijing tana da kolejoji guda l5, wadanda suke hade da sassan Sinanci da tunanin zuciya da dai sauransu, kuma tana da sassan musaman na koyon digiri na farko guda 48. A kan sassan koyon ilmin koyarwa da tunanin zuciya da ba da ilmi ga yaran da ba su kai ga shiga firamare ba da sauransu duk suna da kwarjini sosai a kasar Sin.

Yanzu, yawan malamai da masu aiki na wannan jami'a sun kai kusan da 2500, kuma yawan daliban dake zaune a Jami'ar sun kai fiye da dubu 20, daga cikinsu daliban dake neman digiri na farko sun kai fiye da 7000, Kuma yawan dalibai na kasashen waje dake dalibta a nan sun kai fiye da dubu guda.

Cikin 'yan shekarun da suka shige, a lokacin da jami'ar Beijing take neman habaka sassan ba da ilmi, kana kuma ta kara habaka sauran sassa. Ban da haka kuma jami'ar Beijing tana amfani da fiffitaccen halinta wajen horar da malaman dake gurbin aiki da horar da dimbin 'yan hukuma. Muna fatan ka shiga internet haka:http://www.bnu.edu.cn/

Jami'ar Nan Jing

Jami'ar Nan Jing tana cikin birnin Nan Jing na lardin Jiang Su dake kudu maso gabashin kasar Sin, ita ce jami'I mai kinshigin sassan koyon fasaha da na kimiyya, ita jami'a mai tasowa kuma ita daya ce daga cikin shahararrun jami'o'I na kasar Sin.

Yanzu, Jami'ar Nan jing take kasance da sassan fasaha da na kimiyya da na labarun kasa da na likitanci da sauran kolejoji guda l2, Kuma jimlar rassanta ta kai 43, kuma jimlar malamanta ta kai kusan 2000, kuma jimlar daliban dake cikin jami'a ta kai fiye da dubu 31, daga cikinsu yawan docter da masu koyon digiri na biyu sun kai fiye da dubu 8.5.

Jami'ar Nan jing ita ce daya daga cikin jami'o'i masu sa himma wajen yin musaye musayen ilmi na tsakanin kasashen duniya na kasar Sin,Mr. Li zheng dao da Mr.Ding zhao zhong da sauransu wadanda suka samu lambar Nobel dukkansu sun zama mallaman prefeser masu daukaka na wannan jami'a. In ka so kara sani abubuwa na wannan jami'a, za ka iya shiga internet haka: http://www.nju.edu.cn/

Jami'ar Zhong shan

Jami'ar Zhong shan dake birnin Guang zhou na lardin Guang dong dake kudancin kasar Sin, wadda ita ce mai cikakkun sassan koyon fasaha da na kimiyya. A shekara ta l924, marigayi Sheng zhong shan shi ne shugaban mai tayar da harkar neman dimakuradiyya ta kasar Sin ya kafa wannan jami'a.

Jami'ar Zhong shan ya kasance da sassan koyon fasaha da na kimiyya, Kuma tana da kolejoji guda l9,Kuma rassanta sun kai 79, wannan jami'a tana da wadansu cikakkun tsarin injuna masu zamani da dakunan yin gwaje gwaye. Kuma Jimlar dalibanta ta kai fiye da dubu 41, daga cikinsu dalibai na neman digiri na farko sun kai fiye da dubu l7, kuma masu neman digiri na biyu sun kai kusan dubu 5 da dari 4 da 40, kuma yawan masu neman matsayin docter sun kai dubu daya da dari 9 da 70, kuma yawan dalibai na kasashen waje dake dalibta a nan sun kai 450, Wani koleji mai suna Lin nan mai ni'ima sosai, kuma kayayyakinsa na zamani wato shi ne daya daga cikin kolejoji masu ni'ima sosai na kasar Sin. Kuma wannan jami'a tana da babban dakin karatu, yawan litattafan dake cikin wannan dakin karatu sun fi yawa sosai. http://www.zsu.edu.cn/

Jami'ar Wu han

Jami'ar Wu han tana cikin birnin Wu Han na lardin Hu Bei dake tsakiyar kasar Sin, Ita daya daga cikin jami'o'I masu cikakkun sassan ilmi daban daban na digiri na biyu. Yanzu, Jami'ar Wu Han tana kasance da sassan koyon filosophiya da na tattalin arziki da na dokokin shari'a da aikin ba da ilmi da na fasaha da na tarihi da na aikin gona da na likitanci da sauransu, wato jimlar manyan sassanta ta kai ll, kuma sassan musamman na neman digiri na farko sun kai l05, kuma jimlar yawan mallamanta ta kai dubu 5, kuma yawan daliban dake jami'ar sun kai fiye da dubu 45, daga cikinsu masu neman digirina biyu sun kai fiye da dubu l2. Cikin 'yan shekaru da suka shige, Jami'ar nan ta gayyaci shahararrun kwararru fiye da 300 na gida da na kasashen waje da su zama prefeser masu daukaka don koyar da daliban Jami'ar nan, Kana kuma ta kafa dangantakar musaye musaye da yin hadin guiwa tare da Jami'o'I fiye da 200 na kasashe fiye da 60 da hukumomin bincike kimiyya.

Jami'ar Wu Han tana karkashin wani tudu mai ni'ima sosai, kuma a gabanta akwai wani babban tafki mai fadi kuma mai kyayawan gani sosai, Wato an ce, Jami'ar Wu Han ita daya daga cikin Jami'o'I masu kyawawan gani sosai na duk kasar Sin. In za ka kara neman sanin abubuwan wannan Jami'a, za ka iya shiga hanyar internet haka: http://www.whu.edu.cn/

Jami'ar Zhe Jiang

Jami'ar Zhe Jiang tana cikin birnin Han zhou na lardin Zhe Jiang dake kudu maso gabashin kasar Sin, kuma ita ce daya daga cikin jami'o'I masu babban fasali da cikakkun sassa daban daban wajen yin bincike ilmi, Kana kuma tana da babban tasiri a duk duniya.

Sassan koyo na wannan jami'a suna shafa tattalin arziki da dokokin shari'a da al'adu da tarihi da sauransu iri iri, wato yawan manyan sassanta sun kai ll, yawan sassan dalibai na neman digiri na farko sun kai l08. Yanzu, yawan mallamai da masu aiki na wannan jami'a sun kai fiye da dubu 8 da dari 7, kuma jimlar dalibai dake jami'ar ta kai fiye da dubu 40, daga cikinsu masu neman samu digiri na biyu sun kai fiye da dubu 9.7, kuma masu neman matsayin docter sun kai fiye da dubu 4.2, haka kuma yawan dalibai na kasashen waje dake dalibta a nan sun kai fiye da l000.

Wannan jami'a ta sami babban sakamako a kan bincike ilmin tattalin arziki da na dokokin shari'a da sauran sassa. Jimlar fadin dakunan karatu na wannan jami'a ta kai muraba'in mita fiye da dubu 59, kuma jimlar litattafan dake ajiye a cikin ta kai fiye da miliyan 5.91. In kana son kara neman sani abubuwa na wannan Jami'a sai ka shiga hanyar Internet haka:http: http://www.zju.edu.cn/

Jami'ar Sichuan

Jami'ar Schuan tana cikin birnin Cheng Du na lardin Schuan dake kudu maso yammancin kasar Sin, wadda sassan koyo na ta mafi fadi kuma mafi girma a dukkan wuraren dake yammancin kasar Sin. Yanzu, sassan ba da ilmi nata suna shafi fasaha da na zaman al'umma da na kimiyyar halitta da na likitanci da sauran sassa, Wato muhimman sassan koyo nata sun kai 9.

Yanzu, wannan jami'a tana da kolejoji 30, kuma rassan musamman sun kai ll8. Yanzu, jimlar malamai da masu aiki ta kai ll357, kuma yawan daliban dake neman sama da digiri na farko sun kai dubu 43.9, daga cikinsu yawan dalibai na neman digiri na farko sun kai fiye da dubu 3, kuma yawan masu neman digiri na biyu sun kai fiye da dubu l0, yawan masu neman matsayin docter sun kai 2740, kuma yawan dalibai na kasashen waje da na shiyyar Hong Kong da na Macau dake dalibta a nan sun kai 653. In ka so kara neman sanin abubuwa na wannan Jami'a sai ka shiga hanyar internet haka: http://www.scu.edu.cn/

Jami'ar zirga zirga ta Shang Hai

Jami'ar zirga zirga ta Shang Hai ita ce sassan kimiya su ne kinshiginta, Wato ita shahararriyar jami'a ce wajen koyon ilmin kimiyya. An kafa wannan jami'a ne a shekara ta l896, Yanzu wannan jami'a tana da sassan koyon ilmin kera jiragen ruwa da aikin teku da sassan kera injuna da aikin ba da labaru da sadarwa da sauransu, Yawan kolejojinta sun kai 21, kana kuma rassan masu neman digiri na farko sun kai 55, wadannan suna shafi ilmin kimiyya da fasaha da na aikin gona da na tattalin arziki da sauransu, daga cikin wadansu sassan koyon ilmin kera jiragen ruwa da na aikin teku da na sadarwa da na yin gyare gyaren kayayyaki dukkansu sun kai matsayi na farko na duk duniya.

Yanzu, yawan daliban dake cikin jami'a wajen neman digiri na farko sun kai fiye da dubu l4, kuma yawan daliban dake neman digiri na biyu da na docter sun kai fiye da dubu 7, Kana kuma dalibai na kasashen waje dake dalibta a wannan jami'a sun kai fiye da l600. A cikin shekara da shekaru da suka shige, wannan jami'a ta horad da hagartattun dalibai fiye da dubu l0, cikin har da shahararrun 'yan siyasa da na zaman al'umma da 'yan kimiyya da kwararru da yawa. In ka so kara neman sani abubuwa na game da wannan Jami'a sai ka shiga hanyar internet haka: http://www.sjtu.edu.cn/

>>[Neman ilmi a kasar Sin]

Takaitaccen bayani na neman ilmi a kasar Sin

A cikin 'yan shekarun da suka shige, tattalin arzikin kasar Sin ya sami saurin bunkasuwa, kana kuma matsayinta na duniya yana nan yana daguwa a kwana a tashi, Sabo da haka ne samari na kasashen waje da suka zo kasar Sin don yin dalibta suna nan suna kara yawa sosai. Yanzu, yawan daliban kasashen waje dake dalibta a kasar Sin sun kai dubu 77, daga cikinsu yawan masu kashe kudi na kansu sun kai kashi fiye da 9 cikin dari. Yawancinsu sun zo ne daga kasar Korea ta kudu da Japan da Amurka da Vietnam da Indonesiya da Thailand da Jamus da Rasha da sauran kasashe na shiyoyi da kasashe na duk duniya.

Muhimmin ilmin da dalibai na kasashen waje suke koyo a kasar Sin shi ne yaren sinanci. Daga cikinsu an hade da al'adun kasar Sin da tarihin kasar Sin da ilmin maganin gargajiya ta kasar Sin da sauran sassan halin musamman na kasar Sin. A cikin 'yan shekaru da suka shige, an habaka sassan koyon ilmi, misali dokokin shari'a da tsimi da kudu da sauran masana'antu.

Yanzu kasar Sin ta kuma dauki matakai don kara habaka fasalin dalibai na kasashen waje da su zo kasar Sin don yin dalibta. Misali, a nuna yarda ga daliban dake yin dalibta a jami'o'I da suke zaune a cikin gidajen mazauna na birane, ta yadda za su kara samu damar yin zaman tare da mazauna na kasar Sin da kyau, ta yadda za su kara neman sanin abubuwan kasar Sin. Kuma a kan matsayin neman digiri na biyu, ana daukar yare iri biyu wato na Sinanci da na Turanci don yin koyarwa tare.

Bisa lisafin da aka yi ba sosai ba, an ce, tun daga bayan kafuwar sabuwar kasar Sin har zuwa yanzu,yawan dalibai na kasashen duniya da suka zo kasar Sin don yin dalibta sun wuce dubu 630, wadannan daliban da suka taba koyo a kasar Sin suna cikin kasashe da shiyoyyi guda l70 na duk duniya.Kuma suna nan suna ba da babban amfaninsu ga gine ginen kasar da neman ci gabansu,Kan kuma sun ba da babban amfnainsu wajen ingiza musaye musaye da yin hadin guiwa ta tsakanin kasar Sin da kasashen duniya gaba.

Koyon yaren Sinanci

Koyon yaren Sinanci shi ne babban makasudin da yawancin dalibai na kasashen waje suka zo kasar Sin don yin dalibta, Yanzu yawan daliban da suke dalibta a kasar Sin wadanda suke koyon yaren Sinanci sun kai fiye da kashi 60 cikin dari. Tsarin koyon Sinansi na kasar Sin yana da halin maras alkibla, Wato tsawon lokacinsa ya kai watanni da makonni, wato wannan shi ne kos na gajeren lokaci, kana kuma akwai tsawon lokaci wato na shekaru hudu wadanda za a nemi digiri na farko na jami'0'i. Kasar Sin ta tsara litattafai iri iri don koyar da daliban kasashen waje yaren Sinansi. Kuma bisa matsayin ilmi daban daban na daliban kasashen waje, cikin aikin koyarwa ana daukar yaren turanci da Sinanci tare don yadda daliban kasashen waje za su koyo da kyau.

Yawancin daliban kasashen waje dake yin dalibta a jami'o'I ne wajen koyon yaren Sinanci. Yanzu, yawan jami'o'in da suka karbar daliban kasashen waje na kasar Sin sun kai fiye da 300, wato kai tsaye ne daliban kasashen waje su kansu su iya yin cudanya tare da jami'o'I daban daban na kasar Sin.

Daga shekara ta l992, kasar Sin ta kafa tsarin matsayin cin jarabawar yaren Sinanci, wadda ake kira "Tuo Fu" na sinanci, kuma bisa matakai daban daban don neman sanin matsayin yare Sinanci na masu ci jarrabawa. Yanzu, ba ma kawai a kasar Sin an shirya irin jarrabawa ba,Kana kuma a kasashe da shiyoyyi 28 na duk duniya, an kafa wuraren ci jarrabawa gomai.

A shiga jami'o'i na kasar Sin

In an shiga jami'o'I na kasar Sin, ya kamata a kai matsayin ilmi da na matsayin Sinansi, Bisa bukatu na jami'o'I daban daban ne, in an shiga wadansu jami'o'I ya kamata za a ci jarabawar shigawa. Dalibai su iya yin cudanya tare da jami'o'I ta hanyar internet, idan an sami iznin shigawa, cikin sauki ne za a iya yin rajista a kasar Sin. Yanzu, yawan jami'o'I fiye da 300 na kasar Sin su iya karbar dalibai na shiyoyyi da kasashen waje.

Kana kuma, kudin da za a kashe a jami'o'I na kasar Sin kadan ne kawai, bisa ire irein sassan da za a yoyi ne yawan kudadden da za a kashe suna da banbanci,Yanzu yawan kudaden da kowanen dalibi na jami'a zai kashe za su kai kudin Sin wajen yuan dubu 20.

Kasar Sin tana sa muhimmanci sosai ga shigar da dalibai na kasashen waje da su zo kasar Sin don yin dalibta a jami'o'I daban daban, Domin wannan ya iya daga matsayin ba da ilmi na duniya da kuma ya zama daya daga cikin hanyoyin gina jami'o'I na matsayi na farko na duk duniya. Sabo da haka ne kasar Sin za ta dauki matakai a jere don kyautata muhallin koyo na daliban kasashen wajen yin dalibta, kuma za ta kara jawo dalibai na kasashen waje, musamman za a kara jawo dalibai masu digiri na biyu da za su zo kasar Sin don yin dalibta.

(Hoto: Dalibai na kasashen waje suna kasar Sin)

■ Kimmiya da Fasaha

An koyar da ilmin kimiyya ta kasar Sin

Jama'a masu sauraro,a cikin shirinmu na yau na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya",za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya ruwaito mana kan yadda aka koyar da ilmin kimiyya a makarantar firamare ta kasar Sin

A da a makarantun firamare na kasar Sin mallaman koyarwa ne suka koyar da ilmi dangane da halitatu ta hanyar ba da bayanai.Kafin shekaru uku,ma'aikatar ilmi ta gwamnatin kasar Sin ta bukaci makarantun firamare da su canza hanyoyin da suke bi wajen bayar da ilmin kimiyya,ta jadadda cewa kamata ya yi mallaman koyarwa su zama jagora yayin da 'yan makarantun firamare ke samun ilmi.Daga nan makarantun firamare na kasar Sin sun fara canza hanyoyinsu na samu ilmi.Kwanakin baya makarantar firamare ta jarrabawa ta lardin Shandong ta gwada nasarorin da ta samu wajen canza hanyoyin koyarwa yayin da koyar da ilmin kimiyya.

Makarantar firamare ta jarrabawa ta lardin Shandong tana birnin Jinan,babban birnin lardin Shandong.Da wakilin gidan rediyonmu ya shiga filin nuna kayayyakin kimiyya da fasaha,sai ya ga wani mutum-mutumin inji mai tsawon centimeter 40 dake tafiya a fili,hannunsa na dauke da tsintsiya,yana tafiya sannu a hankali bisa hanyar da aka tsara masa yana kwashe shara,idan ya kamu da wani katanga,sai ya juya jikinsa yana cigaba.'Yan firamare uku na aji na biyar ne suka tsara shirye shiryen aiki na mutum-mutumin injin nan kuma suka harhada shi.

Kasar Sin tana kara kokarin ilmintar da mutanenta

Jama'a masu sauraro,kasar Sin babbar kasa ce a duniya wadda ke da yawan mutane miliyan dubu da dari uku.A cikin shekarun baya gwamnatin kasar Sin da ma'aikatun da abin ya shafa sun dauki matakai daban daban domin ilmintar da mutanenta kan kimiyya,suna yin yunkurin mayar da su kwararu ta yadda za a ciyar da kasar Sin gaba.To a cikin shirinmu na yau,za mu kawo muku wani bayani kan yadda ake kara wa mutanen Sin ilmin kimiyya.

Cikin shekarun baya,a kan yi binciken yawan ilmin kimiyya da mutanen kasar Sin ke da shi a duk fadin kasar Sin a shekaru bibbiyu domin gane halin da mutanen kasar ke ciki wajen ilmi.Binciken da aka yi ya yi nuni da cewa ilmin kimiyya da mutanen Sin ke da shi ya karu sannu a hankali.Duk da haka Mista Li Daguang,wani jami'in cibiyar nazararin yadda ake bayar da ilmin kimiyya ga kowa ta kasar Sin yana ganin cewa saurin karuwar ilmin kimiyya na mutanen Sin bai kai yadda ake bukata ba.Ya ce "bayan da muka yi wasu binciken mun gane cewa karuwar ilmin kimiyya ta mutanen kasar Sin ba ta kai karuwar tattalin arzikinta ba,Idan an kwatanta da na kasashen yamma masu cigaban masana'antu,ilmin kimiyya da muke da shi bai yi yawa ba."

Bisa hanyoyin da ake bi a duniya wajen gane yawan ilmin kimiyya da ake da su da kuma kimantawa,an ce yawan ilmin kimiyya da mutanen kasar Sin ke da shi ya kai kashi daya da digo casa'in da tara cikin dari a shekara ta 2003,ya karu da kashi da digo shida bisa na shekaru biyu da suka gabata.Bisa labarin da muka samu,an ce yawan ilmin kimiyya da mutanen Japan suke da shi ya kai kashi biyar da digo uku cikin kashi dari a shekara ta dubu biyu,ilmin kimiyya na Amurkawa ya kai kashi 17 cikin kashi dari.

Cikin shekarun baya gwamnatin kasar Sin ta kara rubanya kokarinta wajen samar da ilmin kimiyya ga kowa da kowa ta hanyoyi iri iri ciki har da gina dakunan samar da ilmin kimiyya da buga littattafai da mujalloli na ilmin kimiyya domin kowa da kowa.Lokacin da Mista Wang Yusheng,shugban babban dakin samar da ilmin kimiyya da fasahohi na kasar Sin yake hira da wakilin gidan rediyonmu,ya bayyana cewa matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen ilmantar da jama'a sun fara aiki.Ya ce Kasar Sin ta samu cigaba a bayyane wajen samar da ilmin kimiyya ga kowa cikin shekarun baya.ma'aikatun gwamnati sun fitar da wasu manufoffin dake taimakawa cigaban samar da ilmin kimiyya ga kowa,masu samar da ilmin kimiyya ga kowa sun dukufa wajen aikinsu na baza ilmin kimiyya,sai kara yawa suke,an gina wasu manyan dakunan samar da ilmin kimiyya ga kowa da dakunan samar da ilmin kimiyya na halitatu,kafofin yada labarai sun kara mai da hankalinsu wajen samar da ilmin kimiyya ga kowa,wasu littattafai na samar da ilmin kimiyya sun sami karbuwa a cikin jama'a.Mutanen kasar Sin da suke sha'awar ilmin kimiyya sun yi ta karuwa."

Ban da gwamnati,wasu kungiyoyin jama'a na kasar Sin su ma sun shiga ayyukan samar da ilmin kimiyya ga kowa,kungiyar kula da harkokin kimiyya da fasahohi ta kasar Sin tana daya daga cikinsu.Dukkan 'yan kungiyar nan masu ilmin kimiyya da fasahohi ne.Mista Zhang Yutai,jami'in kungiyar nan ya bayyana cewa cikin shekaru da dama da suka gabata,masana ilmin kimiyya na kungiyar su kan samar da ilmin kimiyya ta hanyar ba da lacca ko horo a cikin makarantu ko ungowoyi ko ta hanyar sadarwa ta internet.Ya ce " Kungiyar kimiyya da fasahohi ta kasar Sin tana da fiffiko wajen mallakar ilmin hanyar sadarwa ta internet,ta shirya masana da kwararrun ilmin kimiyya da fasahohi da su shiga kauyuka da ungowoyi na birane da garuruwa da kuma matasa su kan samar da ilmin kimiyya ta hanyar ba da horo da rahoto ko ta kafofin yada labarai kamar gidajen telebijin da na rediyo,da hanyar sadarwa ta internet da littattafai da mujalloli."

Duk da haka kokarin da muke yi bai kai yadda ake bukata a kasar Sin ba saboda yawan mutanenta,yawancin mutanen ba su da ilmin kimiyya da biyan bukatun cigaban kasar ke bukata ba.Shi ya sa gwamnatin kasar Sin na cigaba da kokarinta wajen kara baiwa mutanenta ilmin kimiyya da fasahohi yadda ake bukata.

Kasar Sin ta bude kasuwar duniya ta kumbunan samaniya

A farkon watan Afrilu na shekara ta 2005 ne wani roket da kasar Sin ita kanta ta kera da ake kira "long March" lamba uku da ke dauke da wani tauraron dan Adam na sadarwa mai lamba shida na Asiya da Pacific da kasar Faransa ta kera ya tashi daga cibiyar harba kumbunan samaniya ta Xichuang dake kudu maso yammacin kasar Sin tare da nasara ya shiga hanyar da aka tsara a sararin samaniya.Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta harba watan dan Adam kirar kasashen waje bayan shekaru shida da ta dakatar da harkokin harbar kumbunan samaniya a kasuwar duniya.

A hakika,ban da samar da hidima wajen harkokin harba kumbunan samaniya a kasuwar duniya,tare da saurin cigaban da ta samu wajen fasahohin kera kumbunan cikin shekarun baya,ga shi a yanzu kasar Sin za ta iya samar da taurarin sadarwa iri iri a kasuwar duniya.A cikin shirinmu na yau na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya rubuto mana a kan wannan fanni.

A shekara ta 1985 ne kasar Sin ta shiga kasuwar duniya ta kumbunan samaniya,muhimmiyar harkarta ita ce samar da hidima wajen harba taurarin dam Adam.Kawo yanzu ta harba taurarin dan Adam talatin domin kasashen waje cikin yin amfani da rokoki Long March sama da sau ashirin.A cikin shekaru shida da suka gabata,kasar Sin ta dakatar da tabbatar da kwangilolin da ta daddale saboda rashin daidaici cikin takara a kasuwar duniya.

Hadin kan kasar Sin da Jamus wajen bincike ilmin kimiyya

Kwanakin baya ba da dadewa ba cibiyar binciken ilmin kimiyya ta kasar Sin da kungiyar Max Planck Society,wata shahararriyar kafa ce ta binciken ilmin kimiyya ta kasar Jamus sun yi wani gaggarumin bikin murnar ranar cikon shekaru 30 na hadin kan bangarori biyu tare a nan birnin Beijing.Shugaban kasar Sin Mr.Hu Jintao da takwaransa na kasar Jamus Mr.Johannes Rau sun aiko sakonnin taya murna inda suka yaba da hadin kai tsakanin cibiyar binciken ilmin kimiyya ta kasar Sin da kungiyar Max Planck society da cewa misali ne na hadin kan kasashen duniya wajen ilmin kimiyya da fasaha.

Mista Hu Genxi,wani masanin binciken ilmin kimiyya na farko ne mai shekaru 40 da haihuwa a wannan shekara,yana aiki ne a dakin binciken kimiyya kan sanadin cututtuka na hukumar binciken ilmin kimiyyar abubuwa masu rai dake karkashin cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin.ya zama madugun kungiyar matasa 'yan kimiyya ta Max Planck bayan da ya koma gida daga wata jami'ar Amurka wanda yake aiki ta hanyar daukan ma'aikata a duniya.Daga baya kungiyarsa ta sami nasara mai tsokane idanu a duniya wajen binciken abubuwan kwayoyin halitta da ake kira genes a turance.

Cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin da kungiyar binciken kimiyya ta Max Planck society sun zabi Mista Hu Genshi ta hanyar daukan ma'aikata.Hanyar da aka bi wajen daukar ma'aikata ta taka muhimmiyar rawa wajen samo madugan matasa masu binciken kimiyya.Mista Hu Genxi ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa afarkon shekarun 1990,tsarin cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin ta shiga tsohon yayi.Domin cimma burin kai matsayin duniya.

© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China