Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
 
• Dan takarar shugaban kasar Afghanistan Abdullah Abdullah ya janye jiki daga zagaye na biyu na babban zabe
A ran 1 ga wata, Abdullah Abdullah, dan takarar shugaban kasar Afghanistan kuma tsohon ministan harkokin waje na kasar ya sanar da cewa, ya nuna fargabar cewa ba za a kwatanta adalci a cikin babban zaben ba, don haka ya tsai da kudurin janye jiki daga zagaye na biyu na zaben bayan da ya saurari ra'ayin jama'a.
• Iran ta mai da martani ga shirin yarjejeniyar samar da makamashin nukiliya
A ran 29 ga wata, kasar Iran ta mika wata takarda ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA domin mai da martini ga shirin yarjejeniyar samar da makamashin nukiliya, amma ba a bayyana hakikanin abubuwan da aka rubuta cikin takarda ba.
• An samu matsalar kai farmaki irin ta kunar bakin wake mai tsanani sosai a Iran
A ran 18 ga wata, an samu wata matsalar kai farmaki irin ta kunar bakin wake a lardin Sistan Baluchestan na kasar Iran, inda aka haddasa mutuwar mutane 35, ciki har da manyan hafsoshi 2 na rundunar tsaron juyin juya hali ta Musulunci ta kasar Iran, wasu mutane 28 suka kuma jakkata.
• Iran ta amince da hukumar IAEA ta gudanar da bincike kan masana'antarta ta biyu ta tace sinadarin Uranium a wannan wata
Ranar 4 ga wata, babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA wanda ya kai ziyara kasar Farisa Mista Mohamed El Baradei ya bayyana cewa, Farisar ta riga ta amince da jami'an hukumar su gudanar da bincike kan masana'antar tace sinadarin Uranium ta biyu a kasar a ranar 25 ga wata.
• Gagarumin biki yana sheda nasarar da kasar Sin ta samu
A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, a ginin Tian'anmen da ke cibiyar birnin Beijing, Mao Zedong, marigayi shugaban kasar Sin na wancan lokaci ya sanar da kafuwar sabuwar kasar Sin, wato Jamhuriyar Jama'ar Sin. Bayan shekaru 60 da suka gabata, a wannan rana, kuma a ginin Tian'anmen na birnin Beijing, kasar Sin ta kuma shirya bikin duba faretin sojoji da shagalin yin maci cikin fara'a domin tunawa da wannan muhimmiyar rana.
• An hana nuna Sinima mai suna "District Nine" ta kasar Amurka sakamakon sharrin da ta yi wa kasar Nigeriya
A ranar 19 ga wannan wata, gwamnatin kasar Nigeriya ta ba da umurnin hana nuna sinimar dabon kimiyya mai suna "District Nine" ta kasar Amurka a gidajen nuna sinima daban daban na kasar Nigeriya sakamakon sharrin da ta yi wa kasar Nigeriya a cikin wasu wasannin da aka yi a cikin sinimar.
• An kaddamar da babban taro a karo na 64 na M.D.D
A ranar 15 ga wata agogon New York, an kaddamar da babban taro a karo na 64 na M.D.D a birnin New York, hedkwatar M.D.D, yayin da sabon shugaban babban taron M.D.D kuma sakatare mai kula da harkokin kungiyar tarayyar Afrika na kasar Libya Ali Treki ke yin jawabin fatan alheri, ya bayyana cewa, dole ne a yi gyare-gyare ga babban taron M.D.D...
• Ko an canja halin da ake ciki a titin Wall bayan da aka cika shekara daya da rufewar Lehman Brothers?
Yau shekara daya da ta gabata, wato a ran 15 ga watan Satumba na shekarar bara, ba zato ba tsammani aka sanar da rufe bankin zuba jari na Lehman Brothers wanda ya fi girma na hudu a cikin bankunan kasar Amurka. Sakamakon haka, an haddasa rikicin kudi mafi tsanani a duk duniya tun daga shekaru 30 na karnin da ya gabata.
SearchYYMMDD