Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-15 15:52:52    
Har wa yau dai makomar tattalin arzikin Amurka tana cikin  halin rashin sanin tabbas

cri

Har wa yau dai makomar tattalin arzikin Amurka tana cikin halin rashin sanin tabbas Assalamu alaikun jama'a masu sauraro, barkanku da war haka,barkanmu da sake saduwa da ku a wannan shirin na duniya ina labari. A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyo ya ruwaito mana a kan cewa har yanzu dai makomar tattalin arzikin Amurka tana cikin halin rashin sanin tabbas.

Tun daga shekarar bara da tattalin arzikin Amurka ya shiga yanayin koma baya, kasashen duniya sun mayar da hankalinsu kan lokacin farfadowarsa.Ko shakka babu a kan matsayin kasa mai karfin tattalin arziki a duniya,farfadowar tattalin arzikin kasar Amurka za ta jawo babban tasiri ga tattalin arzikin duniya da ta fito daga kangin mawuyancin hali na yanzu.amma ga dukkan alamu na yanzu,makomar tattalin arzikin Amurka tana cikin halin rashin sanin tabbas. Tun lokacin da shugaba Obama ya hau karagar mulki,gwamnatin Amurka ta kaddamar da shirin sa kaimi ga tattalin arzikinta na dalar Amurka biliyan 787 da shirin kawo sauyi ga hukumomin sa ido na kudade,da kuma shirin tantance dukiyoyi ko munanan kadarori da kuma shirin yi wa takardun lamuni kwaskwarima duk domin gaggauta farfado da tattalin arziki da tsaurara matakan sa ido kan hukumomin kudade. A yayin da yake hira da kafofin yada labarai a ran 2 ga watan Yuli,shugaban kasar Amurka Obama ya yi jawabi kan sakamakon matakai a jere da gwamnatinsa ta dauka.Ya ce"mun riga mun sami nasarar daidaita da kasuwanninmu na kudade,wannan yana da muhimmancin gaske.wannan kuma ci gaba ne da muka samu wajen kubutar da kanmu daga rikicin kudi. Mun kuma ga wasu alamu masu kyau a kasuwannin gidaje da filaye."

1 2 3