Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 15:26:24    
Jihar Hainan ta kasar Sin tana bin hanyar bunkasa tattalin arzikinta kamar yadda ya kamata

cri

Jihar Hainan tsibiri ne mafi girma na biyu a kasar Sin, kuma yana kuriyar kudancin kasar. An kafa jihar a shekarar 1988, sa'an nan an kafa yankin musamman na raya tattalin arziki na Hainan, wanda ya zama irin wannan yanki mafi fadi a kasar Sin. A farkon lokacin kafuwarta, jihar ta dandana wahala daga bunkasuwar bogi a fannin tattalin arziki, bayan haka ta hanyar tsara kyakkyawan fasali na zamani, yanzu jihar Hainan ta riga ta kubutar da kanta daga bunkasuwar bogi a fannin tattalin arziki, kuma tana bin hanyar bunkasa tattalin arzikinta cikin sauri kamar yadda ya kamata.

A cikin misalin shekaru 40 da suka wuce bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, an bunkasa tattalin arzikin jihar sannu sannu. Jimlar kudin da dukkan jihar ta samu daga wajen samar da kayayyaki wato GDP ta kai kudin Sin Yuan sama da biliyan 5 kawai a shekarar 1987. Yayin da shehun malami Liao Xun wanda ke aiki a cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'ummar kasar Sin ya isa birnin Haikou, fadar gwamnatin jihar Hainan a shekarar 1988, ya yi mamaki da komawar bayan wuri a fannin tattalin arziki. Ya ce, "birnin tamkar kauye ne. Filin jirgin sama na birnin ya tashi daidai da wata tashar motoci masu dogon zango a wani birnin arewacin kasar Sin. A cikin birnin, akwai manyan hanyoyi biyu ko uku na suminti ko kwalta ne, sauran dukkan hanyoyi na rairayi ne. Na yi mamaki da ganin irin wannan babban birni na wata jihar kasar Sin wanda ya koma baya kamar haka."

Malam Liao Xun yana daya daga cikin mutane masu dimbin yawa da suka yi kaura zuwa jihar Hainan daga babban yankin kasar Sin don neman arziki. A farkon shekarun 1990, gwamnatin kasar Sin ta fara yin kwaskwarima kan tsarin gidajen kwana don bunkasa kasuwannin sayar da gidaje. A sakamakon karuwar mutane masu dimbin yawa da suka yi kaura zuwa jihar Haian, an nuna himma sosai ga gina gidaje. A cikin irin wannan hali ne, aka kafa kamfanonin sayar da gidaje da yawansu ya wuce dubu 20 a jihar Hainan mai yawan mutane kasa da miliyan 1.6. Wato ko wadanne mutanen Hainan 80 na da wani kamfanin sayar da gidaje daya. Farashin gidaje ma ya karu sama da ninki hudu a cikin shekaru uku. Zuwa shekarar 1993, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai a jere don daidaita batutuwan da aka gamu a kasuwannin sayar da gidaje.

Bayan da jihar ta kubutar da kanta daga halin bunkasuwar bogi a fannin tattalin arziki, hukumar jihar ta gabatar da sabon shirin raya jihar cewa, za a raya jihar Hainan da ta zama wani sabuwar jihar masana'antu da sansanin noman amfanin gona iri na wurare masu zafi da wuraren yawon shakatawa.


1 2