
Haka kuma bisa labarin da wata jaridar Australia ta bayar a ran 23 ga watan Oktoba, an ce, manazarta na cibiyar nazarin lafiyar jikin mutum a fannin haifuwa ta jami'ar Adelaide sun gudanar da bincike kan mata 717 da aka haife su a asibitin sarauniya Elizabeth daga shekara ta 1973 zuwa shekara ta 1975, kuma mata 154 daga cikinsu, iyayensu mata sun taba shan taba lokacin da suke da ciki.
Michael Davids wanda ya gudanar da binciken ya bayyana cewa, yara mata da iyayensu mata suka sha taba ba su da jiki sosai lokacin da aka haife su, amma lokacin da suke girma, wadannan yara sun fi saukin yin kiba fiye da kima, kuma za su kamu da cutar hauhawar jini. Kuma nazarin ya bayyana cewa, idan mata suna shan taba lokacin da suke da ciki, to zai haifar da mumunar illa ga yaransu mata a duk tsawon rayuwarsu.
1 2 3 4 5
|