Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 17:17:06    
Shahararren garin Boao na kasar Sin

cri

A gabashin bakin rairayi na kudancin teku na kasar Sin, akwai wani karamin gari mai suna Boao. Fadinsa ya kai murabba'in kilomita 2 kawai, kuma mutane dubu 10 ko fiye kawai suna zama a nan. Amma tun daga shekarar 2002, a ko wace shekara a kan yi taron dandalin tattaunawa na shekara-shekara na Asiya a wurin. A duk wannan lokaci, wannan gari ya jawo hankulan kafofin yada labaru na duk duniya.

Garin Boao na karkashin shugabacin hukumar birnin Qionghai na lardin Hainan. Mr. Wang Yi, wani ma'aikacin hukumar birnin ya shiga ayyukan shirya taron dandalin tattaunawar tun daga farko. Ya waiwayi abubuwan da suka faru a da. Ya ce,'A shekarar 1985, na zo nan garin Boao, na zo tsibirin Dongyu cikin kwale-kwale. A lokacin da nake yawo a wurin, ina tsammani cewa, wannan tsibiri aljanna ce a duniyarmu. Mazauna wurin na da kirki sosai.'

Irin ni'itattun wurare na halitta su ne suka jawo hankalin Jiang Xiaosong, wani mai masana'antu kuma mai kishin ayyukan al'umma, ya zuba jari domin raya wannan wuri, ya kuma kafa kamfanin kula da harkokin zuba jari na Boao. Daga baya kuma, Mr. Jiang ya ba da tasirinsa ya gayyaci tsoffin kososhin gwamnatocin kasashen Japan da Australia da kuma Philippines da su yi wasan kwallon Golf a Boao, wadanda a karshe dai suka yi kirar shirya taron dandalin tattaunawa na Asiya na Boao. A watan Febrairu na shekarar 2001, an kaddamar da wannan taron dandalin tattaunawa a hukunce, kuma an tsai da kudurin shirya shi a Boao har abada. Tun daga shekarar 2002, a kan shirya wannan taron shekara-shekara a ko wane watan Afrilu a garin Boao, inda jami'an gwamnatoci suka halarci taruruka domin tattauna manyan batutuwan da ke shafar bunkasuwar kasashen Asiya da tekun Pacific da ta duk duniya. Mr. Jiang ya kara da cewa,'Na kai wa Boao ziyara ba domin wani dalili ba, amma bayan da na sauka wurin, kyan karkara ya burge ni, na kaddamar da ayyuka da yawa a nan. In ban ziyarci Boao ba, sai ba a sami taron dandalin tattaunawa na Asiya na Boao ba. Ba shakka, wannan taro ya biya bukatun kasashen Asiya dukka.'

1 2