v Wu Bangguo zai kai ziyara kasashen Afirka 5 nan ba da jimawa ba Shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Wu Bangguo, zai fara rangadinsa na sada zumunta a hukunce a kasashen Afirka biyar daga ranar Litinin din nan ne bisa goron gayyatar da shugabannin majalisun dokokin kasashen suka yi masa, ciki har da Aljeriya, da Gabon, da Habasha, da Madagascar tare kuma da Seychelle