Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-16 19:36:09    
Gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta bayar da kayayyakin tarihi masu daraja ga Beijing

cri

Za a rufe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta shekara ta 2008 gobe, amma sauye-sauye iri daban daban da ta kawo wa kasar Sin, ciki har da kyautatuwar ayyuka marasa shinge na birnin, da ci gaban sha'anin nakasassu, da kuma kyakkyawar dabi'a da mutane suka samu a fannin wayin kai da ladabi ba za su kare ba, gasar za ta bayar da kayayyakin tarihi masu daraja ga kasar Sin. To yanzu ga cikakken bayani.

Zhao Jihua, mai ba da shawara kan aikin horaswa na wasannin Olympics na Beijing ya bayyana cewa, a idonsa, a cikin kayayyakin tarihi da gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta bayar ga Beijing, kaya mafi daraja shi ne kyautatuwar wayin kai na birnin. Kuma ya kara da cewa, "Dukiya mafi daraja ita ce kyautatuwar wayin kai na birni, yanzu Beijing da ke da dogon tarihi yana kasancewa kamar wani birnin da ke kan gaban kuruciya. Idan mazaunan wani birni ke iya samun hasken zuci da hakuri kamar haka, to birnin zai samu boyayyen karfin bunkasuwa sosai a nan gaba."

Haka kuma Lv Zhengming, mataimakin shugaban kungiyar hadin gwiwa ta nakasassu ta Beijing ya bayyana cewa, shirya wasannin Olympics na nakasassu na Beijing zai karfafa zuciyar duk zaman al'umma wajen nuna girmamawa ga nakasassu. Kuma ya kara da cewa, "Ta hanyar shirya wannan wasannin Olympics na nakasassu, a dukkan kasashen duniya musamman ma birnin Beijing har ma duk fadin kasar Sin, za a dauki wani sabon ra'ayi kan nakasassu, wato babu kasancewar mutane marasa kwarewa, sai dai kasancewar mutanen da ke nuna kwarewa a fannoni daban daban, babu nakasassu, sai dai zaman al'umma da suke da nakasa, wanda mutane ke iya canja irinsa. Ina ganin cewa, ta hanyar shirya wasannin Olympics na nakasassu, za a sa kaimi sosai ga duk zaman al'umma wajen nuna fahimta da girmamwa da kulawa da kuma taimako ga nakasassun da ke shan wahala sosai."

1 2