Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 15:26:24    
Jihar Hainan ta kasar Sin tana bin hanyar bunkasa tattalin arzikinta kamar yadda ya kamata

cri

Malam Chen Yongwan, kakakin hukumar aikin noma ta jihar Hainan ya ce, "ta hanyar kyautata tsarin aikin noma, mun tsara manufar mayar da jihar Hainan da ta zama babbar jihar noma kayayyakin lambu a dukkan kasar. Yawan kayayyakin lambun da muka samu ya wuce tan miliyan 4 a shekarar bara, wato ya karu sosai bisa na kafin lokacin kafuwar jihar. Yawancinsu an sayar da su zuwa wurare daban daban na kasar Sin ."

A shekarar bara, yawan masu yawon shakatawa na gida da waje wadanda jihar Hainan ta karba ya wuce miliyan 18, ya kasance cikin sahon gaba a dukkan kasar Sin. Malam Zhang Qi, shugaban hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta jihar Hainan ya bayyana cewa, bisa manufar da jihar ta tsara game da bunkasa harkokin yawon shakatawa ita ce raya jihar da ta zama tsibirin yawon shakatawa na kasa da kasa. Ya kara da cewa, "nan gaba za mu yi kokari musamman domin raya tsibirin Hainan da ya zama tsibirin yawon shakatawa na kasa da kasa. Babban taken farfagandar da muke yi shi ne, tsibirin Hainan wuri mai zafi na kasar Sin aljannar yawon shakatawa ne a gabashin duniya. Don haka nan gaba za mu gudanar da harkokin yawon shakatawa don raya jihar Hainan da ya zama tsibirin yawon shakatawa na kasa da kasa."

Yanzu, jihar Hainan ta kasar Sin tana bin hanyar bunkasa tattalin arzikinta kamar yadda ya kamata.(Halilu)


1 2