Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-15 15:52:52    
Har wa yau dai makomar tattalin arzikin Amurka tana cikin  halin rashin sanin tabbas

cri

Wata babbar manazarciya ta kungiyar manyan mutane masu zarfin ilimi ta kasar Amurka kuma tsohuwar mataimakiyar shugabar hukumar kula da ma'aikatun kudade ta tarayya ta Amurka Madam Alice Rivlin ta bayyana cewa,idan an kwatanta da wasu alamun farfadowa a halin yanzu,yawan mutanen da suka rasa aikin yi ya fi damun jama'a. Ta ce"koma bayan tattalin arziki na Amurka na ci gaba a halin yanzu,har yanzu ba mu san inda zai kwana ba. Da ya ke mun ga yawan GDP ya dakatar da faduwa,mutanen da suka rasa aikin yi suna ci gaba da karuwa a wani lokaci.wannan ba bakon labari ba ne. mummunar tabarbarewa ce da ake gani, kila yawan marasa aikin yi ya ja koma bayan farfadowar tattalin arziki." Ta la'akari da hali mai muni da tattalin arzikin Amurka ke ciki, kwanakin baya wakilin kungiyar mashawarta na shugaba Obama wajen tinkarar tabarbarewar tattalin arziki Mr Laura Tyson ya yi nuni da cewa shirin sa kaimi ga tattalin arziki da dalar Amurka biliyan 787 da aka fitar da shi a watan Fabrairu na bana na da iyaka,sakamakon tabbatar da shi bai bayyanu ba,kamata ya yi a yi la'akari da tsara wani sabon shirin sa kaimi kan harkokin kudade domin yin shirin daidaita tattalin arziki idan lokaci ya yi.duk da haka shugaba Obama bai mayar da martani ga shirinsa ba. A cikin jawabin da ya saba yi a kowane mako a ranar 11 ga watan Yuli,shugaban kasar Amurka Obama ya yi kira ga jama'ar kasa da su yi hakuri da shirin da ake tafiyar da shi a halin yanzu.(Ali)


1 2 3