Xi Jinping ya kama hanyar halartar taron koli na G20 2014-11-14 A yau Jumma'a 14 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga nan birnin Beijing, don fara ziyarar a wasu kasashen ketare. Kamar yadda aka tsara da farko zai halarci taron kolin kungiyar G20 da za a shirya a birnin Brisbane na kasar Australia, daga baya kuma zai kai ziyarar aiki a kasashen Australia, New Zealand, da kuma Fiji