Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 23:02:46    
Aikin raya harshe da kalmomin kabilar Tibet ya shiga cikin sabon zamani

cri

Assalam alaikum! Masu saurare, barkanku da war haka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin shirinmu na "Kananan kabilun kasar Sin", Murtala ne ke matukar farin-cikin gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Masu saurare, 'yan kabilar Tibet suna da nasu harshe da kalmomi, wadanda aka dade ana yin amfani da su a fannoni da dama tun farkon lokacin da aka kirkiro su har zuwa yanzu, ciki har da addini, da tattalin arziki, da al'adu, da siyasa, gami da zaman rayuwar jama'a na yau da kullum. Harshe da kalmomi na kabilar Tibet suna taka muhimmiyar rawa a fannonin gadar kyawawan al'adun gargajiya na kabilar, da bunkasuwar kabilar. A cikin 'yan shekarun nan, sakamakon kirkire-kirkiren da ake yi ta hanyar kimiyya da fasaha, da cigaban aikin ilmantarwa, harshe da kuma kalmomi na kabilar Tibet suna bunkasuwa ba tare da kakkautawa ba.

A halin da ake ciki yanzu, a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, baya ga shirye-shiryen da ake watsawa ta kafofin rediyo da talabijin, har wa yau kuma akwai 'yan kabilar Tibet da dama wadanda ke yin amfani da wayar tafi-da-gidanka dauke da kalmomin Tibet.

1 2 3