Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-11 16:21:10    
Wu Bangguo ya halarci bikin kaddamar da aikin gina cibiyar taron kungiyar AU da ya samu taimako daga wajen kasar Sin

cri

A ran 10 ga wata da safe, a cikin kide-kiden da ke da halin musamman na kabilar kasar Habasha, birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasa da ke kan tudun gabashin Afirka ya samu wani bako na kasar Sin wato shugaban majalisar wakilan jama'ar Sin Wu Bangguo, inda aka shirya bikin kaddamar da aikin gina cibiyar taron kungiyar tarayyar Afirka wato AU da ya samu taimako daga wajen kasar Sin. A wurin shirya bikin, tutocin kasar Sin da membobin kungiyar AU suna karkatawa cikin iska yayin da manyan na'urori fiye da goma a shirye suke. Baki ciki har da Wu Bangguo da shugaban kwamitin kula da harkokin AU Jean Ping sun shaida wannan muhimmin sakamako mai kyau da aka samu daga hadin gwiwar Sin da Afirka cikin aminci tare.

Kuma a gun bikin, Wu Bangguo ya sanar da kaddamar da aikin gina cibiyar taron kungiyar AU. Ya ce, "Yanzu na sanar da cewa, an kaddamar da aikin gina cibiyar taron kungiyar AU a hukunce."

A watan Nuwamba na shekara ta 2006, shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka 48 sun halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka kan hadin kansu, kuma sun tabbatar da kulla dangantakar abokantaka ta sabon salo tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, wato zaman daidai wa daida da kuma samun amincewa da juna a fannin siyasa, da hadin gwiwa don moriyar juna a fannin tattalin arziki, da kuma yin cudanya da koyi da juna a fannin al'adu. Haka kuma shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayar da matakai 8 wajen hadin kai tare da Afirka a cikin shekaru 3 tun daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2010, wadanda daya daga cikinsu shi ne samar da taimako wajen gina cibiyar taron kungiyar AU. Kuma wannan aiki shi ne aiki mafi girma da kasar Sin ta samar da taimako a kansa a Afirka ban da aikin shimfida hanyoyin jirgin kasa tsakanin kasashen Tanzania da Zambia, kuma an kiyasta cewa, za a iya kammala aikin a shekara ta 2010.

A gun bikin, Wu Bangguo ya ba da jawabin cewa, kaddamar da aikin gina cibiyar taron kungiyar AU ta shaida cewa, tabbas ne hadin gwiwar Sin da Afirka zai samu wata kyakkyawar makoma. Kuma ya kara da cewa, "Abin farin ciki shi ne, a cikin shekaru 2 da suka gabata, matakan da aka dauka bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka kan hadin kansu sun samu muhimman sakamako masu matukar kyau bisa kokarin da bangarorin Sin da Afirka ke yi. Kuma an riga an aiwatar da manufofi da matakai 8 da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen hadin gwiwa tare da Afirka yadda ya kamata, ta yadda aka sauya kaunar da jama'ar Sin ke nunawa jama'ar Afirka zuwa hakikanan abubuwa."

Bugu da kari kuma, Mr. Jean Ping, shugaban kwamitin kula da harkokin AU ya ba da jawabi, inda ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da ta bai wa jama'ar Afirka wannan kyauta mai daraja lokacin da kungiyar AU ke girma sannu a hankali. Kuma ya bayyana cewa, aikin gina cibiyar taron kungiyar AU zai ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka. Ya ce, "Ina son in sake jaddada cewa, Afirka za ta sa muhimmanci sosai kan wannan kyauta ta musamman da ta zo daga kasar Sin, za mu tuna da irin wannan kaunar da Sin ke nuna mana har abada. Cibiyar za ta kafa tushe mai inganci ga dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, ta yadda bangarorin biyu za su samu babban ci gaba wajen hadin kansu."(Kande Gao)