Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-21 15:29:43    
Yankin gwajin ayyukan gona na zamani da ke lardin Zhejiang na kasar Sin

cri

Masu karatu, gida mai dumi da ke renon ire-ire da muka gabatar dazun nan wani karamin kashi ne na yankin gwajin ayyukan gona na zamani a lardin Zhejiang. Bisa labarin da muka samu, an ce, an kaddamar da kafa yankin a shekara ta 2001, kuma fadinsa ya kai fiye da kadada 330, yawan kudaden da aka kebe wajen gina shi ya zarce kudin Sin wato Yuan miliyan 500. Kuma a cikin yankin, ana iya samun hukumomin nazarin kimiyya fiye da 20 ciki har da cibiyar ilmin kimiyya na ayyukan gona ta kasar Sin da jami'ar Zhejiang. A fannin fasahohin zamani na ayyukan gona, ban da wadanda kasar Sin ita kanta take da hakkin mallakar ilminsu, an shigo da fasahohin zamani daga kasashen Amurka da Faransa da Holland da dai sauransu. Ban da ledar ciyar da ire-ire, fasahar kwaikwayon halitta ta cibiyar kwaikwayon halittun tsire-tsire ta yankin ta kai matsayin koli na kasar Sin. Zhu Xiaoxiang, mai kula da yankin gwajin ya gaya wa wakilinmu cewa, ta fasahar kwaikwayon halitta, yanzu ana iya samar da dimbin tsire-tsire da furanni masu daraja sosai wadanda da kyar aka iya ciyar da su a da, ta haka manoma sun samu fa'ida sosai. Kuma ya kara da cewa,

"A lokacin da, idan ana son shigo da furen Moon Orchid daga yankin Taiwan na kasar Sin, to za a biya Yuan 15 zuwa 30 ga ko wanensu, amma yanzu in manoma suka biya Yuan 3 zuwa 5 kawai, to za su iya samun furen Moon Orchid da muka samar."

Kuma Mr. Zhu ya bayyana cewa, yanzu yawan tsire-tsire masu wuyar samuwa da cibiyar ta kwaikwayi hallitunsu ya riga ya kai miliyan 30 a ko wace shekara.


1 2 3