Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-21 15:29:43    
Yankin gwajin ayyukan gona na zamani da ke lardin Zhejiang na kasar Sin

cri

A cikin shirinmu na yau za mu shiga yankin ayyukan gona na zamani da zai zama abin koyi a lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, inda ake iya gano cewa, na'urar kwamfuta tana kulawa da girman shuke-shuke daga dukkan fannoni, ana yin wa shuke-shuke ban ruwa ta hanyar tattara ruwan sama, kuma ana kiyaye da kuma kyautata tsire-tsire masu wuyar samuwa ta hanyar kwaikwayon halitta. To yanzu bari mu leka yankin tare.

A cikin yankin gwajin ayyukan gona na zamani ta lardin Zhejiang, wakilinmu ya ga wani gida mai dumi da ake renon ire-ire da ke da matukar girma, amma abin mamaki shi ne a cikin ledar, ba a iya ganin kasa ko kadan ba, bishiyoyi suna girma a kan ulun ma'adinai, kuma ana sanya wata allura a cikin gindin ko wane tsiro, kamar yadda a kan yi wa mutane a cikin asibiti. Wadannan bishiyoyi sun samu ruwan gina jiki ne ta allurar bisa tsarin ban ruwa da na'urar kwamfuta ke sarrafawa. Gu Shenyan, wata ma'aikaciya ta yankin ta gaya mana cewa,

"Na'urar kwamfuta ita ce ta sarrafa zafin ledar da danshinta da kuma iskar da ke cikinta da dai sauransu. A cikin wata leda, muna bukatar ma'aikata daya ko biyu kawai, sauran ayyuka kuma ana iya gudanar da su ta kwamfuta."


1 2 3