Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-16 19:36:09    
Gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta bayar da kayayyakin tarihi masu daraja ga Beijing

cri

Bayan da aka kaddamar da wasannin Olympics na nakasassu ba da jimawa ba, shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na duniya Philip Craven ya taba nuni da cewa, shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta shekara ta 2008 cikin nasara zai bayar da dimbin kayayyakin tarihi masu daraja ga Beijing har ma duk kasar Sin, kuma wadannan kayayyakin tarihi za su amfana wa nakasassu miliyan 83 na kasar Sin cikin dogon lokaci. kuma Mr. Craven ya ce, "Ana iya samun wata cibiyar motsa jiki don warkarwa mai kayatarwa da ke kusa da filin jiragen sama na Beijing, wadda aka fara yin amfani da ita a shekara ta 2007. A bayyane ne ana iya gano cewa, an gina wannan cibiya ne domin nan gaba a maimakon wannan gasa kawai. Kuma wannan ya shaida cewa, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan wasannin Olympics na nakasassu."

Kamar yadda Mr. Craven ya ce, kasar Sin ba za ta daina yin kokari ba, kuma za ta ci gaba da aikinta a wannan fanni. Liu Zhi, kakakin wasannin Olympics na nakasassu na Beijing ya ce, "Bayan wasannin Olympics na nakasassu, za a ci gaba da yin amfani da wadannan ayyuka. Kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne za mu tsara wani cikakken tsari domin ci gaba da nuna kulawa ga nakasassu cikin dogon lokaci. Game da nakasassu kuma, za su gano a zo a gani, cewa za a ci gaba da yin amfani da kayayyakin tarihi da wasannin motsa jiki na nakasassu suka bayar cikin dogon lokaci ba tare da kasala ba."(Kande Gao)


1 2