Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 17:17:06    
Shahararren garin Boao na kasar Sin

cri

Hanyoyin mota sun hada garin Boao da sauran wurare da yawa. A ko wace shekara, a kan yi taruruka manya da kanana fiye da dari 1 a wurin, haka kuma, miliyoyin masu yawon shakatawa su kan kawo wa Boao ziyara. A tashar jiragen ruwa ta Yudaitan, in lokacin hutu ya yi, to, tana cike da dimbin mutane.Mr. Wang, wani mai jagorantar masu yawon shakatawa, ya gaya mana cewa, 'Mutane suna kawo wa Boao ziyara domin kallon kyan karkara na halitta da ke shan bamban da na sauran wurare. Akwai wani wurin da koguna 3 suka hadu da juna da kuma bakin teku mai suna Yudaitan mafi matsatsi a duniya. Muhimmin dalilin da ya sa aka yi taron dandalin tattaunawa na Asiya a nan shi ne domin irin wadannan ni'imtattun wurare a Boao.'

In babu manyan taruruka, to, yawancin masu yawon shakatawa su kan kawo wa Boao ziyara da safe. Shi ya sa mazauna wurin da ke tukin kwale-kwale a wuraren yawon shakatawa da kuma wadanda ke wanke dodon hotuna ko kuma sayar da amfanin gona da aka samu a Boao a kawai su kan gama aikinsu da yamma misalin da karfe 2 zuwa 3. Ta haka, an sake yin tsit a garin. Babu mutane da yawa a kan hanyoyi masu fadi. A kantuna, iyalai su kan yi hira cikin murna.

Wu Enze, sakataren kwamitin garin Boao na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi karin bayani da cewa, bisa shirin da aka tsara wajen raya garin, za a kebe wani yankin musamman mai fadin misalin kilomita dari 1 ko fiye a kewayen garin Boao, haka kuma, za a kara inganta karfin garin a fannonin ba da hidima ga al'umma da kuma kula da harkokin garin kamar yadda ya kamata. Burinsa shi ne raya garinsa na Boao zuwa wurin hutawa da zai fi yin shahara a duniya. Mr. Wu ya ce,'Mun gabatar da manufar raya garinmu zuwa wurin da ke kasancewar aljanna a duniyarmu. Muna da dimbin albarkatun yawon shakatawa da al'adu masu sigogin musamman. Ba mu raya garinmu zuwa birni na zamani ba, muna neman kafa garinsu na Boao zuwa wani karamin gari da zai kasance aljanna ce a duniyarmu, wanda ke da sigar musamman ta kasar Sin, kuma za a sami kwanciyar hankali da halin soyayya a nan, ban da wannan kuma, zai dace da rayuwar mutane. Don haka, mazauna birane za su iya hutawa da nishadi a nan, za su yi sakin jiki da jin dadin zamansu nawa nawa a garinmu.'


1 2