Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 23:02:46    
Aikin raya harshe da kalmomin kabilar Tibet ya shiga cikin sabon zamani

cri

Shugaban rukunin binciken wayar salula dake dauke da kalmomin Tibet, kana mataimakin babban injiniya daga reshen kamfanin sadarwa na kasar Sin dake jihar Tibet Mista Nyima Dondrup ya nuna cewa, tun shekara ta 2003, aka soma bunkasa harkokin sadarwa a jihar Tibet bisa ga la'akari da hakikanin halin da ake ciki a wurin, wadanda aka kammala a karshen wannan shekara. Nyima Dondrup ya ce: "Bayan da aka biya bukatun manoma da makiyaya na yin amfani da wayar salula, suna yin farin-ciki kwarai da gaske. Amma sun ce, kada su aika sakonni ta wayar salula, saboda ba su fahimci kalmomin daidaitaccen Sinanci ba. A waje guda kuma, suna so su karo ilimi a fannonin hasashen yanayi, da kimiyya da fasaha ta wayar salula, amma ba su gane rubutattun kalmomi na daidaitaccen Sinanci ba. Shi ya sa a karshen shekara ta 2004, mun kafa wani rukuni na musamman don binciken wayar tafi-da-gidanka dauke da kalmomin kabilar Tibet."

Irin wannan wayar salula dake dauke da kalmomin kabilar Tibet ta sami karbuwa sosai daga wajen 'yan kabilar Tibet, a halin yanzu, yawan mutanen da suke yin amfani da irin wannan waya ya zarce dubu 30. Sakataren kwamitin kauyen Bangdui na garin Bangdui na gundumar Dazi ta jihar Tibet Nyima Dondrup ya ce, kusan dukkanin iyalai 400 a kauyensu na mallakar irin wannan wayar salula, inda ya bayyana cewa: "Idan jama'a ba su fahimci harshen daidaitaccen Sinanci ba, da wuya ainun gare su wajen yin amfani da wayar tafi-da-gidanka. Yanzu, irin wannan wayar dake dauke da harshen kabilar Tibet ta kawo sauki ga zaman rayuwar 'yan kabilar. Mahaifina mai shekaru 76 da haihuwa, shi ma yana amfani da irin wannan wayar salula."

1 2 3