>
Babi06: Kabilu da Addinai
■ Kabilu

>>[Kabilun Kasar Sin]

Kabilun Kasar Sin

Kasar Sin dayantacciyar kasa ce mai kabilu da yawa, kuma tana daya daga cikin kasashe mafiya yawan mutane a duniya. A halin yanzu. yawan mutanenta ya kai miliyan 1300, kuma tana da kabilu 56.

Kabilu na kasar Sin sun hada da kabilar Han, da ta Mongoliya, da Hui, da Tibet, da Uygur, da Miao, da Yi, da Zhuang, da Buyi, da Korea, da Man, da Dong, da Yao, da Bai, da Tujia, da Hani, da Hazak, da Dai, da Li, da Lisu, da Wa, da She, da Gaoshan, da Lahu, da Shui, da Dongxiang, da Naxi, da Jingpo, da Kurkez, da Tu, da Dawoer, da Mulao, da Qiang, da Bulang, da Sala, da Maonan, da Gelao, da Xibo, da Achang, da Pumi, da Tajik, da Nu, da Uzbek, da Rasha, da Ewenke, da Deang, da Baoan, da Yugu, da Jing, da Tatar, da Dulong, da Elunchun, da Hezhe, da Menba, da Luoba, da kuma kabilar Jinuo. Sa'an nan kuma akwai wasu mutane da ba a san ko daga wace kabila ce suka fito ba.

A kasar Sin, 'yan kabilar Han sun dauki kimanin kashi 92 cikin dari bisa dukkan mutanen kasar, sauran kashi 8 ko fiye su ne 'yan kananan kabilu. Ban da kabilar Han, a kan kira sauran kabilu 55 na kasar Sin da sunan "kananan kabilu", dalilin da ya sa haka shi ne domin 'yan kabilun nan ba su da yawa idan an kwatanta su da 'yan kabilar Han. Yawancin 'yan kananan kabilun nan suna zama ne a wurare da ke a arewa maso yammacin kasar Sin da kudu maso yamma da arewa maso gabas da kuma sauransu.

Bisa sauye-sauyen tarihi na dogon lokaci, yanzu 'yan kabilu dabam daban na kasar Sin suna zama ne a yawancin wuraren da 'yan kabilar Han suka fi yawa, haka nan kuma yawancin 'yan kananan kabilu suna zaune ne a wasu wuraren da suke zama a cunkushe. Daga cikin kananan kabilu 55, ban da 'yan kabilar Hui da kabilar Man duka suna magana ne da yaren kabilar Han wato Sinanci da kuma yin rubutu da shi, sauran 'yan kananan kabilu kuwa suna magana da harsunansu ko Sinanci, kuma suna yin rubutunsu. A cikin shekaru masu yawa da suka gabata, 'yan wadannan kananan kabilu 56 suna zaman rayuwa da yin sana'o'i tare a yankunan kasar Sin masu fadin muraba'in kilomita miliyan 9 da dubu 600, sun kuma rubuta dogon tarihin kasar Sin, da kyawawan al'adunsu.

Kabilu wadanda yawan mutanen ko wacensu ya wuce miliyan goma

Kabilar Han

Kabilar Han ita ce ta fi yawan mutane a cikin duk kabilu 56 na kasar Sin, haka kuma ita kabila ce mafi yawan mutane a cikin duk kabilu na duniya. Yanzu, yawan 'yan kabilar Han ya kai wajen biliyan 1.2. Yau fiye da shekaru 5,000 ke nan da aka sami tarihin wayin kai na kabilar Han, a zamanin da, 'yan kabilar Han mutane ne da ke zaune a wurare da ke a mafarin Rawayen Kogi da tsakiyarsa, wadanda kuma ake kiransu da sunan "Hua Xia". A cikin wannan tsawon lokaci ne, 'yan kabilar Han sun yi ta yin auratayya a tsakaninsu da 'yan sauran kabilu sannu a hankali, daga baya dai suna da nasaba sosai a tsakaninsu. An fara kiran wadannan mutanen sunan kabilar Han ne tun daga zamanin daular Han. 'Yan kabilar Han suna magana da yarensu da kuma yin rubutu da shi. Yaren Han yana cikin reshen harshen Han da na Tibet, yana da manyan karin harshuna guda 8 wandanda suka hada da karin harshe na arewa, da karin harshe mai suna "Wu", da "Xiang", da " Gan", da "Kejia", da " Minnan", da "Minbei" da kuma "Yue", amma dukansu suna magana da "Putonghua", wato daidaitaccen Sinanci. Rubutun Han yana daya daga cikin tsoffin rubuce-rubuce a duniya, kuma sannu a hankali aka mayar da rubutun Han da aka yi a kan kasusuwa da tsoffin abubuwa da aka yi da tagulla don su zama rubutun Han na yanzu. Yawan babbakunsa ya wuce 80,000. Daga cikinsu, akwai babbaku 7,000 wadanda aka fi yin rubutu da su. Yanzu, harshen Han ya zama daya daga cikin manyan harsuna da aka fi yin magana da su a duniya. Hatsi babban abinci ne ga 'yan kabilar Han, sa'an nan kuma suna cin naman dabbobi da kayayyakin lambu. A cikin wani dogon lokaci da ya wuce, sannu a hankali 'yan kabilar Han sun saba da cin abinci sau uku a ko wace rana. Shinkafa da alkama manyan abinci iri biyu ne ga 'yan kabilar Han. Ban da wadannan kuma suna cin masara, da dawa, da gero, da doya da sauran irinsu a wurare dabam daban. Bisa hali da ake ciki a wurare dabam daban dangane da zaman yau da kullum, 'yan kabilar Han sun sami al'adar cin abincinsu iri dabam daban. A kan rarraba dafaffun kayayyakin lambu da 'yan kabilar Han da na sauran kabilu suka dafa gida hudu wadanda suka hada da "kayan lambun kudu mai zaki" da "kayan lambun arewa mai gishiri" da "kayan lambun gabas mai yaji" da kuma "kayan lambun yamma mai tsami". A halin yanzu, daga dadin wadannan kayayyakin lambu da ake dafawa, aka sami dafaffun kayayyakin lambu iri 8 wadanda suka hada da dafaffun kayayyakin lambu na "Xiang" da "Chuan" da "Yue", da "arewa maso gabas" da kuma sauransu. Giya da ruwan shayi manyan abubuwan sha ne iri biyu ga 'yan kabilar Han. Kasar Sin kasa ce da aka fara samun shayi, kuma daga wajenta ne aka gano hanyar da ake bi wajen yin giya tun da farko a duniya. Tun can shekaru aru-aru, ya kasance da al'adun giya da na shayi a kasar Sin. Ban da wadannan abubuwan sha iri biyu, ana yin amfani da 'ya'yan itatuwa iri dabam daban wajen samun ruwan sha a wurare dabam daban kuma a yanayi dabam daban. 'Yan kabilar Han suna da bukukuwan gargajiya masu yawa, daga cikinsu, bikin sallar bazara da a kan yi bisa kalandar manoma ta kasar Sin ita ce ta fi muhimmanci. Ban da wadannan kuwa akwai sauran manyan bukukuwa wadanda suka hada da bikin fitilun gargajiya da a kan shirya a ran 15 ga watan Janairu na kalandar manoma, da bikin bautawa a kaburburan kakani da kakani a ran 5 ga watan Afrilu na kalandar Miladiyya, da bikin tseren kwalekwalen gargajiya na kasar Sin da a kan yi a ran 5 ga watan Mayu na kalandar manoma ta kasar Sin, da kuma bikin tsakiyar watan Augusta na kalandar manoma ta kasar Sin da sauransu.

Kabilar Zhuang

Kabilar Zhuang wata kabila ce da yawan mutanenta ya fi na duk sauran kananan kabilu na kasar Sin. Yawancinsu suna zaune ne a Jihar Guangxi Ta Kabilar Zhuang Mai Ikon Aiwatar Da Harkokin Kanta da ke a kudancin kasar Sin, suna magana da harshen Zhuang wanda ke cikin reshen harshen Tibet da Sinanci. 'Yan kabilar Zhuang mazaunan wurin asali da ke a kudancin kasar Sin, suna da dogon tarihi. A cikin shekaru dubbai da suka wuce, kakanin-kakanin 'yan kabilar Zhuang sun fara zama a wurare da ke a kudancin kasar Sin. An kafa Jihar Guangxi Ta Kabilar Zhuang Mai Ikon Aiwatar Da Harkokin Kanta a shekarar 1958. Aikin gona babbar sana'a ce ga 'yan kabilar Zhuang. Shinkafa da masara amfanin gona ne da suka fi nomawa. 'Yan kabilar Zhuang suna sha'awar wake-wake ainun, sabo da haka an nuna yabo cewa, kauyukan 'yan kabilar Zhuang wurare ne na masu tashin wake-wake. Zanen siliki mai launi iri na kabilar Zhuang (Zhuang brocade) kayan fasaha na gargajiyar 'yan kabilar Zhuang ne. A zamanin da, 'yan kabilar Zhuang suna bin tsohon addini. Bayan zamanin daular Tang da ta Song, an yadada addinin Buddah da na Dao a wurare da 'yan kabilar Zhuang ke zaune. A zamanin yanzu, addinin Kirista da na Katolika su ma an yadada su a wadannan wuraren 'yan kabilar Zhuang, amma har yanzu dai wadanda ke bin wadannan addinai biyu ba su da yawa.

Kabilu wadanda yawan mutanen ko wacensu ya yi kasa da dubu 10

A kasar Sin, akwai kabilu 20 wadanda yawan mutanen ko wacensu ya yi kasa da dubu 100. Wadannan kabilun sun hada da kabilar Bulang, da ta Tajik, da Achang, da Pumi, da Ewenke, da Nu, da Jing, da Jinuo, da Deang, da Baoan, da Rasha, da Yugu, da Uzbek, da Menba, da Elunchun, da Dulong, da Tatar, da Hezhe, da Gaoshan, da kuma ta Luoba.

Kabilar Luoba

Yawan 'yan kabilar Luoba ya kai kimanin 3, 000. Idan an kwantata su da na sauran 'yan kabilu na kasar Sin, sai a gano cewa, 'yan kabilar Luoba sun yi kadan. Yawancinsu suna zaune ne a kudu maso gabashin jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin. 'Yan kabilar Luoba da ke zaune a arewacin gunduma mai suna Motuo suna magana da harshen Tibet, sauran 'yan kabilar nan kuma suna magana da harshen Luoba. Harshen Luoba yana cikin tsarin harshen Han da na Tibet, karin harshen nan da 'yan kabilar ke magana ya sha bamban a wurare dabam daban da suke zaune. An sami kalmar Luoba ne daga harshen Tibet, ma'anarta ita ce "mutanen kudu", kuma 'yan kabilar Tibet na kiransu da sunan haka. Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, 'yan kabilar Luoba sun tuna da abubuwa ne ta hanyar sassaka katako da nannade igiya, ba su da rubutunsu, kuma kadan daga cikinsu suna jin harshen Tibet sosai. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, 'yan kabilar Luoba suna more ikonsu na zaman daidaici a tsakanin kabila da kabila, kuma sun fara yin sana'o'insu ta hanyar zamani bisa babban taimako da gwamnatin kasa da 'yanuwa na sauran kabilu daban daban suka yi musu, sun zami ci gaba da sauri wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da na al'adu. 'Yan kabilar Luoba suna bin addinin zamanin da wato nuna imani ga duk halittu.

Kabilar Dulong

Yawan 'yan kabilar Dulong ya kai 7,400 ko fiye. Yawancinsu kuwa suna zaune ne a wurare da ke kwarin Kogin Dulongjiang na gundumar Gongshan ta kabilar Dulong da ta Nu mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta lardin Yunan. Suna magana da yarensu na Dulong, wanda ke cikin reshen harshen Han da na Tibet, amma ba su da rubutu. 'Yan kabilar Dulong sun yi imani da duk abubuwan da ke da rai, kuma suna nuna girmamawa ga halitta. A cikin littafi mai suna "Dayantaccen Tarihin Zamanin Babbar Daular Yuan", an fara bayyana wasu abubuwa dangane da kabilar Dulong, amma an kira wannan kabilar da sunan "Qiao". Zuwan zamanin daular Ming da ta Qing, an fara kiran kabilar nan da sunan "Qiu" ko " Qu". Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, an amince da sunan "Dulong" da 'yan kabilar nan ke kiran kansu da shi, wato ke nan sun cim ma burinsu. A zamanin da, 'yan kabilar Dulong suna baya-baya ainun wajen yin sana'o'i da zaman rayuwarsu. Sun yi amfani da kayayyakin aiki da suka yi da itacen daji da gora, sun yi aikin noma ta hanyar kona karmami da sauran karan amfanin gona da itatuwa da aka yi sassabensu. Sa'an nan kuma sun yi dibar 'ya'yan itatuwa da ganyaye, da aikin kamun kifaye, da farauta duk domin zaman rayuwarsu na yau da kullum. Bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, an kubutar da 'yan kabilar Dulong daga wannan halin na kasancewa baya-baya. 'Yan kabilar Dulong mutane ne masu himma, da son baki, da zumunci kwarai. Idan wani daga cikinsu ya gamu da wahala, sai sauran duk mutanen kauyensa za su taimake shi. Haka nan kuma naman daji da suka samu, su kan rarraba shi a tsakanin duk masu farauta. Su kan cika alkawarinsu, kuma maganarsu ba ta tashi, kuma da kyakkyawar al'adar gargajiyarsu, alal misali, " yana da wuya a yi tsintuwa a kan hanya saboda babu wanda kayansa ke bacewa, kuma mutane ba su kulle kofa da dare, saboda akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali ".

Kabilar Jinuo

Yawan 'yan kabilar Jinou ya wuce 20,000, yawancinsu suna zaune ne a wani babban dutse na yankin Xishuangbanna na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Suna magana da harshensu, amma ba su da rubutu. Harshen Jinuo wani reshe ne ga tsarin harshen Han da na Tibet. A da, 'yan kabilar Jinuo sun nuna imaninsu ga duk halittu, kuma suna nuna girmamawa ga kakanni-kakanninsu. 'Yan kabilar Jinuo suna kiran kabilarsu da sunan Jinou. Babu bayani da aka rubuta cikin littafin tarihi dangane da asalin kabilar Jinou. 'Yan kabilar nan suna nuna girmamawa ga marigayi dan siyasa Zhuge Liang. An ce, wasu sojoji na marigayi Zhuge Liang sun yi kaura zuwa wuraren kabilar Jinou ne daga Puer da Mojiang da kuma sauran wurare masu nisa da ke a arewacin kasar Sin. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, 'yan kabilar Jinou sun shiga zamanin gurguzu daga karshen zamanin jahiliya, sun kubutar da kansu daga halin baya-baya da suke ciki na yin noma ta hanyar sassabe da kona ciyawa da itatuwa, da tunawa da abubuwa ta hanyar sassaka gora, da yin ciniki ta hanyar musayar kayayyaki, da warkar da masu cuta ta hanyar camfe-camfe. A halin yanzu, ma'aikatan hukuma da likitoci da 'yan kasuwa da ma'aikatan gona sun riga sun kware wajen ayyukansu.

Kabilar Elunchun

Yawan 'yan kabilar Elunchun ya zarce 8,000, da yawansu suna zama a dutse mai suna Da Xinganling da dutse mai suna Xiao Xinganling da ke a mahadar jihar Mongoliya Ta Gida Mai Ikon Aiwatar Da Harkokin Kanta da lardin Heilongjiang. Akwai gundumar kabilar Elunchun mai ikon aiwatar da harkokin kanta da aka kafa a yankin Hulunbeier na Jihar Mongoliya Ta Gida Mai Ikon Aiwatar Da Harkokin Kanta. 'Yan kabilar Elunchun suna magana da harshensu wanda yake daya daga cikin tsarin harshen Aertai. Amma ba su da rubutu, su kan yi rubutun Sinanci wato rubutun kabilar Han. "Elunchun" suna ne da 'yan kabilar nan ke kiran kansu da shi, ma'anarta ita ce "mutanen da ke zaune a kan dutse". A farkon zamanin daular Qing, an riga an rubuta wannan sunan kabilar a cikin littafin tarihi. Tun can zamanin da, babbar sana'a ce da 'yan kabilar Elunchun suka fi yi ita ce farauta, sai kuma aikin kamun kifaye da cire ganyaye da sauran abubuwa. Kusan duk maza masu dadin hannu ne kuma sun kware wajen hawan dawaki, sun fahimci halayen zaman rayuwar naman daji iri daban daban sosai, don haka sun kware kwarai wajen yin farauta. Kusan a ce, a shekarun 1940, kabilar nan wata kabilar mayawata ce. Duk namun daji da 'yan kabilar suka samu su kan rarraba shi a tsakaninsu daidai wa daida. Haka nan kuma sun saba da rarraba wa junansu abubuwan zaman yau da kullum daidai wa daida kamar yadda aka yi a zamanin jahiliya. Musamman ma tsofaffi da marasa lafiya da wadanda suka ji raunuka da nakasassu su iya samun rabonsu, kuma rabonsu ya fi sauran yawa. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, 'yan kabilar Elunchun sun shiga cikin lokacin zaman gurguzu kai tsaye. Yanzu an riga zaunar da su a wuri daya, sun yi sallama da aikin farauta, kuma sun zama masu kare dazuzzuka da naman daji. 'Yan kabilar Elunchun masu fasaha da himma ( clever da deft) ne. Sun iya yin kyawawan kayayyakin fasaha da bawon itatuwa kamar su tufafi da takalma da akwatuna da bokitai da makamantansu, har da kananan kwale-kwale. Dadin dadawa an yi zane-zane masu kyaun gani a jikin wadannan abubuwa. A galibi dai, 'yan kabilar Elunchun suna bin wani irin addinin da ake kira "Saman" cikin harshensu, suna nuna imani ga halittu, kuma suna nuna girmamawa ga kakannin-kakanninsu.

Kabilar Tatar

Yawan 'yan kabilar Tatar ya tashi kimanin 5,000, suna zaune a wurare dabam daban na Jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kanta, amma da yawa suna zaune a birnin Yining da birnin Tacheng da birnin Urumqi da sauran birane. 'Yan kabilar nan suna magana da harshensu wanda yake daya daga cikin tsarin harshen Aertai. Ban da tsofaffi suna magana da harshen Tatar, sauran 'yan kabilar nan suna magana da harshen Hazak ko harshen Uygur. Wasu 'yan kabilar Tatar sun dauki babbakun Larabaci a matsayin babbakun harshensu, amma da ya ke 'yan kabilar sun dade suna zaune tare da 'yan kabilar Hazak da ta Uygur, suna cuduwa da junansu sosai, sabili da haka 'yan kabilar Tatar su kan yi rubutun harsunan kabilun nan biyu. Yawancin 'yan kabilar Tatar musulmi ne. Kakanni-kakanninsu sun fito ne daga wata kabila mai suna "Dada" ta tsohuwar kasa mai suna "Tujuehan da ke a arewancin kasar Sin, tun can farko ne aka taba rubuta labarunsu a cikin littafin tarihi na zamanin daular Tang. A lokacin da 'yan kabilar Mongoliya suka yi maci zuwa yamma a karni na 13, mutanen yammacin duniya sun kira su da sunan Tatar. A farkon karni na 19, 'yan kabilar Tatar da yawa sun yi kaura daga kasar Rasha zuwa jihar Xinjiang ta kasar Sin, haka nan kuma sauran 'yan kabilar Tatar da dama su ma sun yi kaura zuwa kasr Sin bayan yakin duniya na biyu, dukansu sun zama 'yan kabilar Tatar a kasar Sin. Kiwan dabbobi babbar sana'a ce ga 'yan kabilar Tatar da ke zaune da kauyuka. Yawan masu ilmi 'yan kabilar Tatar musamman ma masu aikin ba da ilmi su kan zauna a garuruwa da birane, sun ba da babban taimakonsu ga aikin ba da ilmi a jihar Xinjiang.

Manufar kasar Sin dangane da harkokin kabilu

Kasar Sin dayantacciyar kasa ce mai kabilu da yawa. Gwamnatin kasar Sin tana aiwatar da manufar harkokin kabilu bisa zaman daidaici tsakanin kabila da kabila, da hadin kansu, da kuma bai wa junansu taimako, sa'an nan kuma tana girmama 'yancin bin addinai na kananan kabilu, da dabi'unsu, da dai al'adunsu, kana tana kare su yayin da suke yin wadannan abubuwa.

Tsarin wuraren kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu wani tsarin siyasa ne mai muhimmanci ga kasar Sin. A karkashin wannan tsarin, 'yan kananan kabilu dabam daban suna aiwatar da harkokin mulkinsu da kansu a wuraren da suke zaune a cunkushe, suna kafa hukumominsu don aiwatar da harkokin mulki su da kansu duk a dayantaccen jagorancin gwamnatin kasa. Gwamnatin kasa tana ba da tabbaci ga hukumomin kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokinsu su gudanar da dokokin shari'ar kasa da manufofinta bisa hakikanin halin da ake ciki a wadannan wurare; da horar da 'yan kananan kabilu masu dimbin yawa don su zama ma'aikatan hukuma ta matakai dabam daban da kwararru a fannoni dabam daban da kuma ma'aikata 'yan fasaha; kuma a karkashin shugabancin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, jama'a 'yan kabilu dabam daban da ke zaune a wuraren kananan kabilau masu ikon aiwatar da harkokin kansu su hada guiwarsu da sauran jama'ar duk kasa baki daya, su yi kokari sosai wajen raya kasar Sin mai tsarin mulkin gurguzu, da gaggauta bunkasa harkokin tattalin arziki da na al'adu na wurarensu, su raya wurarensu masu wadata da hadin kai.

Bisa abubuwa da aka yi a cikin fiye da shekaru 10 da suka wuce, Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wadda ke rike da mulkin kasa ta sami ra'ayoyinta da manufofinta masu yawa dangane da batutuwan kabilu. Wadannan ra'ayoyi da manufofi sun hada da bullowar kabilu da ci gabansu da kuma hallakarsu zai dauki dogon lokaci, sabili da haka ma yana kasancewa da batutuwan kabilu har cikin dogon lokaci.

Lokacin zaman gurguzu lokaci ne da duk kabilu ke samun wadata da arziki tare, sa'an nan kuma abubuwa iri daya da ke tsakanin kabila da kabila kullum sai kara yawa suke yi, amma za a ci gaba da samun halayen musamman da bambance-bambance tsakanin kabila da kabila.

Matsalar kabilu tana daya daga cikin matsalolin zamantakewar al'umma. Babu yadda za a yi a daidaita matsalar kabilu sannu a hankali, sai an daidaita duk matsalolin zamantakewar al'umma, kuma sai ta hanyar yin sha'aninsu na raya zaman gurguzu, za a iya daidaita matsalar kabilun kasar Sin ta yanzu sannu a hankali.

Duk kabilu kome yawan mutanensu, da tsawon lokacin tarihinsu, da kuma matsayinsu na bunkasuwa dukansu sun ba da taimakonsu ga raya wayin kan kasarsu, sabili da haka kamata ya yi, su yi zaman daidaici a tsakaninsu. Haka nan kuma a kara karfin hadin kan jama'ar kabilu dabam daban, su kare dinkuwar kasa.

Yin kokari sosai wajen bunkasa harkokin tattalin arziki babban aiki ne ga raya zaman guruzu, kuma ga ayyukan kabilun kasar Sin a zamanin yau. Don haka ya kamata, duk kabilu su taimaki juna don neman samun ci gaba da wadatuwa tare.

Tsarin wuraren kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu babban taimako ne da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta bayar ga hasashen Marksanci dangane da harkokin kabilu, kuma babban tsari ne ga daidaita batutuwan kabilu na kasar Sin.

A yi kokari wajen horar da 'yan kananan kabilu masu dimbin yawa don su zama nagartattun ma'aikatan hukuma masu ilmi, wannan yana da matukar muhimmanci ga gudanar da harkokin kabilu da kyau da kuma daidaita batutuwan kabilu.

A wasu wurare, ba za a iya bambanta batutuwan kabilu daga batutuwan addinai ba, sabo da haka ya kamata, a mai da hankali sosai ga aiwatar da manufofin gwamnati dangane da harkokin addinai cikin gaskiya kuma daga duk fannoni, a duk yayin da ake neman daidaita batutuwan kabilu.

Haka zalika a lokacin da gwamnatin kasar Sin ke kokartawa wajen neman bunkasa harkokin tattalin arziki, da al'adu, da na ba da ilmi, da kuma sauran sha'anoni, tana daga matsayin zaman rayuwar dimbin 'yan kananan kabilu ciki har da masu bin addinai a fannin kayayyaki da al'adu, ta fi mai da hankali ga girmama wa 'yan kananan kabilu 'yancin bin addinansu, da kare al'adun tarihi na kananan kabilu. Ta yi bincike-bincike a kan kayayyakin al'adun tarihi ciki har da al'adun addinai, ta tattara su, ta yi nazari a kansu, ta kyautata su, kuma ta wallafa littattafansu. Ban da wadannan kuma gwamnatin kasar Sin ta kashe makudan kudade wajen yin kwaskwarima a kan haikalai da dakunan Ibada wadanda ke da muhimmanci ga tarihi da al'adu a wuraren da kananan kabilu da yawa ke zaune.

Horar da 'yan kannan kabilu harkar shugabanci

Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankalinta sosai ga horar da 'yan kananan kabilu don su zama shugabanni. Yawan shugabanni 'yan kananan kabilu ya karu sosai, har wa yau da yawa daga cikinsu sun ci zaben zaman shugabanni na matakai dabam daban masu matsayin sama da gunduma. Yanzu, 'yan kananan kabilu suna rike da duk mukaman gwamnonin jihohin kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu guda 5 a kasar Sin, da na shugabannin yankunan kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu guda 30, da shugabannin gundumomin kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu guda 119.

Haka zalika jama'ar kabilu dabam daban suna kula da harkokin siyasa da na zamantakewar al'umma na kasar Sin. Duk kabilu 56 na da wakilansu da shugabanninsu a cikin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin. Yawansu kuwa ya dauki sama da kashi 10 cikin dari bisa na duk mambobin majalisun nan biyu.

>>[Tattalin Arzikin Kabilu]

Harkokin tattalin arziki na kananan kabilun kasar Sin

Yayin da ake ta samun ci gaba wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin, an kuma yi ta samun ci gaba wajen bunkasa harkokin tattalin arziki a wurare da 'yan kananan kabilu masu yawa ke zaune.

Aikin kiwo yana daya daga cikin manyan sana'o'i da ake yi a wurare da 'yan kananan kabilu masu yawa ke zaune a kasar Sin. Bayan shekaru 80 na karni na 20, an fara gudanar da tsarin dora nauyin aikin kiwo da na hakki a wuyar makiyaya a kasar Sin, wato ke nan an sayar wa iyalan makiyaya da dabbobin kungiyar hadin guiwar makiyayya, an kuma rarraba musu filayen ciyawa, haka nan kuma an yi ta kara kokari wajen raya filayen ciyawa, da kuma kula da su. Yanzu, an riga an sami ci gaba da sauri wajen bunkasa aikin kiwon dabbobi a manyan makiyayai na kasar Sin wadanda suka hada da lardin Qinghai, da na Gansu, da Sichuan, da jihar Xinjiang, da ta Ningxia, da kuma ta Mongoliya ta Gida da dai sauransu. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, jimlar dabbobi da ake kiwo yanzu a makiyayai da sauran waurare na kasar Sin ta kai kimanin miliyan 100. Yawan dabbobi da suke rayuwa da wadanda ake sayar da su dukansu ya karu sosai. Haka zalika yanzu, an kafa makiyaya na iyalai masu zaman kansu a makiyayai da dama. Wadannan makiyayan iyalai masu zaman kansu sun kara cin riba sosai daga wajen dabbobi masu dimbin yawa da suke kara kiwo ta hanyar zamani.

Birane na yankuna da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune cibiyoyi ne ga bunkasa harkokin tattalin arziki na wadannan yankunan, dalilin da ya sa haka shi ne domin ana samun albarkatan tattalin arziki mai yawa, kuma ana yawan yin harkokin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma da ba na aikin noma ba. Bayan shekaru 80 na karni na 20, an gaggauta bunkasa harkokin tattalin arzikin birane na yankuna da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune, yayin da ake bunkasa harkokin tattalin arziki a sauran wurare na kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yanzu, yawan masana'antu da ake da su a wuraren kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu na kasar Sin ya kai kimanin miliyan 1, ta haka an kafa tsarin masana'antu da ke hade da manyan masana'antu na zamani, da masana'antu masu zaman kansu, da kasuwanni, da wuraren hidima da sauran irinsu da yawa. Yawan mutane da ke zaune a birane na jihar Mongoliya ta gida, da ta Ningxia, da Xinjiang da lardin Qinghai da dai sauransu ya wuce matsakaicin yawan mutane da ke zaune a birane na kasar Sin. Wannan ya ba da babban taimako wajen bunkasa harkokin tattalin arziki a wurare da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune daga fannoni dabam daban.

Sakamakon da aka samu wajen bunkasu tattalin arziki na masu zaman kansu ya alamanta ci gaba da aka samu wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin birane na yankunan da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune. Alal misali, a karshen karni na 20, yawan kudi da aka samu daga wajen tattalin arziki na masu zaman kansu ya dauki fiye da kashi 40 cikin dari bisa jimlar kudi da aka samu wajen samar da kayayyaki a duk lardin Qinghai.

Ban da wadannan kuma yayin da ake kara aiwatar da manufar bude wa kasashen waje kofa a kasar Sin, birane da dama na yankuna da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune su ma a hankali-hankali sun kara yin musaye-musaye da hadin guiwa tsakaninsu da kasashen waje a fannin tattalin arziki da fasaha. Yanzu, a wadannan yankuna, an riga an kafa manyan masana'antu da yawa wadanda suka shahara sosai a gida da waje, kamar Babban Kamfanin Eredus Na Yin Kayayyakin Ulu Mai Taushi na Jihar Mogoliya ta Gida Mai Ikon Aiwatar Da Harkokin Kanta, da Babban Kamfanin Tianshan ta Jihar Xinjiang Ta Kabilar Uygur Mai Ikon Aiwatar Da Harkokin Kanta da dai sauransu.

Kimiyya da fasaha ta kananan kabilun kasar Sin

Domin neman gaggauta bunkasa harkokin kimiyya da fasaha a wurare da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune, gwamnatin Sin ta dauki matakai masu yawa musamman wajen horar da 'yan kananan kabilu don su zama 'yan kimiyya da fasaha. Jami'o'i da kolejoji sun dauki dalibai 'yan kananan kabilu ko shirya musu kosakosai yadda aka tsara, kuma an kara kafa sassan koyon ilmi da ake karancinsu a jami'o'i da kolejojin kananan kabilu don kara horar da dalibai 'yan kananan kabilu da su zama masu fasaha a fannoni dabam daban. Haka nan kuma an dauki tsauraran matakai wajen daga matsayin ilmi na 'yan kananan kabilu, an taimaki kananan kabilu wajen shigar da kwararru da kayayyakin aiki na zamani cikin wurarensu, an kyautata masana'antunsu na gargajiya da kayayyakin gargajiya da suke fitarwa, don kara cin riba daga wajen tattalin arziki, an kafa tsarin yadada kimiyya da fasaha da kuma kyautata shi a kauyuka da makiyayai, an kara kokari wajen koya wa 'yan kananan kabilu kimiyya. Bisa manufofi da aka tsara game da samar da kyawawan guraben aiki da na zaman yau da kullum, an sa kaimi ga 'yan kimiyya da fasaha don su ba da taimakonsu a wurare da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune. Wurare masu sukuni su ba da gudummuwar kimiyya da fasaha ga wadannan wurare, alal misali an dauki kwararru aiki bayan lokacin tashinsu daga aiki, an aika da 'yan kimiyya da fasaha zuwa wadannan wuraren don ba da lacca da yin aiki cikin wani gajeren lokaci, da yin hadin guiwarsu wajen samar da fasaha, da horar da 'yan kananan kabilu da sauransu. Yanzu, an riga an kafa dimbin cibiyoyin nazarin kimiyya da fasaha da suke da nasaba sosai da tattalin arzikin kasa da zaman rayuwar jama'a da halayen musamman na kananan kabilu a wurare da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune. Ta haka an riga an kafa cikakken tsarin nazarin kimiyya da suka shafi ayyukan ilmi dabam daban, kuma an sami masu fasaha da yawan gaske a wadannan wuraren.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan 'yan kimiyya da injiniyoyi da suka fito daga wuraren kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu na kasar Sin ya kai kimanin dubu 100. Yanzu, 'yan kimiyya da fasaha na kananan kabilu sun riga sun zama wani ginshiki ga bunkasa harkokin kimiyya da fasaha na kasar Sin. Daga cikinsu akwai wakilan cibiyar kimiyya ta kasar Sin, da wakilan cibiyar aikin injiniya ta kasar, da jagoran masu nazarin kimiyya, da kuma kwararru wadanda suka fi ba da babban taimako ga yadada kimiyya. Alal misali, Mista Wang Shiwen, wakili dan kabilar Hui na cibiyar kimiyya ta kasar Sin wanda ya dade yana aikin warkar da tsofaffi masu ciwon zuciya da ba su ceton gaggawa, kuma yana nazarin kimiya da aikin koyarwa, ya ba da babban taimakonsa wajen samar da wani sabon ilmi wato aikin likitanci na jiyyar tsofaffi. Miss Wei Yu, wakiliya 'yar kabilar Zhuang ta cibiyar aikin injiniya ta kasar Sin wadda ta taba samun digirin dokta na aikin masana'antu daga wata jami'ar koyon aikin masana'antu ta kasar Jamus, ta zama daya daga cikin jagoran da suka fara yin nazarin sabon ilmin abubuwa masu rai ta hanyar yin amfani da naura mai aiki da kwakwalwa. Madam Zheng Huiyu, 'yar kabilar Korea wadda ita shehun malama ce a fannin kimiyyar noma wadda ta dade tana nazari kan renon irin wake dabam daban, ta sami nasara wajen renon wani kyakkyawan iri na karamin wake mai lambar Jilin 20.

Aikin ba da ilmi ga 'yan kananan kabilu na kasar Sin

Aikin ba da ilmi ginshiki ne ga bunkasa harkokin kimiyya da na fasaha. Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai da manufofin musamman masu yawa don bunkasa aikin ba da ilmi ga 'yan kananan kabilu. A karkashin wadannan manufofi da matakai, ana ba da muhimmanci da taimako ga bunkasa aikin bai wa 'yan kananan kabilu ilmi, an kafa hukumomin musamman don kula da aikin ba da ilmi ta hanyar dimokuradiyya. An girmama wa iko da moriya da 'yan kananan kabilu ke da su wajen bunkasa aikin ba da ilmi cikin 'yanci a wuraren da suke zaune da yawa. An mai da hankali sosai ga koyar da harsunan kananan kabilu, yayin da ake koya musu Sinanci wato harshen Han. An kara kokari wajen wallafa littattafan koyarwa cikin harsunan kananan kabilu, kuma an kara kokari wajen horar da 'yan kananan kabilu don su zama malaman koyarwa. An ba da taimakon kudi musamman ga 'yan kananan kabilu da wurare da yawa suke zaune. Bisa halin da ake ciki a wuraren da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune, an shirya makarantun kananan kabilu iri dabam daban, an dauki 'yan kananan kabilu cikin wadannan makarantu don ba su ilmi, haka nan kuma an ba su taimako a fannin zaman rayuwarsu, ka zalika an nemi wurare masu sukuni da su ba da taimakonsu ga wurare da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune.

Gwamnatin Sin ta dauki tsauraran matakai masu yawa wajen bunkasa harkokin makarantu a wurare da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune, an yi amfani da duk abubuwa da ake da su wajen kafa makarantun firamare da na sakandare da kolejoji da jami'o'i ta hanyoyi dabam daban, kuma idan 'yan wata karamar kabila na magana da harshensu, to, sai a yi aikin koyarwa cikin harshensu a makaratun firamare da na sakandare na wannan karamar kabila. Ta haka yawan 'yan kananan kabilu wadanda ke karatu a makarantun iri dabam daban ya karu karuwar gaske. Haka zalika an kafa kolejoji da jami'o'i na kananan kabilu a wurare da suke da yawa a arewa maso yammacin kasar Sin, da arewa maso gabas da kuma kudu maso yammacin kasar, don horar da dalibai 'yan kananan kabilu dubu dubbai.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yanzu, akwai dalibai na kananan kabilu 55 na kasar Sin wadanda ke karatu a jami'o'i, sa'an nan kuma dalibai na wasu kananan kabilu na neman digiri na biyu da na daktar.

(Hoton Jami'ar Kabilu na Kasar Sin)

Al'adun kananan kabilu a kasar Sin

A jihohin kananan kabilu da yankunansu masu ikon aiwatar da harkokin kansu dabam daban, bi da bi aka kafa kungiyoyin mawallafa, da na 'yan wasan kwaikwayo, da na mawaka, da na raye-raye, da na masu zane-zane, da na ma'aikatan sinima, da na masu daukar hoto da dai sauransu bisa halin da ake ciki don cin gadon al'adun kananan kabilu da kuma yalwata su. Haka nan kuma bi da bi aka bude sassan koyon adabin kananan kabilu a jami'o'i da kolejojin kananan kabilu da ke a wuraren kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu da dama, sa'an nan an kafa makarantun koyon wasannin fasaha kamar kolejin koyon wake-wake da na wasan kwaikwayo da na koyon aikin sinima da sauransu a wasu daga cikin wadannan wurare, wadanda suka horar da dimbin kwararru 'yan kananan kabilu a fannin adabi da fasaha. Alal misali, ya zuwa yanzu, bi da bi aka kafa kolejin koyon likitancin Tibet, da na Mongoliya, da na Uygur, da makarantun koyon ilmin likitanci da na hada magunguna na kananan kabilu a jihar Tibet, da ta Mongoliya Ta Gida, da kuma ta Xinjiang don neman bunkasa harkokin likitanci na kananan kabilu.

Yanzu, an riga an sami mawallafa da 'yan wasannin fasaha na kananan kabilu masu dimbin yawa a kasar Sin, kamar Mista Lao She, mawallafi dan kabilar Man, da Kang Langying, mai tsara wakoki dan kabilar Dai, da Wu Baixin, mawallafi dan kabilar Hezhe da sauransu. Haka zalika bi da bi an kafa kungiyoyin 'yan kananan kabilu masu gabatar da wasannin fasaha a matsayin sana'a da kungiyoyinsu na bayan aiki, wadanda ke ta gabatar da wasanninsu a kauyuka da makiyayai da garuruwa da kuma sauran wurare da 'yan kananan kabilu da yawa ke zaune.

Bugu da kari kuma an wallafa littattafa da yawa dangane da bayanonin wasannin fasaha da bangaren adabi na kananan kabilu. Daga cikinsu, akwai manyan littattafan wasanin fasaha guda 10 kamar "Babban Littafin Wake-Wake Na Jama'ar Kasar Sin" , da "Babban Littafin Wake-Waken Wasannin Opera Na Kasar Sin ", da "Babban Littafin Kayayyakin Kide-Kide Na Jama'ar Kabilun Kasar Sin", da "Babban Littafin Wake-Waken Wasannin Gargajiya na Kasar Sin", da "Babban Littafin Raye-Raye Na Jama'ar Kabilun Kasar Sin", da "Tarihin Wasannin Kwikwayo na Kasar Sin", da " Babban Littafin Tatsuniyoyi Na Jama'ar Kasar Sin", da "Babban littafin Wakokin Yara Na Kasar Sin", da "Babban Littafin Karin Magana Na Kasar Sin", da kuma "Babban Littafin Wasannin Gargajiya Na Kasar Sin." Wadannan manyan littattafai sun hada da bayanoni masu dimbin yawa game da wasannin fasaha na kananan kabilu.

Ban da wadannan kuma an kara samun ci gaba wajen buga mujallolin adabi da wasannin fasaha na kananan kabilu. A halin yanzu, yawan irin wadannan majalloli ya wuce 100 a kasar Sin. Daga cikinsu akwai mujallolin wakoki, da na wake-wake da kide-kide, da na zane-zane, da na cinima da wasannin kwaikwayo da sauransu wadanda ake buga su a wurare dabam daban. Haka nan ana buga wasu mujallolin nan cikin harsunan kananan kabilu sama da 20. Ta haka yawan littattafai, da na jaridu da mujalloli da ake bugawa a wuraren kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu na kasar Siin ya karu karuwar gaske. Alal misali yawan ire-iren littattafai da ake bugawa cikin rubutun kananan kabilu ya wuce 3,400.

>>[Manyan bukukuwa]

Manyan bukukuwa na kananan kabilu a kasar Sin

Bukukuwa da kananan kabilun kasar Sin ke yi suna da yawan gaske. Kusan ko wace karamar kabila tana da nata babban bikinta, Alal misali, bikin sabuwar shekara ta kabilar Tibet bisa kalandarta, da bikin yayyafa ruwa na kabilar Dai, da bikin yula na kabilar Yi, da bikin titin watan Maris na kabilar Bai, da bikin wake-wake na kabilar Zhuang, da bikin nune-nune na Nadam na kabilar Mongoliya da sauransu. Haka nan kuma wasu hukumomin wuri-wuri sun kafa doka game da mayar da ranakun bukukuwan kananan kabilu da dama don su zama ranakun hutu, alal misali, ranar sabuwar shekara ta kalandar Tibet, da ranar babbar salla da sauransu.

Babbar Salla

Babbar Salla, sallar Ibada ce da Musulmi ke yi a duk shekara, wanda ake "kira Id-el kabir" a cikin Larabci, abin da ake nufi da "Ed-el" shi ne biki, haka kuma "Kabir" yana nufin babba mafi muihimmanci. Babbar salla salla ce ga 'yan kabilar Hui, da ta Uygur, da Hazak, da Uzbek, da Tajik, da Tatar, da Kurkez, da Sala, da Dongxiang, da ta Baoan da sauransu wadanda ke bin addinin musulunci. Ran 10 ga watan Zulhajji ranar Babbar Salla ce ta kalandar Hijira. Musulmi su kan tsabtace gidajensu sosai a gabannin ranar Babbar Salla, suna yin kek, da Fanke, da cincin da sauran irinsu dabam daban. A wannan rana da asuba, Musulmi su kan yi alwala, su ci ado, su je masallatai don saurarar huduba da limamai kan yi musu. Haka nan ko wane iyalin musulmi ya kan yanka rago ko rakumi ko shanu don yin sadaka da rarraba wa dangi da aminai, da kuma karbar baki. Musulmi su kan ci naman rago, da kek, da fanke, da cincin da dai sauran irinsu, da kuma 'ya'yan itatuwa da kankana da kuma sauransu, suna yin hira cikin aminci. A lokacin da 'yan kabilar Uygur da ke zaune a jihar Xinjiang ta kasar Sin ke murnar ranar Babbar Salla, su kan shirya babban taron wake-wake da raya-raye. Haka nan 'yan kabilar Hazak, da ta Kurkez, da Tajik, da Uzbek da sauransu su ma su kan shirya gasar kamun rago, da ta tsaren doki, da kokawa a lokacin da suke murnar Babbar Salla.

(Babbar Salla)

Karamar Salla

Karamar Salla wadda ake kira "Ed Alfitir" cikin Larbaci. Karamar Salla ma salla ce ga 'yan kabilar Hui, da ta Uygur, da Hazak, da Uzbek, da Tajik, da Tatar, da Kurkez, da Sala, da Tongxiang, da ta Baoan da sauransu. A kan yi murnar ranar Karamar Salla a ran 1 ga watan Shauwal na Kalandar Hijira. Watan Ramadan na ko wace shekara ta Kalandar Hijira Watan Azumi ne. A kan yi azumi har kwanaki 29 ko 30. A lokacin azumi, Musulmi su kan gama cin abincinsu kafin alfijiri ya fito. Bayan fitowar alfijiri , ba za su ci abinci ko sha ruwa ba ko da kuwa suna jin yunwa ko kishirwa, wadanda su kan sha taba ma ba su sha. Ban da wadannan kuma, an nemi Musulmi da su kaurace wa jima'i, su yi hakuri da duk kwadayinsu, kuma su daina yin tunani da aiki maras kyau a watan Azumi don nuna imaninsu ga Allah. Amma yara da tsofaffi da gajiyayyu an dauke musu yin Azumi, haka nan mata da ke yin al'ada ma an dauke musu, amma za su iya cin abinci yadda suke so, kuma bai kamata su ci abinci ko shan ruwa a idon jama'a ba. Wadanda suka kamu da cututtuka ko matafiya su ma an iya dauke musu yin Azumi, amma ya zama tilas su rama bayan watan Azumi. Idan wani bai iya ramuwa ba, sai ya ba da kudi ko dukiya a matsayin kaffara ga musakai, ko ya yi azumin kwana sittin a jere, wato tilas ya ciyar da miskinai 60 har na kwana 60 a jere. In dare ya yi, wato a lokacin da za a sha ruwa, a kan yi kiran salla a masallatai, daga nan Musulmi suna iya fara cin abinci. Har ma idan wani bako matafiyi da ke yin azumi, ya shigo gari, to, zai iya shiga cikin wani gidan Musulmi da ba a san shi ba, mai gidan nan zai tarye shi da hannu bibbiyu.

A kan shirya kasaitaccen biki don murnar ranar Karamar Salla. Kafin ranar karamar Salla, Musulmi su kan shafa wa gidajensu fenti, su tsabtace farfajiya sosai, su yi aski, kuma su yi wanka da sauransu. Ango da amarya su kan yi bikin daurin aure a lokacin Karamar Salla.

Sabuwar shekara ta Kalandar Tibet

Ranar sabuwar shekara ta Kalandar Tibet rana ce ta biki mai matukar muhimmanci ga 'yan kabilar Tibet. 'Yan kabilar Tibet su kan shafe kwanaki 15 wato tun daga ran 1 har zuwa ran 15 ga watan Janairu na Kalandar Tibet suna gudanar da harkokin wannan bikin. A ranar sabuwar shekara, da gari ya waye, sai samari da 'yan mata da suke rangada ado su kan taya wa juna murnar sabuwar shekara, kuma su yi wa juna fatan zaman alheri. 'Yan kabilar Tibet wadanda suka yi ado su kan shiga cikin dakunan Ibada da ke daura da wurare da suke zaune don yin addu'a, ko su runtuma zuwa tituna don yin wake-wake da raye-raye, amma ba za su iya bakuntar iyalan danginsu ko na aminansu ba.

(Hoton Sabuwar shekara ta Kalandar Tibet)

Bikin Nune-Nune Na Nadam

Bikin Nune-Nune Na Nadam bikin gargajiya ne da 'yan kabilar Mongoliya da ke zaune a Jihar Mongoliya ta Gida, da Jihar Xinjiang, da Lardin Gansu, da kuma Lardin Qinghai su kan shirya sau daya a ko wace shekara. 'Yan kabilar Mongoliya su kan shirya wannan bikin ne a watan Yuli da watan Augusta na yanayin kaka, wato lokacin da aka sami haki mai kyau kuma mai lafiya a makiyayansu, kuma dabbobi da suke kiwo sun yi kiwo, kuma yanayi ya yi kyau kwarai. Abin da ake nufi da "Nadam" cikin harshen Mongoliya shi ne "nishadi" ko "wasanni". 'Yan kabilar Mongoliya sun dade suna yin wannan biki shekara da shekaru. A zamanin da, a kan yi bukukuwa bisa babban mataki a lokacin da ake yin Bikin Nune-Nunen Nadam, limamai suna kunna turare da fitilu, su karanta addu'o'in addinin Buddah, don neman Allah ya kiyaye su daga masifa. Yanzu, manyan harkoki da a kan gudanar a gun wannan bikin sun hada da wasan kokawa, da tseren dawaki, da wasan harba kibau da sauran wasannin gargajiyar 'yan kabilar Mongoliya, har ma a wurarensu da dama a kan yi gasar guje-guje da tsalle-tsalle, da wasan jaye-jaye na igiya, da wasan kwallon raga, da wasan kwallon kwando da sauran wasannin motsa jiki.

■ Addinai

>>[Halin addinai]

Halin addinai na kasar Sin

Kasar Sin kasa ce mai addinai da yawa. Manyan addinai da a ke bi a kasar Sin sun hada da addinin Buddah, da addinin Dao, da addinin Musulunci, da addinin Kirista da kuma na darikar Katolika.

Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, a halin yanzu, yawan mutane da ke bin addinai ya kai fiye da miliyan 100 a kasar Sin, gidajen Ibadansu sun wuce dubu 85, haka nan kuma limamansu da ma'aikatansu sun kai kimanin dubu 300, kungiyoyinsu kuwa sun kai fiye da 3,000, ka zalika yawan kolejojinsu da makarantunsu na koyon harkokin addinai ya kai 74.

Daga cikin kungiyoyin mabiyan addinai na duk kasar Sin, akwai Kungiyar 'Yan Addinin Buddah Ta Kasar Sin, da Kungiyar 'Yan Addinin Dao Ta Kasar Sin, da Kungiyar Musulmi Ta Kasar Sin, da Kungiyar 'Yan Darikar Katolika Masu Kishin Kasa Ta Sin, da Kungiyar Limaman Darikar Katolika ta Kasar Sin, da Kwamitin 'Yan Addinin Kirista Masu Kishin Kasa ta Kasar Sin, da Kungiyar "yan Addinin Kirista Ta Kasar Sin da kuma dai sauransu. Bisa tsarin ka'idojinsu, kungiyoyin mabiyan addinai dabam daban su ne ke zaban shugabanninsu da kungiyoyin shugabancinsu, kuma suna gudanar da harkokin addinansu cikin 'yanci, haka zalika suna kafa kolejoji da makarantun koyon harkokin addinai don biya wa mabiyan addinai bukatunsu, suna wallafa littattafan addinai, su buga mujallolin addinai, kuma su yi harkokin hidima domin jama'a.

Manyan addinai na kasar Sin

Addinin Buddah

An kawo addinin Buddah a kasar Sin ne a misalin karni na 1. Bayan da aka shiga karni na 4, an yadada addinin Buddah sosai a ko ina cikin kasar Sin, kuma sannu a hankali ya zama addini mafi girma a kasar Sin. Addinin Buddah na kasar Sin ya kasu cikin darikokin harsuna uku wadanda suka hada da addinin Buddah na darikar harshen Han, da addinin Buddah na darikar harshen Tibet, da kuma addinin Buddah na darikar harshen Bali (ko addinin Buddah na darikar Kudu). Yawan limamai da ke zama a cikin dakunan Ibada na wadannan darikokin harsunan uku ya kai dubu 200. A halin yanzu, akwai dakunan Ibada na addinin Buddah sama da dubu 13 wadanda kofofinsu a bude suke a kasar Sin, tare da kolejoji da makarantun koyon addinin Buddah wadanda yawansu ya kai 33, da kuma mujallolin addinin Buddah iri dabam daban har misalin 50 da ake bugawa a kasar Sin.

Addinin Buddah na darikar Tibet yana daya daga cikin darikokin addinin Buddah na kasar Sin. An fi yadada shi a Jihar Tibet Mai Ikon Aiwatar Da Harkokin Kanta, da Jihar Mongoliya Ta Gida Mai Ikon Aiwatar Da Harkokin Kanta, da Lardin Qinghai da sauran wurare. Yawancin 'yan kabilar Tibet, da ta Mongoliya, da ta Yugu, da ta Menba, da ta Luoba, da ta Tu suna bin addin Buddah, yawansu kuma ya wuce miliyan 7. Haka nan kuma ana bin addinin Buddah na darikar Kudu ne musamman a yankin Xishuangbanna ta kabilar Dai mai ikon aiwatar da harkokin kanta, da yankin Dehong ta kabilar Dai da ta Jingpo mai ikon aiwatar da harkokin kanta, da yankin Simao da dai sauran wurare na lardin Yunnan da ke a kudu maso yammacin kasar Sin, haka nan kuma yawancin 'yan kabilar Dai, da ta Bulang, da ta Achang, da ta Wa suna bin addinin Buddah na darikar Kudu, wadandan yawansu ya wuce miliyan 1 a yanzu. Mabiyan addinin Buddah na darikar Han yawancinsu 'yan kabilar Han ne, kuma suna zaune a wurare dabam daban na kasar Sin.

(Hoton shahararen gidan Ibada na addinin Buddah mai suna Shaolin na kasar Sin)

Addinin Dao

Addinin Dao addini ne na asalin kasar Sin, an fara same shi ne a karni na 2, wato yau sama da shekaru 1,800 ke nan. Addinin Dao ya gaji al'adar gargajiya ta kasar Sin wato nuna girmamawa ga halitta da kakani-kakani, ya taba samun darikoki da dama a cikin tarihi, amma wadanda a sannu da hankali suka zama manyan darikoki biyu kamar darikar Quanzhendao da darikar Zhengyidao. Addinin Dao ya kawo tasirinsa ga kabilar Han a wasu fannoni. Da kyar ake samun mutane da ke bin addinin Dao, dalilin da ya sa haka shi ne domin addinin Dao ba shi da wani shirin ka'in da na'in na bikin zaman mabiyansa, kuma ba ta da ka'idoji masu tsanani. A halin yanzu, yawan dakunan Ibada na addinin Dao ya wuce 1,500 a kasar Sin, limamai maza da mata wadanda ke zama a cikin wadannan dakunan Ibada sun kai fiye da dubu 25.

(Hoton Dutsen Qingshan na lardin Sichuan, Wurin mai tsarki na addinin Dao)

Addinin Musulunci

A karni na 7 ne, aka kawo addinin Musulunci a kasar Sin. 'Yan kananan kabilu wato kabilar Hui, da ta Uygur, da Tatar, da Kurkez, da Hazak, da Uzbek, da Dongxiang, da Sala, da kuma Baoan wadanda yawansu ya wuce miliyan 18, yawancinsu musulmi ne. Yawancin Musulmi na kasar Sin kuwa suna zaune ne a jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kanta, da Jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon aiwatar da harkokin kanta, da lardin Gansu, da lardin Qinghai da lardin Yunnan, sauransu kadan suna zama a sauran larduna da birane na kasar. Haka nan kuma a kasar Sin, akwai masallatai da yawansu ya kai fiye da 30,000, tare da limamai sama da 40,000.

(Hoton Masallaci mai suna Tongxin na jihar Ningxia)

Darikar Katolika

Tun daga karni na 7, an sha kawo darikar Katolika a kasar Sin, an kuma yadada shi sosai a kasar Sin ne, bayan da aka yi Yakin Tabar Wiwi a shekarar 1840. A halin yanzu, jam'iyyar Darikar Katolika Ta kasar Sin tana da shiyyoyinta 100, mabiyan darikar Katolika kuwa sun kai kimanin miliyan 5, haka zalika akwai majami'un darikar Katolika da sauran dakunan Ibadanta wadanda yanzu kofofinsu a bude suke kuma yawansu ya kai kimanin 5,000, da kuma kolejojin koyon darikar Katolika 12 a kasar Sin. A cikin shekarun nan 20 ko fiye da suka wuce, Jam'iyyar Darikar Katolika Ta Kasar Sin ta horar da limamanta samari fiye da 1,500. Daga cikinsu akwai samari limamai dari da wani abu sun sami damar yin karatu a kasashen waje don kara zurfafa ilminsu. Ban da wadannan kuma wannan jam'iyyar tana da sabbin 'yan mata sista 3,000, da mata sista sama da 200 wadanda suka dau niyyar bin darikar nan har duk rayuwarsu. A ko wace shekara yawan mabiyan darikar Katolika na kasar Sin da a kan yi musu Baftizma (Baptism) ya wuce 50,000, haka kuma an riga an buga littattafan "Darikar Katolika" (The Holy Bible) wandanda yawansu ya wuce miliyan 3.

(Hoton Majam'ar Addinin Katolika a bakin hanyar Wangfujing ta birnin Beijing)

Addinin Kirista

A farkon karni na 19, an kawo addinin Kirista a kasar Sin, an yadada shi sosai bayan Yakin Tabar Wiwi. A shekarar 1950, addinin Kirista ya yi kira ga mabiyansa da su kawar da tasiri da mayaudara suka yi musu, su horar da su wajen nuna kishin kasa, kuma su yi kokari don tabbatar da aiwatar da harkokinsu su da kansu, da talaffinsu da kuma yadada addininsu su da kansu. Yanzu, yawan 'yan addinin Kirista ya kai kimanin miliyan 10 a kasar Sin, kuma akwai limamansu da kuma 'yan mishansu sama da 18,000, da majami'unsu 12,000 da wani abu, da kuma kananan dakunan Ibada da yawansu ya wuce 25,000.

>>[Musaye-musaye da Manufofin Addinai]

Manufofin kasar Sin dangane da harkokin addinai

Bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, gwamnatin kasar ta tsara manufofin 'yancin bin addinai, kuma ta aiwatar da su, ta haka huldar da aka kafa a tsakanin gwamnatin da bangaren addinai ya dace da halin da ake ciki a kasar. 'Yan kasar Sin suna da 'yancin bin addinansu, da na bayyana imaninsu da kuma addinai da suke bi. Duk addinai suna kan matsayi na daidaici, suna zama tare cikin jituwa, kuma ba su taba yin rikici a tsakaninsu ba, duk 'yan kasa da ke bin addinai da wadanda ba su bin addinai su ma suna girmamawa juna, suna hadin kansu, kuma suna zaman jituwa a tsakaninsu.

A karkashin tsarin mulki na Jamhuriyar Jama'ar Sin, an ce, "duk 'yan kasar Sin na da 'yancin bin addininsu." "An haramta duk ma'aikatun gwamnati da kungiyoyin jama'a da mutane su tilasta wa 'yan kasa da su bi addini ko kin bin addini, an kuma haramta a nuna bambanci ga 'yan kasa da ke bin addini ko ba su bin addini." "Hukumomin kasa suna kare mabiya addinai domin su gudanar da harkokin addinansu yadda ya kamata." Haka zalika an ce, "an haramta tada zaune tsaye da lahanta lafiyar jikin 'yan kasa, ko kawo cikas ga tsarin ba da ilmi na kasa ta hanyar yin amfani da addinai." Kana kuma "an haramta wa kungiyoyin addinai karbar umurni daga kasashen waje, kuma an haramta wa 'mabiya addinai su bi umurni daga kasashen waje wajen gudanar da harkokin addinansu."

Dadin dadawa, bisa abubuwa da aka tanada a cikin "dokar wuraren kananan kabilu masu ikon aiwatar da harkokin kansu", da "manyan dokokin jama'a", da "dokar ba da ilmi", da "dokar aiki", da "dokar ba da ilmin tilas", da "dokar zaben majalisun wakilan jama'a", da "dokar kannan hukumomi na kauyuka", da "dokar tallace-tallace" da dai sauransu, an ce, duk masu bin addinai suna da ikon zabe da kuma cin zabe; an kare dukiyoyin halal na kungiyoyin addinai, an ware aikin ba da ilmi daga harkokin addinai, duk 'yan kasa wadanda ke bin addinai dabam daban suna da ikon samun ilmi cikin daidaici. Kamata ya yi, jama'ar kabilu dabam daban su girmama juna da harshensu da rubutu, da dabi'u da addinansu. Haka nan kuma an haramta a nuna bambanci ga 'yan kasa da ke bin addinai dabam daban, yayin da suke neman aikin yi, ka zalika an haramta a nuna bambanci ga kabilu da addinai, yayin da ake yin tallace-tallace, ko buga tambura a jikin kayayyaki.

A watan Janairu na shekarar 1994, gwamnatin kasar Sin ta bayar da "dokokin kula da harkokin wuraren Ibada na addinai dabam daban", don kare ikonsu da moriyarsu ta halal. A watan Febrairu na wannan shekarar, gwamnatin kasar Sin ta kuma bayar da "dokar kula da harkokin addini da baki daga kasashen waje ke yi a Jamhuriyar Jama'ar Sin", don girmama 'yancin bin addinai da baki daga kasashen waje ke yi a kasar Sin, da kare ma'amalar aminci da musaye-musayen al'adu da ilmi da ake yi a tsakaninsu da bangaren addinai na kasar Sin a fannin addinai.

Ban da wadannan kuma a karkashin dokokin kasar Sin da abin ya shafa, an kare limamai da ma'aikatan addinai daga wajen gudanar da harkokin koyarwa yadda ya kamata, an kare duk harkokin addinai da ake yi a wuraren Ibada da gidan mabiyan addinai bisa al'adarsu yadda ya kamata, haka zalika an kare kungiyoyin addinai da mabiyansu bisa dokokin shari'a wajen gudanar da harkokin addinansu kamar yin addu'a a gaban gumakan addinai, da karanta littattafan addinai, da yin salla, da addu'a, da huduba, da holimas (Mass), da baftizma, da azumi, da shigar da wani don ya zama limamin addinin Buddah, da yin bukukuwan addinai da dai sauransu, kuma su da kansu su yi harkokinsu, sa'an nan kuma an haramta yi musu shisshigi.

Daidai kamar yadda ake yi a kasashe dabam daban, kasar Sin ita ma tana aiwatar da ka'idar ware aikin ba da ilmi daga harkokin addinai. Yayin da ake ba da ilmi ga 'yan kasa, ba a koyar wa 'yan makaranta ilmin addinai. Amma ana koyar da ilmin addinai da yin nazarinsu a wasu kolejoji da jami'o'i da kuma cibiyoyin nazarin ilmi. A cikin kolejoji da makarantu da kungiyoyin addinai dabam daban suka kafa, ana koyar da ilmin addinai musamman domin biya wa addinai dabam daban bukatunsu.

A cikin yalwatuwar dogon tarihi, al'adun addinai dabam daban na kasar Sin sun riga sun zama daya daga cikin al'adun gargajiya na kasar Sin. Duk addinai sun gabatar da cewa, a bauta wa zamantakewar al'umma, a kawo wa jama'a alheri. Alal misali, addinin Buddah yana kira da "a yi kishin kasa, da nuna kauna ga juna", addinin Kirista da darikar Katolika suna kira da " a taimaki juna", addinin Dao na kira da " a nuna wa juna kauna, a ba da taimako ga saura", addinin Musulunci kuma yana kira da " a bauta wa Allah, sannan a tabbatar da zaman lafiya da daidaici a tsakanin al'umma".

Musaye-musaye tsakanin mabiyan addinai na Sin da kasashen waje

An kawo addinin Buddah, da addinin Musulunci, da addinin Kirista da kuma darikar Katolika a kasar Sin daga kasashen waje. Duk wadannan addinai ne ga duk duniya, kuma suna kan matsayi mai matukar muhimmanci a duniya, suna da mabiyansu masu dimbin yawa a kasashe da shiyyoyi da yawa, daga ciki kasashe da dama sun dauke su a matsayin addinin kasa.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, an yi ta samun ci gaba wajen yin musaye-musaye a tsakanin bangarorin addinan kasar Sin da na kasashen waje. Addinai dabam daban na kasar Sin suna yin musaye-musaye a tsakaninsu da takwarorinsu a fannoni da yawa. Alal misali, bangaren addinin Buddah ya kan yi musaye-musaye tsakanin mabiyansa da na kasar Thailand, da Korea ta Kudu, da Japan, da Myanmar, da Sri Lanka, da Vietnam da kuma sauran kasashe da ke makwabtaka da kasar Sin ta hanyoyi dabam daban. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta taba nuna kayayyakin tarihi da ta samu bayan da aka kona gawawwakin limaman Buddah a kasar Thailand, da Myanmar da kuma Sri Lanka don mabiyan addinin Buddah su nuna girmamawa da yin addu'a ga wadannan kayayyakin tarihin. Haka nan kuma bangaren addini na kasar Thailand da bangaren addini na jihar Tibet ta kasar Sin sun kafa tsarin musaye-musayen ilmin addinin Buddah a tsakaninsu cikin lokaci-lokaci.

Ban da wadannan, bisa gayyatar da wasu kasashen yammacin Turai da na arewacin nahiyar Amurka suka yi musu ne, kungiyoyin manyan addinai dabam daban na kasar Sin sun sha yi ziyarce-ziyarce a wadannan kasashe, ta haka ba ma kawai sun kara fahimtar addinan wadannan kasashen ba, hatta ma sun kara fadakar da jama'ar kasashen nan abubuwa game da addinan kasar Sin.

(Hoton kayayyakin tarihi wadanda aka samu bayan da aka kona gawawwakin limaman Buddah wadanda kuma aka nuna a Hong Kong)

© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China