Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 23:39:00    
An bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri

Lawal:Zhao Chunluan, wata jami'ar hadaddiyar kungiyar nakasassu ta birnin Beijing ta bayyana cewa, Lubabatu:"Wadannan manufofi sun hada da ba da tabbacin zaman al'ummar kasa da sa kaimi kan samar wa nakasassu guraban aikin yi da kuma tabbatar da ganin nakasassu su iya gudanar da harkokin zaman al'ummar kasa cikin adalci."

Lawal:A watan Afrilu na wannan shekara, hukumar kafa dokoki ta kasar Sin ta yi gyare-gyare kan "dokar ba da tabbaci ga nakasassu", ta inganta ba da tabbaci ga nakasassu, ta kuma fara aiwatar da ita a ran 1 ga watan Yuli. A watan Yuni na shekarar da muke ciki, zaunannen kwamiti na majalisar wakilai ta jama'ar kasar Sin ya zartas da "yarjejeniyar kiyaye ikon nakasassu" da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara. Wannan yarjejeniya na matsayin dokar duniya ta farko da aka tsara kan kiyaye ikon nakasassu daga dukkan fannoni a tarihin Majalisar Dinkin Duniya.

Lubabatu:Wu Dawei, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya yi bayani da cewa, Lawal:"Zartas da wannan yarjejeniya yana amfanawa wajen kara samar da kyakkyawan muhalli na girmama ikon nakasassu da mutuncinsu, haka kuma, ya bai wa kasar Sin taimako wajen sa kaimi kan bunkasuwar sha'anin ba da tabbaci ga nakasassu."

Lawal:Jama'a masu sauraro, barkanku da cigaba da sauraron shirinmu na musamman kan bikin bude gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing daga nan gidan rediyon kasar Sin, wato CRI.

Lubabatu:A matsayinsa na daya da ke cikin hasashe iri uku na gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing, "morewa tare" ya nuna mana cewa, "nakasassu da mutane marasa nakasa suna cikin duniya iri daya, kuma suna kirkiro wa kansu makoma tare. "morewa tare" shi ne neman sanya nakasassu da mutane marasa nakasa da su sami dama cikin adalci cikin gasannin Olympic da zaman rayuwa ta yau da kullum.

Mr. Li Xiaogang, wani injiniya mai gyaran kayayyakin da ke yin amfani da wutar lantarki. Ko da yake yana zama kan keken guragu a ko wace rana, amma yana son zuwa filin gasa domin kallon gasar Olympic kwarai, kuma ya cimma burinsa a sakamakon kayayyaki da na'urori marasa shinge da aka shirya a nan birnin Beijing saboda gasar Olympic ta nakasassu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9