Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-01 18:23:16    
Jam'iyyar kwaminis ta Sin na kara mai da hankali a kan sauraron ra'ayoyin jama'a domin inganta kanta a sabon halin da ake ciki

cri

Mr.Li Zhongjie ya ce, a nan gaba, jam'iyyar kwaminis ta Sin za ta bi hakikanin halin da ake ciki, ta yi ta inganta kanta, don neman karin ci gaba. Wani taron ofishin siyasa na jam'iyyar kwaminis ta Sin da aka yi a ran 29 ga watan Yuni da ya gabata ya bayyana kokarin da jam'iyyar ke yi wajen kara sauraron ra'ayoyin jama'a. Taron dai ya dudduba da kuma amince da sabon tsarin binciken ayyukan shugabannin jam'iyyar, wanda ke neman daga matsayin gamsuwar jama'a a wajen binciken ayyukan shugabannin jam'iyyar. A ganin Mr.Li Zhongjie, sabon tsarin na iya bayyana yadda shugabannin ke gudanar da ayyukansu sosai Kamar yadda ya ce,"Misali, tsarin ya kyautata hanyoyin binciken ayyukan shugabannin jam'iyyar, kuma tana iya binciken ayyukan shugabannin daga dukkan fannoni, wato ba ma kawai za a duba nasarorinsu a wajen raya tattalin arziki ba, hatta ma za a duba yadda suke bunkasa zaman al'umma, ciki har da ba da kariya ga muhalli, ta yadda za a tabbatar da samun dauwamammen ci gaba."(Lubabatu)


1 2 3