Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 23:39:00    
An bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri

Lubabatu:'Yan wasa na kasa da kasa su ma suna sa rai ga gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing. Tawagar wakilai ta kasar Sin ta fi girma a gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing. Shugaban tawagar, Mr. Wang Xinxian ya ce, 'yan wasa na kasar Sin za su yi kokari a ko wane wasa. Ya ce, Lawal:"A dukkan wasannin, 'yan wasanmu za su yi kokari da suke iya yi, domin kara samun maki mai kyau. Ban da wannan kuma, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta wannan karo ta zama wani gaggarumin biki mai jituwa da jin dadi, wasannin nakasassu kuma za su bayar da jin dadi ga jama'a."

Lubabatu:Gasar wasannin Olympics ta nakasassu ba wata gasa da 'yan wasa nakasassu suke halarta kawai ba, har ma ta zama wani dandali da ke dauke da burin nakasassu, da ke wuce iyakarsu da kansu, da kuma bayyana ra'ayi cewa, nakasassu da sauran jama'a da ba na nakasassu ba suna da duniya daya, suna more jin dadi tare.

Lawal:Duniya daya, mafarki daya! A yau da dare, an bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing. A cikin kwanaki fiye da 10 masu zuwa, 'yan wasa nakasassu da suka zo daga kasa da kasa za su dauki hakikanan matakai a nan birnin Beijing, domin bayyana ra'ayinsu na wuce iyakarsu, da bayyana ra'ayoyin Olympic na hadin kai, da zaman lafiya, da zaman jituwa, za su hada zukatan nakasassu da na wadanda ba nakasassu ba wuri daya, za su bude wani shafin kide kide masu kayatarwa na gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing !

Lubabatu:Jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na musamman na bikin kaddamar da gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing daga nan sashen Hausa na Gidan Rediyon Kasar Sin, Ni Lubabatu da Lawal Mamuda ke nuna godiya da sauraron shirin, a madadin Sanusi da Jamila da Bilkisu da Musa da Dandali da Kande da suka shirya, muke cewa a kasance lafiya.


1 2 3 4 5 6 7 8 9