An cimma yarjejeniyoyi da dama tsakanin Sin da Nijeriya A ranar 10 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na tarayyar Nijeriya, Goodluck Jonathan, wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar ta Sin, ganarwar da aka dauka a matsayin ganawa tsakanin kasar da ta fi yawan al'umma a duniya, da kuma wadda ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka. A ganawar da suka yi ta tsawon sa'a guda, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra'ayi dangane da yadda za a dada bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen nasu, da ma kasashen Afirka baki daya, inda suka jaddada muhimmancin taimakon juna, da samun ci gaban tare a matsayin burin bai-daya na kasashen biyu
|