Rahoto kan albarkatan yawon shakatawa
Kasar Sin tana da fadi ainun, da kyawawan duwatsu da koguna, da dauwamammun al'adu, da dimbin kabilu masu shan bambancin dabi'ar gargajiya, da kayayyakin dake da sigar musamman ta kasar da kuma dabarun dafa abinci masu dadi,wadanda suka shahara ko a gida ko a waje; Ban da wannan kuma, kasar Sin tana da albarkatan yawon shakatawa masu yawan gaske,wadanda kuma suke da boyayyen karfi da kuma kyakkyawar makoma a nan gaba. Tare da bunkasuwar tattalin arziki da kuma kara yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da ake yi a kasar Sin, sana'ar yawon shakatawa ta rigaya ta zama irin sabon ginshikin yalwata tattalin arzikin kasar. Yanzu, ana yi ta habaka yawan wuraren yawon shakatawa ko'ina a kasar Sin yayin da ake dinga kyautata manyan ayyuka. Sakamakon haka, yawan baki da sukan zo nan kasar Sin domin yin yawon shakatawa sai kara karuwa yake a kowace shekara.
Ya kasance da ire-iren albarkatan yawon shakatawa masu yawan gaske. Ga fadamar Ai Tin dake wurin Turufan na jihar Xin Jiang, tana kasa da leburin teku da mita 155; Ga manyan duwatsu na Himalaya. Manyan duwatsu na Himalaya sun hada da manyan duwatsu a jere, suna zaune a kan iyakar kasa dake tsakanin kasashen Sin, da Indiya da kuma Nepal da dai sauran kasashe. Tsawonsu ya kai kilomita dubu biyu da dari hudu ko fiye; kuma matsakaicin tsawonsu ya fi mita dubu shida kan leburin teku, wato su ne duwatsu mafiya tsayi a duniya. Babban dutse mafi tsayi shi ne tsaunin Zhumolangma, wato babban tsauni mafi tsayi a duniya wanda ake kira Everest da Turanci, wato yawan tsayinsa daga laburin teku ya kai mita 8848.13; Abun da ya fi ba mutane sha'awa, shi ne yawan ratar tsayin dake tsakanin wannan fadama ta Ai Tin da kololuwar tsaununa ta Jumolanma ya kai mita 9,003. Lallai wannan ba safai akan ga irinsa ba a duk duniya;
Kasar Sin tana daya daga cikin wuraren haifar da wayin kai na duniya, wato ke nan tana da tarihi mai haske da kuma kyawawan al'adu, da kuma wurare ko kayayyakin tarihi, wadanda kuma suka zama albarkatan yawon shakatawa masu daraja. Alal misali: an gano tsofaffin wurare 29 na can zamanin da a cikin larduna 34 tun bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekara ta 1949.
A cikin shahararrun wurare da kayayyaki masu yawan gaske na kasar Sin, gumakan dawaki da kuma dawakin motocin tagulla dake cikin kabarin masu yawan gaske na kasar Sin, gumakan dawaki da kuma dawakin motocin tagulla dake cikin kabarin Sarki Ying Zheng na daular Qin suka fi janyo hankulan mutane masu yawon shakatawa da yawansu ya kai miliyan daya a kowace shekara; Ban da wannan kuma, zane-zane kan bango na Fafakar Mo Gao dake birnin Dunhuang sun zama tamkar ma'adana mai daraja ta fasaha a duniya; Bugu da kari kuma, shahararriyar babbar ganuwa, wani wuri ne da kowane mutum ke kishin zuwa; Dadin dadawa, kasar Sin tana da kabilu 56, wadanda kowanensu yana da nasa tarihi da al'adu da kuma dabi'ar gargajiya dake da halayen musamman .
Babban take na yawon shakatawa
Domin kara yin farfaganda ga baki masu yawon shakatawa da kyau da kuma bayyana albarkatan yawon shakatawa na kasar Sin, tun daga shekara ta 1992, hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ta kan fito da shirye-shiryen yawon shakatawa, wadanda suke da halayen musamman iri daban daban, da tayar da harkokin yawon shakatawa a jere, da gwada kyawawan hanyoyi da kuma wuraren yawon shakatawa da kuma aiwatar da manufar sa kaimi ga baki daga kasashen waje,wadanda sukan zo nan domin yin yawon shakatawa. Babban take na yawon shakatawa na kasar Sin a wannan shekara, shi ne ' Yawon shakatawa na zaman yau da kullum na farar hula'.
Al'ummar kasar Sin tana da tarihin wayin kai mai dorewa da ya kai shekaru 5,000; A duk tsawon lokacin, an yi tallafin Sinawa masu kirki wadanda sukan nuna bajinta da kuma kwazo da himma wajen aiki, wadanda kuma suke da salo irin na musamman na zaman rayuwa, da girke-girken gargajiya, da kuma dabi' u da al'ada na musamman. Lallai irin wannan zaman rayuwar Sinawa dake da halin musamman mai ban sha'awa ya riga ya zama wani muhimmin kashi dake cikin al'adun kasar Sin; haka kuma ya zama albarkatan yawon shakatawa dake da kyakkyawar darajar zamantewar al'umma.
Zaman rayuwar Sinawa na da halin musamman na Gabashin duniya ko a fannin gidajen kwana da cin abinci da sanya tufafi ko a fannin nishadi, da bukukuwa da kuma dabi'ar gargajiya. An tabbatar da babban take na yawon shakatawa na farar hula ne domin a bar baki daga kasashen waje su shiga cikin zamantakewar al'umma, da aikake-aikacen da ake yi a kasar Sin don more zaman jin dadi dake da halin musamman na Sinawa da kuma yin koyi da kyawawan al'adu da Sinawa suka kago.
Muhimmman harkokin yawon shakatawa da hukumar
yawon shakatawa ta kasar Sin ta yi a ' yan shekarun baya:
1992 Shekarar yawon shakatawa ta
sada zumunta 2000 Yawon shakatawa na sabon karni a shekara ta 2000
1993 Yawon shakatawa a kyawawan
tsaunuka da koguna na kasar Sin 2001 Yawon shakatawa na yin wasannin motsa jiki na 2001 a kasar Sin
1994 Yawon shakatawa a wuraren
tarihi na kasar Sin 2002 Yawon shakatawa na duba fasahohin jama'a na kasar Sin
1995 Yawon shakatawa na duba halin al'ada na jama'a da kuma abubuwan
gargajiya na wassu wurare na kasar Sin 2003 Yawon shakatawa a ' Daular girke-girke ta kasar Sin
1996 Yawon shakatawa na lokacin hutu 2004 Yawon shakatawa na rayuwar kabilun kasar Sin
1997 Shekarar yawon shakatawa ta kasar Sin
1999 Yawon shakatawa na duba muhallin hallitu a shekarar 1999
>>[Kyakyawar Kasar Sin]
Kyawawan wurare masu ni'ima na kasar Sin
Kasar Sin wata kasa ce mai yawan albarkatan yawon shakatawa dake da manyan koguna da tsaunuka, da dabbobi da tsire-tsire iri daban daban, da dimbin tsofaffin kayayyaki da wurare na tarihi. Yanzu, kungiyar NESCO ta majalisar dinkin duniya ta riga ta rubuta sunayen wuraren tarihi guda 29 na kasar Sin cikin ' Littafin sunayen wuraren tarihi na duniya' ; Daga cikinsu, akwai wurare guda 3 na hallita, da wurare guda 21 na al'adu da kuma sauran wuraren makamantansu guda 4; Lallai wadannan wuraren tarihi sun shaida hali na-gari na Sinawa.
Shahararrun halitattun wurare na kasar Sin
Ya kasance da albarkatun hallita masu yawan gaske a kasar Sin. Ban da wuraren tarihi na hallita na duniya kamar Jiu Zhai Gou, da Zhang Jia Jie da kuma Huang Long, kuma akwai kyawawan wurare masu ni'ima da yawa a kasar Sin, kamar Guilin dake kudu maso yammacin kasar, da Chang Bai Shan dake arewa maso gabashin kasar, da tsaunin Si Gu Niang na lardin Guizhou, da Xi Shuan Ban Na na lardin Yunnan da kuma tsibirin Ye Dao na lardin Hainan da dai sauran wurare, wadanda lallai suka cancanci mutane da su yi yawon shakatawa a can.
Guilin
Birnin Guilin yana jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda kuma ba zafi kuma ba sanyi, kuma ana iya ganin launin kore shar ko'ina a wurin. Bisa binciken labarin kasa da aka yi, an ce, yau da shekaru kimanin miliyan 300 da suka gabata, wurin Guilin wani babban teku ne.
Guilin, wani tsohon gari ne dake da tsawon tarihi na shekaru 2110, wanda kuma yake da dauwamammun al'adu; Yanzu, ya kasance da muhimman wuraren tarihi 109 a matsayin gwamnatin kasa, da jiha mai cin gashin kai da kuma na birni.
Yansu, ya kasance da manyan hotel-hotel 28 da kuma ofisoshin shirya tafiye-tafiye 18 a birnin Guilin, inda kuma akwai tafintoci da kuma masu ba da jagora ga yawon shakatawa da yawansu ya wuce 1,000 da suke aiki a tsanake; Kazalika, akwai hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama fiye da 40 na birnin, wadanda suka hada manyan birane na cikin gida da na kasahen waje.
Tsaunin Chang Bai Shan
Tsaunin Chang Bai Shan yana a lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin, kuma tsauni ne kan bakin iyakar kasashen Sin da Korea ta Arewa. Ga bishiyoyi masu launin kore-shar ba iyaka; Ga dabbobin daji masu daraja suna nan iri dabam daban dake bisa bishiyoyin. Tuni a shekara ta 1980, an dora tsaunin Chang Bai cikin shiyyoyin kare dabbobin daji na duniya na M.D.D ;
Tsaunin Chang Bai, babban tsauni ne na farko na arewa maso gabashin kasar Sin. A da, tsaunin Chang Bai, asalin ' yan kabilar Man ne. Mutane sukan samu saukin zirga-zirga wajen yawon shakatawa a tsaunin Chang Bai.
Shahararrun biranen yawon shakatawa na kasar Sin
Kasar Sin tana da fadi ainun,da kabilu da yawa, wadda kuma take da dimbin birane dake da halayen musamman iri daban daban, alal misali: a arewacin kasar Sin, akwai birnin Beijng, wato fadar mulkin kasar; a gabashin kasar Sin, akwai birnin Shanghai, wato cibiyar tattalin arziki ce ta kasar; a yammacin kasar Sin, akwai kyakkyawan birnin Lahsa dake da halin musamman na kabilar; a kudancin kasar Sin, akwai birnin Kunming dake da yanayi mai kyau a duk shekara, wadanda kuma suka zama tamkar lu'u-lu'u masu haske da aka lallafta a kan duk fadin kasar Sin da yawansu ya kai muraba'in kilo-mita miliyan tara da dubu dari shida.
Kasar Sin tana da kyawawan biranen yawon shakatawa 137, ciki har da birnin Shanghai, da birnin Beijing, da birnin Tianjin, da birnin Chongqing, da birnin Shenzheng, da birnin Hangzhou, da birnin Dalian, da birnin Nanjing, da birnin Shamen, da birnin Guangzhou, da birnin Chengdu, da birnin Shenyang, da birnin Qingdao, da birnin Ningbo, da birnin Xian, da birnin Harbin, da birnin Jinan, da birnin Changchun, da kuma birnin Lhasa da dai sauransu. Ban da wannan kuma, an zabi birnin Harbin, da birnin Jilin, da birnin Zhenzhou, da birnin Zhaoqing, da birnin Liuzhou da kuma birnin Qingdao don su zama shahararrun birane guda 10 na al'adun tarihi.
Beijing
Birnin Beijing, babban birnin kasar Sin ne, Kuma cibiyar siyasa da tattalin arziki ce ta kasar Sin.
Birnin Beijing na da tarihi mai dorewa. Tun can da a shekara ta 770 zuwa shekara ta 221 kafin haihuwar Annabi Isa aleihisalam, birnin Beijing ya riga ya zama fadar mulkin wassu kananan kasashe. Birnin Beijing ya zama hedkwatar kasa ce a daular Jing ; Daga baya, daular Yuan, da daular Ming da kuma daular Qing dukkansu sun kafa hedkwatarsu a nan Beijing, inda sarakuna 34 suka taba ba da umurni da yin babakere a harkokin gwamnatin kasa.
Bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekara ta 1944 musamman ma a cikin shekaru fiye da 20 bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, birnin Beijing ya yi manyan sauye-sauye. Ga manyan gine-gine masu benaye barjak ; kuma ana ta yin musanye-musanye tare da kasashen waje ; Birnin Beijing ya fi daukar hankulan miliyoyin masu yawon shakatawa na gida da na kasashen waje a kowace shekara.
Yanzu ya kasance da wassu shahararrun kayayyaki da wurare na tarihi masu ban sha'awa na kasar Sin a nan Beijing, wato su ne Dakin Ibada na Tiantan, da Lambun shan iska na Yi He Yuan, da Dakin tekuna na Beijing, da Babbar Ganuwa, da Lambun shan iska na Beihai da Jingshan, da Lambun shan iska na Al'ummar Kasar Sin, da Dakin kimiyya da fasaha ta kasar Sin, da Gidan dabbobi na Beijing da kuma Lambun shan iska na tsire-tsire na Beijing.
Xi'an
Birnin Xi'an, zauren lardin Shanxi na kasar Sin ne, wanda yake a arewa maso yammacin kasar, wanda kuma ya zama tamkar cibiyar siyasa, da tattalin arziki da kuma zirga-zirga na shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin da kuma wassu larduna maras mafita ta teku na kasar.
Daga cikin manyan tsofaffin birane guda shida wato birnin Xian, da birnin Luoyang, da birnin Nanjing, da birnin Kaifeng, da birnin Hangzhou da kuma birin Beijing na kasar Sin, birnin Xian ya fi su dadewa a tarihi a fannin kafa dauloli mafiya yawa tun tuni kuma cikin lokaci mafi tsawo. Saboda haka, wannan tsohon birnin Xian na tsawon shekaru dubu ya ba da babban tasiri a cikin tarihin kasar Sin.
Birnin Xian, wani shahararren wurin yawon shakatawa ne na kasar Sin. Dakin nuna gumakan dawaki na Sarki Yin Zheng na Daular Qing, wanda ake kiransa ' Babban abun al'ajabi na 8 a duniya' yana unguwar Lintong ta birnin Xian, inda akwai gumaka fiye da 6,000 wadanda kuma aka dauka cewa ganowa ce mafi girma da aka yi a cikin karni na 20; Ban da wannan kuma, a wannan birni, akwai Hasumiya ta Dayan, da Wurin wanka na Huaqing da kuma tsaunin Huashan da dai sauran wurare masu kayatarwa.
Lhasa
Birnin Lhasa, hedkwata ce ta jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin. Fadin birnin ya kai muraba'in kilo-mita 29,052. Wannan birni yana a arewacin tsaunukan Himalaya, inda yanayi yana da kyau. Ban da wannan kuma lokuta samun hasken rana da akan samu a duk shekara a wannan birni sun wuce awoyi 3,000; Ana kiran birnin a kan cewa ' Birnin Hasken Rana'.
Birnin Lhasa yana kan babban tudun Qinghai-Tibet, wanda ake kiransa ' Kololuwar Tsaununa a duniya'; kuma matsakaicin leburin teku na babban tudun ya kai mita 3,600 ko fiye; Daga watan Afrilu zuwa watan Oktoba na kowace shekara, lokaci ne mafi kyau da akan zo nan domin yin yawon shakatawa.
A cikin yaren Tibet, ma'anar kalmar Lhasa ita ce wuri ne mai tsarki da mala'iku ke zaune. Tarihin garin Lhasa dauwamamme ne, wanda ke da al'adun addini na musamman ; A cikin garin, da akwai Dakin Ibada na Dazhao, da Titin Ba Kuo da kuma Fadar Sarki ta Budalah da dai sauran wuraren yawon shakatawa masu ban sha'awa.
Kyawawan kananan birane da garuruwa
Biranen kasar Sin suna da tarihi mai dorewa, musamman ma wassu kananan birane dake da tarihi na tsawon shekaru 100 ko fiye da suka fi daukar hankulan mutane. Alal misali: an riga an rubuta suna garin Li Jiang na lardin Yunnan cikin littafin sunayen wuraren tarihi na duniya. Tarihi da al'adu da kuma zamanin da da na yanzu na kananan birane da garuruwa na kasar Sin sun ba da sha'awa sosai ga masu yawon shakatawa na gida da na waje.
1. Zhouzhuang
To, yanzu bari mu dan gutsura muku bayani kan garin Zhouzhuang. Garin Zhouzhuan yana nan gabashin lardin Jiangsu na kasar Sin, kuma yana da nisan kilo-mita 38 kawai daga tsohon birnin Suzhou. Wani shahararren mai zane-zane na kasar Sin malam Wi Guanzhong ya taba rubuta wani bayani dake cewa:' Tsaunin Huang Shan ya fi kyaun gani bisa tsaunuka da koguna na kasar Sin; haka kuma garin Zhouzhuang ya fi kyaun gani bisa garuruwa da kauyuka,wadanda koguna ke kewaya su na kasar'. Kazalika, wassu jaridun kasashen waje suna kiran garin Zhouzhuang gari ne na farko dake da koguna a kasar Sin'.
Kashi 60 cikin kashi 100 na gidajen mazauna garin Zhouzhuang, an gina su ne a daular Ming da daular Qing; kuma fadin garin ya kai muraba'in kilo-mita 0.4 kawai. Muhallin garin Zhouzhuang yana da kyau, inda mawallafa da masana ilmi da yawa na zamanin da sukan yi kararu a tsanake.
Garin Zhouzhuang yana kusa da birnin Shanghai; kuma akan samu sauki wajen tafiye-tafiye tsakanin wuraren biyu.
2. Tsohon gari na Feng Huang
Garin Feng Huang yana jihar Xiangxi ta kabilar Tujia da kabilar Miao mai cin gashin kai ta lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin. Wani shahararren mawallafi na kasar New Zealand mai suna Louise Aray yana kiran garin Feng Huang a kan cewa shi ne daga cikin kyawawan kananan garuruwa na kasar Sin. An gina wannan gari ne a daular Qing mallakar sarki Kangxi.
Garin Feng Huang ya shahara ne saboda aka haifi mashahurin mawallafi na zamanin yau na kasar Sin mai suna Shen Congwen a nan.
>>[Girke-girken kasar Sin]
Girke-girken kasar Sin
Al'adar girke-girken kasar Sin ita ce kashi daya mai muhimmanci daga cikin al'adun al'ummar kasar Sin; kuma girke-girken kasar Sin sun yi suna sosai a duk duniya kuma suna da dogon tarihi. Girke-girken kasar Sin suna nan iri iri masu yawan gaske dake kasancewa a wassu lardunan kasar; Wadanda suka fi shere mutane suna kasancewa a larduna 8, wato lardin Shandong, da lardin Sichuan, da lardin Guangdong, da lardin Fujian, da lardin Jiangsu, da lardin Zhejiang da kuma lardin Anhui. Mutane sukan kira su 'Muhimman tsare-tsare iri 8 na girke-girken kasar Sin'. Kasancewar tsarin girke-girke tana da nasaba da tarihi mai dorewa na girke-girken da kuma dabarun dafa abinci; kuma tana samun tasiri daga labarin kasa, da yanayin sama, da albarkatai da kayayyaki irin na musamman da kuma tsarin gargajiya dangane da abinci da shaye-shaye na wurin da ake bin tsarin girke-girken.
Yanzu za mu shirya muku wassu shahararrun girke-girken kasar Sin, wadanda da sauki ne ake iya dafawa :
1. Yalon da aka dafa tare cda barbashin naman tumaki ;
2. Jatan lande mai dadin ci;
3. Shinkafa da aka dafa tare da kwai ;
4. Miyar kaza mai dadin sha;
5. Kaguwarda aka dafa cikin tukunya irin na turari;
6. Naman da aka dafa da ruwan magin waken soya;
7. Dankalin turawar da aka dafa tare da koren tattasai;
8. Naman sa da aka dafa tare da dankalin turawa;
9. Dankalin turawar da aka dafa tare da koren tattasai da yalo;
10. Kajin da aka dafa cikin ruwa;
11. Kakambar da aka soya tare da kwai;
12. Naman tumakin da aka dafa tare da karas;
13. Dankalin turawar da aka dafa tare da koren tattasai mai yaji;
14. Naman kaji da aka dafa da ruwan tsami;
15. Kwadon ' yan ' yan itatuwa;
16. Kwadon kayayyakin lambu;
17. Jatan lande da aka dafa cikin ruwa;
18. Ganyen tafarnuwa da aka soya tare da kwai ;
19. Naman sa da aka dafa tare da koren tattasai ;
20. Kifin da aka dafa cikin tukunya irin na turari ;
21. Albasa da aka soya tare da kwai ;
22. Naman tumakin da aka soya tare da ganyen albasa ;
23. Tumatir da aka soya tare da kwai ;
24. Datsattsen naman kajin da aka soya tare da yaji ;
25. Soyayyen naman kaji;
26. Tuwon yalon da aka cakuda;
27. Soyayyen kayayyakin lambu;
28. Kabejin da aka dafa da ruwan tsami;
29. Soyayyen jatan lande;
30. Kifin da aka dafa da ruwan tsami.
>>[Domin masu yowon shakatawa]
Shahararrun hotel-hotel na kasar Sin
Yanzu kasance da manyan hotel-hotel da yawansu ya kai 8,880 a babban yankin kasar Sin ( ban da yankin Hongkong, da Macao da kuma na Taiwan ), wadanda suka bazu a larduna, da biranen dake karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya kai tsaye da kuma jihohi masu cin gashin kansu gida 31 dake da dakuna kusan 900,000; Daga cikinsu, akwai hotel-hotel 175 masu taurari biyar, da hotel-hotel 635 masu taurari hudu da hotel-hotel 2846 masu taurari uku, da hotel-hotel 4,414 masu taurari biyu da kuma hotel-hotel 810 masu tauraro daya. Ga wassu manyan hotel-hotel masu taurari biyar a kasa:
【 Manyan hotel-hotel na kasar Sin 】
[Beijing]
Sunan Hotel Lambar wayarsa Adireshinsa
Beijing hotel 86-10-65137766 Gini mai lamba 33 dake gabashin Titiin Chang An na Gundumar Dongcheng;
Babban hotel na kasar Sin 86-10-65052266 Gini mai lamba 1 dake kan babban titin Jian Guo Men
Hotel na Babbar Ganuwa 86-10-65905566 Gini mai lamba 10 dake arewacin kewayayyiyar hanya ta 3 ta gabas
Hotel na Kunlun 86-10-65003388 Gini dake kudancin Xin Yuan na Gundumar Chao Yang
Hotel na Chang Fu Gong 86-10-65125555 Gini mai lamba 26 dake babban titi na waje da Jian Guo Men
Hotel na Gui Bin Lou 86-10-65137788 Gini mai lamba 35 dake kan gabashin babban titi na Chang An na Beijing na kasar Sin
Hotel na Xiangerila 86-10-68512211 Gini dake kan hanyar Wi Zhu Yuan a Gundumar Hai Dian
kuma Hotel na Wang Fu 86-10-65128899 Gini dake cikin lungu mai suna Jin Yu na Gundumar Dong Cheng
[Shanghai]
Sunan Hotel Lambar wayarsa Adireshinsa
Babban Hotel na Xin Jin Jiang 86-21-64151188 Gini mai lamba 161 dake kan hanyar Chang Le ta Shanghai
Babban Hotel na Hilton 86-21-62480000 Gini mai lamba 250 dake kan hanyar Hua Shan ta Shanghai
Babban Hotel na Xiangerila na Pu Dong 86-21-68828888 Gini mai lamba 33 dake kan hanyar Fu Cheng ta Sabuwar Gundumar Pu Dong ta Shanghai
Hotel na Pottmanlega 86-21-62798888 Gini mai lamba 1376 dake yammacin hanyar Nan Jing a Gundumar Jin An ta Shanghai
[Tianjin]
Sunan Hotel Lambar wayarsa Adireshinsa
Babban Hotel na Shiraton 86-22-3343388 Gini dake kan hanyar Jin Shan ta Gundumar He ta birnin Tian Jin
[Guangzhou]
Sunan Hotel Lambar wayarsa Adireshinsa
Hotel na Bai Tian Er na Guangzhou 86-20-81886968 Gini mai lamba 1 dake kudancin titin Sha Mian na Guangzhou
Hotel na Quangzhou Huayuan 86-20-83338989 Gini mai lamba 368 dake gabashin hanyar Huanshi ta birnin Guangzhou
Babban hotel na kasar Sin 86-20-86663388 Gini dake kan hanyar Liu Hua ta gundumar Yue Xiu ta birnin Guangzhou
[Dalian]
Sunan Hotel Lambar wayarsa Adireshinsa
Babban hotel na Fu Lihua 86-411-82630888 Gini dake kan hanyar Jama'a na Dalian
[Xi'an]
Sunan Hotel Lambar wayarsa Adireshinsa
Hotel na Kai Hue( Ar Fang Gong) 86-29-7231234 Gini mai lamba 158 dake kan gabashin babban titi na Xi'An
Babban hotel na Shiraton 86-29-4261888 Gini mai lamba 12 dake kan hanyar Fong Hao a Xi'An
Shahararrun ofisoshin shirya tafiye-tafiye na kasar Sin
Yanzu ya kasance da ofisoshin shirya tafiye-tafiya 11,615 dungum a kasar Sin; kuma 1,358 daga cikinsu na kasa da kasa ne, kuma 10,257 da suka yi saura na cikin gida ne. Shahararrun ofisoshin shirya tafiye-tafiye su ne:
Beijing
Ofishin shirya tafiye-tafiye Lambar wayarsa Adireshinsa
Ofishin shirya tafiye-tafiye na kasa da kasa na kasar Sin 86-10-85228866 Gini dake babban titi mai lamba 1 na arewacin Dongdan na Gundumar Dongcheng ta birnin Beijing
Ofishin shirya tafiye-tafiye na kasar Sin 86-10-64622288 Gini mai lamba 2 dake gabashin kewayayyiyar hanya ta 3 ta birnin Beijing
Ofishin shirya tafiye-tafiye na samari na kasar Sin 86-10-64656380 Gini mai lamba 1 dake hanyar Zuo Jia Zhuang a Gundumar Chao Yang ta birnin Beijing
Ofishin shirya tafiye-tafiye na Kang Hui na kasar Sin 86-10-65940885 Gini mai lamba 5 dake kudancin hanyar dakin nune-nunen kayayyakin noma na birnin Beijing
Shanghai
Ofishin shirya tafiye-tafiye Lambar wayarsa Adireshinsa
Ofishin shirya tafiye-tafiya na kasa da kasa na Wai Hang na Shanghai 86-21-63500170 Gini mai lamba 800 dake gabashin hanya ta Nanjing a Shanghai
Ofishin shirya tafiye-tafiye na kasa da kasa na Yangtse na Shanghai 86-21-62999403 Gini mai lamba 595 dake Hanyar Guilin ta Gundumar raya tattalin arziki na zamani ta Cao He Jin a birnin Shanghai
Guangzhou
Ofishin shirya tafiye-tafiye Lambar wayarsa Adireshinsa
Ofishin shirya tafiye-tafiye na kasa da kasa na Tian Ma na Guangzhou 86-20-81881880 Gini mai lamba 113 dake yammacin hanyar Yan Jiang ta birnin Guangzhou
Xi'an
Ofishin shirya tafiye-tafiye Lambar wayarsa Adireshinsa
Ofishin shirya tafiye-tafiye na kasa da kasa na Tarbiyya na Xi'An 86-29-5361018 Gini mai lamba 447 dake kudancin hanyar Chang An ta birnin Xi'An
Shenzhen
Ofishin shirya tafiye-tafiye Lambar wayarsa Adireshinsa
Ofishin shirya tafiye-tafiye na Bao Ye na Shenzhen 86-755-82101915 Gini mai lamba 1014 dake tsakiyar hanya ta Shen Nan a birnin Shenzhen
Chengdu
Ofishin shirya tafiye-tafiye Lambar wayarsa Adireshinsa
Kamfanin shirya tafiye-tafiye na Hai Wai na Cheng Du 86-28-86741113 Gini mai suna Shun Ji dake babban titi mai suna Shun Cheng na birnin Cheng Du
Sanarwa kan aikin cika takardar visa a kasar Sin
Bisa mataki na farko ga matafiya dake son yin yawon shakatawa a kasar Sin, lallai cika takardar visa yana da muhimmancin gaske. Idan baki suna so su zo nan kasar Sin domin yin yawon shakatawa, to ya kamata su je ofishin jakadanci ko karamin ofishin jakadanci na kasar Sin dake kasarsu domin cika takardar visa; Idan ya kasance da wata kungiya dake kunshe da mutane 9 ko fiye tana so ta zo nan kasar Sin domin yin ziyara, to ta iya neman cika takardar visa ta kungiya; Ban da wannan kuma, an tanadi, cewa baki dake zaune a shiyyar musamman ta Hongkong idan suna so su je shiyyar musamman ta Shenzhen domin yin ziyara, to suna iya shigowa cikin yankin kasar Sin ba tare da bukatar cika takardar visa ba a cikin awoyi 72; Duk baki dake rike da takardar visa ta matafiya, tilas ne su shigo cikin yankin kasar Sin daga tashoshin kwastan da kasar Sin ta bude musu kuma bayan da hukumomin bincike masu tsaron bakin iyakar kasa ta kasar Sin suka dudduba su.
Aminai, kuna iya yin yawon shakatawa rike da takardar visa da kuma fasfo a duk wuraren dake cikin yankin kasar Sin wadanda gwamnatin kasar ta bude musu. Ko shakka babu gwamnatin kasar Sin takan kiyaye hujja da kuma fa'ida na halal na dukkan bakin dake cikin yankin kasar Sin; Amma duk da haka, bai kamata baki matafiya su yi abubuwan da ba su dace ba a cikin yankin kasar Sin; Duk wadanda suka yi abubuwan rashin da'a a fannin neman aikin yi, da yin farfaganda kan harkokin addini da kuma daukar labarai, labuddah za a yanke musu hukunci; A sa'I daya kuma, ya kamata baki matafiya su nuna biyayya ga dokokin shari'a da kuma dabi'ar gargajiya na kasar Sin yayin da suke tafiye-tafiye a cikin yankin kasar.
Aminai baki suna iya yin yawon shakatawa a kasar Sin bisa wa'adin da aka kayyade musu a cikin takardar visa; Idan suna so su ci gaba da yin tafiye-tafiya bayan wa'adin yada zango ya cika, to suna iya gabatar da rokonsu na tsawaita ma'adin ga hukumar ' yan sanda ta wurin da suke a can; Idan baki sun gama tafiye-tafiye, to talas ne su yi fici daga tashar kwastan ta kasa da kasa da gwamnatin kasar Sin ta bude musu musamman bayan duddubawar da hukumar tsaron bakin iyakar kasar ta yi musu.
Sanarwa kan shigi da fici daga kasar Sin
Wajibi ne a bi ka'idoji dangane da shigi da fici daga kasar Sin :
1. Bayyanawa :
Ya kamata fasinjoji su bayyana wa jam'an kwastan hakikanan abubuwan da suke dauke da su kamar haka :
Kayayyakin da kwastan ta buga musu haraji ko rage yawan haraji, wadanda akan shigo da su daga kasashen waje da kuma kayayyakin da kasar Sin ta hana shigo da fitar da su zuwa kasashen waje, da kuma kayayyakin tarihi,da kudade, da zinariya da azurfa da , makamantansu har da abubuwan dab'i da kaset da CD da VCD da makamantansu da ake iya saurara ko kallon hutuna, wadanda kasar Sin ta kayyade shigowa ko fitarwa ;
2. Hanyar mai lambar ja da hanyar mai lambar kore,wato :
Hanyar masu dauke da abubuwan dake bukatar jami'an kwastan su sani da kuma hanyar wadanda ba su dauke da wani abu da lallai sai jami'an kwastan sun sani.
3. Sauran ka'idoji :
A lokacin da fasinjoji ke shiga da fita a filin jirgin sama, tilas ne su sa kayansu cikin wata na'urar kwastan dake nuna mene ne a cikin akwatuna ko jakunansu.
Sanarwa kan harkokin kiwon lafiya
Hukumar sa ido kan lafiyar dabbobi ta Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, wata hukuma ce ta aiwatar da dokoki dake shafar harkokin waje, wadda takan dudduba lafiyar dabbobi bisa nauyin da majalisar gudanarwa ta Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta danka mata. Wannan hukuma da kuma sauran kananan hukumomin sa ido kan lafiyar dabbobi na wurare daban daban na kasar dake karkashin shugabancinta sukan dudduba lafiyar dabbobi bisa doka ga wadanda suka yi shigi da fici daga tashoshin kwasatan da gwamnatin kasar Sin take bude wa kasashen waje; Sa'annan tashoshin kwasatan su ba da iznin shigi ko fici bisa wata takardar musamman ta dudduba kayayyakin da abun ya shafa.
Duk fasinjoji da kodagan da suka yi shigi da fici, tilas ne su kai kayayyakin da suke rike da su ko yin jigilarsu ta jirgin sama ko jirgin kasa ko jirgin ruwa, wadanda kuma mai yiwuwa ne su watsa ciwace-ciwace masu yaduwa a gaban hukumomin sa ido kan lafiyar dabbobi da kayayyaki; Wadannan hukumomi sukan tsabtace ko rushe wassu cimaka da aka kawo da su daga wuraren da annoba ta auku da kuma wadanda aka kazamtar da su; Tashoshin kwasatan sukan ba da iznin shigi ko fici bisa takardar shaida da hukumomin sa ido kan lafiyar dabbobi suka sa hannu a kai.
Duk wadanda suka zo daga wuraren da annobar ciwon shawara ta auku, tilas ne su gwada takardar yin allurar riga-kafin irin wannan ciwo a gaban hukumomin sa ido kan lafiyar dabbobi;
Ayyukan da akan sa ido kan ciwace-ciwace masu yadawa sun hada da wadanda suka yi shigi da fici, da kayayyakin tafiye-tafiye, da abinci, da kuma ruwan sha da suke rike da su, har da ire-iren kwaro masu haifar da cututtuka, da dabbobi da kuma ciwace-ciwace masu yaduwa.
Lallai hukumomin sa ido kan lafiyar dabbobi na kasar Sin za su hana baki da suka kamu da ciwon sida, da ciwon sanyi, da ciwon kuturta, da kuma ciwon huhu har da wadanda suka gamu da tabuwar hankali su shigo cikin yankin kasar.
Sanarwa kan yadda ake yin amfani da kudade a kasar Sin
1. Kudin Kasar Sin:
Kudin kasar Sin, shi ne Renminbi Yuan, wanda Bankin Jama'ar kasar Sin ya buga. Muhimmin sashen kudin Renminbi, shi ne Yuan; sauran sassa biyu, su ne
Jiao da Feng. Yuan daya Jiao goma ne; kuma Jiao daya feng goma ne. Takardun darajar kudin Yuan suna da iri daban daban, kamar Yuan daya, da Yuan biyu, da Yuan biyar, da Yuan goma, da Yuan 50 da kuma Yuan dari daya; Takardun darajar kudin Jiao sun hada da Jiao daya, da Jiao biyu da kuma Jiao biyar; kuma Takardun darajar kudin Feng sun hada da Feng daya, da Feng biyu da kuma Feng biyar. Lambar takaitaccen kudin Renminbi Yuan, ita ce RMB¥.
2. Musanyar kudaden kasashen waje:
Kudaden kasashen waje da ake iya yin musanye-musanye, su ne Dolar Amurka, da Pound na kasar Burtaniya, da Yen na kasar Japan, da Dolar Australiya, da Franc na kasar Belguim, da Dolar Canada, da Dolar Hongkong, da Franc na kasar Swiss,da Crone na kasar Norway, da Dolar Singapore, da Dolar Macao,da Euro da Yuan New Ziland da dai sauransu. Bankunan kasar Sin suna kula da musanye-musanyen kudaden waje.
Bisa abubuwan da aka tanada a cikin doka kan aikin kula da kudaden waje da bankunan kasar Sin suke aiwatarwa yanzu, an ce, a cikin yankin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, a hana yin amfani da kudaden waje kai tsaye wajen sayen kayayyaki. Domin saukaka hanyoyin da baki da kuma ' yan-uwa na Hongkong, da Macao da kumana Taiwan suke bi wajen kashe kudade, Bankin kasar Sin da kuma sauran bankunan ma'amalar kudaden waje da aka amince da su suna iya karbar chek din kudi na matafiya da kuma katin bashi na kasashen waje domin ba da kudin kasar Sin wato Renminbi Yuan; A sa'i daya kuma, suna yin ma'amalar canjin tsabar kudaden waje iri 14 da kuma sabon kudin Taiwan. Ban da wadannan bankuna, wassu otel-otel da kantuna su ma suna tafiyar da irin wannan aikin canjin musanyen kudade.
3. Katunan bashi wato Credit Card a Turance na kasashen waje da ake iya bayarwa a kasar Sin:
Yanzu, muhimman kantunan bashi na kasashen waje da ake iya bayarwa a kasar Sin sun hada da Katin Master, da Katin Vise, da Katin American Express, da Katin JCB da kuma Katin Diners.
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China |