
Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Amurka suka bayar, an ce, manazarta na jami'ar Wake Forest ta jihar North Carolina ta kasar Amurka sun samu wannan sakamako ne bayan da suka gudanar da wani bincike ga mutane wajen dubu 285 kan al'adar cin abinci da kuma lafiyar jikinsu.
Bisa ma'aunin da hukumar kula da abinci da magunguna ta kasar Amurka ta bayar, an ce, abincin da ke da hatsi kadai shi ne abincin da ake yi da alkama da sha'ir da dai sauran hatsi, wanda yake kunshe da vitamin da fibre da trace elements da kuma sinadarin da ke hana toshewar hanyar jini wato antioxidant, ta haka zai ba da tasiri sosai wajen rage yawan kitsen da ke taruwa a jijiya, wanda ke hana jini gudu, da kuma shawo kan toshewar hanyoyin jini.
Haka kuma manazarta sun nuna cewa, ba kawai cin abinci da ke da hatsi kadai yana iya shawo kan cututtukan zuciya da hauhawar jini ba, har ma yana iya bayar da amfani wajen shawo kan cututtukan ciki da kuma cutar sukari.(Kande Gao) 1 2 3
|