
A cikin wannan bincike na shekaru 10 zuwa 15, sabo da an rage yawan gishirin da wadannan mutane suka ci, shi ya sa yawan mutanen da suka kamu da cututtukan zuciya da hauhawar jini ta ragu da kashi 25 cikin dari. Kuma game da wadanda suka kamu da wadannan cututtuka, yawansu da suka mutu ya ragu da kashi 20 cikin dari.
Haka kuma kungiyar binciken ta nuna cewa, sabo da ta gudanar da wannan bincike ga mutane masu dimbin yawa cikin dogon lokaci, shi ya sa ta samu wata shaida mai karfi, wato lalle cin gishiri kadan zai iya rigakafin kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini.
To, masu karatu, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu gabatar muku da wani labari daban kan cewa, cin abinci da yawa da ke da hatsi kadai zai iya rage hadarin kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini.
1 2 3
|