Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-05 19:00:25    
Iran ta amince da hukumar IAEA ta gudanar da bincike kan masana'antarta ta biyu ta tace sinadarin Uranium a wannan wata

cri

Ranar 4 ga wata, babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA wanda ya kai ziyara kasar Farisa Mista Mohamed El Baradei ya bayyana cewa, Farisar ta riga ta amince da jami'an hukumar su gudanar da bincike kan masana'antar tace sinadarin Uranium ta biyu a kasar a ranar 25 ga wata.

Ranar 3 ga wata da maraice, Mohamed El Baradei ya isa birnin Tehran na kasar Iran. Babban makasudin ziyararsa a wannan gami shi ne, yin shawarwari tare da jami'an gwamnatin Iran kan batun nukiliyar kasar. A ranar 4 ga wata kuma, El Baradei ya yi shawarwari tare da shugaban kasar Mahmoud Ahmadinejad, gami da mataimakin shugaban kasar, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar makamashin nukiliya ta Iran Ali Akbar Salehi. Daga bisani, El Baradei da Ali Akbar Salehi sun shirya taron manema labarai cikin hadin-gwiwa, inda Salehi ya nuna cewa, an yi shawarwari tsakaninsu tare da samun cikakkiyar nasara, haka kuma El Baradei ya ce, an samu ci gaba a yayin shawarwarin, kasar Iran ta riga ta amince da jami'an hukumar IAEA su gudanar da bincike kan masana'antar tace sinadarin Uranium ta biyu dake dab da birnin Qom na kasar.

1 2 3